Magoya bayan Trump sun tayar da rikici a Majalisar Dokokin Amurka

Wannan shafi ne da ke kawo muku abarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sasssan duniya a ranar da muka shiga sabuwar shekarar 2021.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Halima Umar Saleh

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta duka labaran da muka wallafa a wannan shafin.

  2. Dalilin da ya sa ake zanga-zanga a gaban Majalisar Tarayyar Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan jerin zanga-zangar da aka yi kan adawa da dokar kullen korona, da suka haɗa da na Michigan inda masu ta da zune tsaye suka kutsa majalisar jihar, a yanzu kuma ga irin hakan na faruwa a babban birnin Amurkan Washington DC.

    A yayin da ƴan majalisar dokokin ƙasar ke taron haɗin gwiwa a ranar Laraba don tabbatar da nasarar Joe Biden, sai lamarin ya gamu da cikas sakamakon ɓarkewar rikici tsakanin ƴan sanda da masu zanga-zanga a cikin ginin majalisar.

    Trump ya shafe makonni yana iƙirarin cewa shi ne ya lashe zaɓen ƙasar, inda ya ce an yi maguɗi a manyan jihohin da Biden ya yi nasara ba tare da ya gabatar da wata hujja ba.

    Shi da magoya bayansa sun yi ta matsa wa mataimakinsa Mike pence kan ya sauya sakamakon zaɓen ta hanyar ƙin tabbatar da nasarar Biden, wani abu da ƙwararru suka ce ba shi da ƙarfin iko a shari’ance na yin hakan.

    A kwanakin da suka kawo ranar tabbatarwar, Trump ya ce zai halarci taron gangamin “Save America” wato “A ceci Amurka” da za a yi ranar Laraba a birnin Washington, inda ya yi alƙawari a Twitter cewa gangamin zai kasance babba kuma gagarumi.

    Sa’a guda bayan da Trump ya yi wa dubban mutane jawabi tare da alƙawarin cewa ba zai taɓa amsa shan kaye ba, sai rikici ya ɓarke.

  3. Ƴan sanda na barazanar harbi a cikin majalisa

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sandan da ke cikin Majalisar Taryyar Amurka sun kama wasu daga cikin masu zanga-zangar, yayin da wasu daga cikinsu ke ci gaba da shiga ginin majalisar.

    Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun haura bango inda suka afka ciki, amma tuni ƴan sanda suka ciro bindigoginsu da kuma barazanar harbin masu zanga-zangar.

    Matamakin shugaban ƙasa ya yi kira ga masu goyon bayan Trump da su bar ginin na Capitol tare da dakatar da rikicin.

    “Ba za mu lamunci wannan hari a kan majalisarmu ba, kuma za a tuhumi duk wanda aka kama da laifi," a cewar Mike Pence.

  4. An buƙaci ƴan majalisa da manema labarai su nemi mafaka

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana cewa ƴan majalisa da manema labarai da ke cikin ginin majalisar su fice su nemi maɓoya tare da sanya takunkumin da zai kare su daga shaƙar hayaƙi mai sa hawaye.

    Masu zanga-zangar sun ci gaba da kutsawa cikin ginin Capitol, wasu na ta ɗaukar hotuna.

    Wasu kuma suna ihun “Trump muke so” ta yadda ƙarar tasu ta karaɗe wajen, yayin da ake ta ƙoƙarin nemar wa ƴn jarida da ƴn majalisun mafaka.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Mike Pence ya sha alwashin tabbatar da nasarar Biden duk da gargaɗin Trump

    Tun da fari dai mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya ce ba zai hana tabbatar da nasarar Joe Biden a zaben shugaban kasa ba, a yayin zaman hadin gwiwar na majalisun kasar.

    Sai dai ya ce zai bai wa masu son kalubalantar zaben dama su bayyana ra’ayoyinsu kan nasarar da Mista Biden ya samu, abin da a bisa al’ada wani karamin al’amari ne, sai dai ga alama karamar magana ta zama babba.

    Shugaba Donald Trump tun da farko ya bukaci Mista Pence da ka da ya tabbatar da sakamakon yayin zaman majalisun, sai dai Shugaban Majalisar Dattijan Mitch McConnell, ya fada wa majalisar cewa babu wata hujja da ke nuna cewa an aikata wani abu da zai sauya sakamakon zaben.

    Ya ce: “Babu wani abu da aka kawo gaban mu dake nuna an yi ba dai-dai ba a ko ina da da ya kusa zama wani gaggarumin abu, wani gagarumin abuda zai kawo wa daukacin zaben tawaya”.

  6. Shugaba Trump ya yi kira da magoya bayansa da su bi komai a sannu

    Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kira ga magoya bayansa da su bi komai a sannu a yayin da suka dirar wa Majalisar Dokokin ƙasar wato Capitol.

    Ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa “su bi doka da odar majalusar.“Tabbas suna bayan ƙasarmu ne,” kamar yadda ya rubuta.

    “Ku yi komai cikin nutsuwa.Kafafen yada labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa an yi ta watsa hayaƙi mai sa ahwaye a cikin ginin majalisar yayin da mutanen da ke kutsawa ciki ke ƙaruwa.

    Tuni dai magajin garin birnin Washington Muriel Bowser ya yi umarnin sanya dokar hana zirag-zirga da za ta fara aiki da misalin ƙarfe 6 na marecen ƙasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Labarai da dumi-dumi, Magoya bayan Trump na zanga-zanga a Majalisar Dokokin Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images..

    Rahotanni daga Washington DC na Amurka na cewa rikici ya ɓarke a cikin harabar Majalisar Tarayyar Amurka, bayan magoya bayan Donald Trump sun afka ciki suna zanga-zanga.

    Tuni dai Mista Trump ɗin ya aika da saƙo a shafin Twitter inda ya buƙaci a daina tayar da tarzoma.

    Ƴan majalisar sun taru ne don tabbatar ne zaɓen Joe Biden – wani al’amari da masu zanga-zangar suka yi watsi da shi.

    Hotuna sun nuna yadda masu zanga-zangar suka taru a wajen ginin majalisar dattikai.

    Wasu hotunan sun nuna yadda masu zanga-zangar ke ɗauke da makamai.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Mutum 130,000 masu cutar korona ke kwance a asibiti a Amurka

    ambulance

    Asalin hoton, Getty Images

    Fiye da mutum 130,000 ke kwance a asibiti a Amurka inda suke karbar maganin cutar korona, wani adadi da aka samu tun lokacin da annobar ta bulla.

    Yawan sabbin wadanda suka kamu da cutar ya kasance wani gagarumi, musamman a kudanci da kuma yammacin Amurka.

    Akwai damuwa cewa alluran riga-kafin cutar biyu da aka amince da su a yi wa Amurkawa cikin hanzari sauri ba.

    Lamarin ya kai wasu jihohi sun fadada aikinsu don hanzarta yi wa jama’a allurar, ta hanyar sanya dakarun tsaren kasa cikin aikin a North Carolina da Maryland.

  9. Ana ci gaba da bincike kan yaron da ake zargin an yi lalata da shi a makaranta

    Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike kan wadanda ake zargi da yin lalata da wani yaro dan shekara 11 a makarantar Deeper Life da ke a jihar.

    Bayan ta kammala bincike ne za ta gurfanar da wadanda ake zargin.

    A makon karshe na shekara ta 2020 ne mahaifiyar yaron da ake kira Deborah ta yi zargi ta kafofin sada zumunta cewa daliban sakandare na kwana da ke gaba da Don Davies sun yi lalata da shi.

  10. Mutum 14 sun mutu a hatsarin mota a Jihar Kogi ta Najeriya

    Aƙalla mutum 14 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a ranar Laraba a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa hatsarin ya faru ne tsakanin wata motar bas ta fasinja da kuma tirelar ɗaukar siminti a kan titin Obajana-Lokoja.

    A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Kingsley Fanwo ya fitar, ya ce gwamnatin jihar ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya rutsa da su.

    Punch ta ce kwamishinan ya ce tuni ma’aikatan hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta FRSC ta kwashe gawarwakin daga wajen da abin ya faru.

  11. Ƙungiyar Ƙwadago ta soki matakin gwamnatin Najeriya na ƙarin farashin lantarki

    Ƙungiyar kwadagonta Najeriya ta soki matakin da gwamnati ta dauka na kara farashin kiliwat na wutar lantarki daga naira biyu zuwa naira hudu.

    Kungiyar ta ce karin farshin zai munana halin kuncin da al’umma ke ciki, don haka ba za ta amince da shi ba.

    Hukumar da ke kula da harkokin wutar lantarki ta kasar ta ce an yi ƙarin farashin ne bisa la’akari da hauhawar farashi.

    Kungiyar kwadagon Najeriyar ta ce gwamnatin kasar ba ta kama hanyar da za su fahinci juna ba da wannan karin farashin wutar lantarki da aka yi, inda kilowatt daya ya tashi daga naira biyu zuwa naira hudu.

    Saboda a cewar kungiyar, har yanzu ba su daidaita da gwamnati ba dangane da wani tsohon karin farshin da aka yi a watan satumban bara, don haka ba ta ga yadda za ta amince da wani sabon kari na kasha hamsin cikin dari ba.

    Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron rahoton da Ibrahim Isa ya hada:

    Bayanan sautiRahoton Ibrahim Isa kan ƙorafin NLC kan ƙarin kuɗin lantarki
  12. Ƴan kasuwar Legas na rangadin lallashin manoman kayan gwari

    Wata tawagar ‘yan kasuwa daga kasuwar kasa da kasa ta Mile 12 da ke Legas na ci gaba da rangadin jihohin arewacin kasar domin lallashin dilalai da manoman kayan gwari do su ci gaba da kai hajojinsu a can.

    An dai samu janyen kafar fataucin kayan gwarin daga arewa zuwa kudu a baya-bayan nan sakamakon matsalolin tsaro da rikice da haraje-haraje da makamantansu.

    Tawagar dai ta fara rangadin ne daga jihar Sakkwato inda a jiya suka gana da manoma da kuma dillalan kayan gwari daga jihohin Sakkwato Kebbi da Zamfara.

    Ga rahoton Haruna Shehu Tangaza:

    Bayanan sautiRahoton Haruna Tangaza kan rangadi masu kayan gwari
  13. 'Hukumar Kwastam ta samar wa gwamnatin harajin fiye da tiriliyan 1.5 a 2020'

    Hamid Ali

    Asalin hoton, Nigeria Custom

    Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya ta ce ta samarwa gwamnati harajin fiye da naira tiriliyan daya da rabi a shekarar 2020.

    Kudin da hukumar ta tara ya haura abinda aka yi hasashen za ta iya tarawa naira tiriliyan daya da biliyan 380.

    Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Joseph Attah ya fitar ranar Larabar nan, ta nuna cewa hukumar ta cimma wannan nasara duk da kalubalen cutar korona.

    Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Kanal Hamid Ali mai ritaya yana cewa duk shekara kudaden da hukumar ke tarawa suna karuwa saboda wasu sauye-sauye da ake aiwatarwa.

    Joseph Attah ya ce rufe iyakokin tudu da aka yi sun tilastawa masu fasa kwauri su shigar da kayansu ta ruwa da kuma filayen jiragen sama, kuma hakan ya taimaka wajen karuwar kudin shigar da hukumar ta tara.

    Hukumar ta ce a yanzu tana samun harajin da ya kama daga naira biliyan biyar zuwa biliyan tara a kowace rana, sabanin abin da take samu kafin rufe iyaka da ba ya wuce naira biliyan hudu zuwa kbiyar kowace rana.

    Sanarwar ta Joseph Attah ta ce hukumar ta hana fasa kwauri ta kuma kwace haramtattun kayayyaki 4,304 da suka hada makamai da kayan sa maye, da man gyada da daskararrun kaji da kuma shinkafa ‘yar waje.

  14. Bam ya hallaka sojojin Kamaru huɗu da wani jami'in gwamnati

    Sojoji huɗu da wani jami'in gwamnatin Kamaru sun mutu a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar, bayan da motarsu ta bi ta kan wani abin fashewa, a cewar jami'ai.

    Mutanen biyar na tafiya ne tare da wani ayarin motoci a lokacin da fashewar ta faru a kan titin tafiya garin Mbengwi, kusan kilomita 450 daga Yaoundé, babban birnin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin, amma gwamnati tana zargin ƴan aware masu ɗauke da makamai.

    Yankin masu amfani da Turancin Ingilishi na Kamaru na fama da rikice-rikice tun shekarar 2017, inda mayaƙan sa kai ke neman ɓallewa daga yankin masu amfani da Faransanci.

  15. Masu katin ƴan ƙasa za su biya kuɗi idan suna son gyara wasu bayanai - NIMC

    NIN

    Asalin hoton, Other

    Hukumar Samar da Katin Ƴan Ƙasa ta Najeriya NIMC, ta ce ƴan ƙasar da ke da lambar katin ƴan ƙasa ta NIN za su dinga biyan wasu kuɗaɗe a lokacin da suke son sauya bayanansu ko sauya katinsu na ƴan ƙasa.

    Wani babban jami'i a hukumar Funmi Opesanwo, ta ce kuɗaɗen da za a dinga cajin mutanen na yin wasu sauye-sauye ne.

    Ta ce suna da tsare-tsaren ayyuka daban-daban da hukumar ta tanadar kamar idan mutum na son sauya suna ko adireshi ko kuma sauya katin, inda a nan ne za a biya wasu kuɗaɗe, amma idan mutum zai yi rijista ne a karon farko to ba zai biya komai ba.

    Ga mutanen da ke son sauya ranar haihuwarsu, za su biya naira 15,000.

    Idan kuma adireshinka za ka sauya ko kuma za ka gyara sunanka, to naira 500 kacal za ka biya.

    Idan kuma sauya katinka za ka yi da sabo to za ka biya naira 5,000.

    Madam Opesanwo ta ce: "Domin saua ranar haihuwa, kudin da za a biya N15,000. Idan kuma sauya kati za a yi, to za a biya N5,000. Domin gyara adireshi ku suna kuwa, abin da za a biya N500. Don haka mutane ba su fahimci abin ba, sai suka zaci NIMC ta ce su biya wasu kuɗaɗe ne. Wannan kuɗi na sauye-sauyen da mutum ke so ne."

  16. Kotun Burtaniya ta ƙi bayar da belin Julian Assange

    Julian Assange

    Asalin hoton, PA Media

    Wata kotu a Burtaniya ta ƙi amincewa da bayar da belin mai shafin kwarmata bayanai na intanet, Julian Assange.

    Alƙalin kotun ya ce akwai ƙwaƙƙwarar hujjar cewa muddin aka sake shi, zai ƙi zuwa kotu yayin da za a saurari ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke na ƙin miƙa shi ga Amurka.

    Amurka dai na ƙalubalantar hukunci, da aka yanke ranar Litinin, inda ta buƙaci da a miƙa mata Mista Assange don ya fuskanci tuhume-tuhumen da suka shafi wallafa wasu dubun-dubatar bayanan soji da na diflomasiyya.

  17. Zimbabwe na neman ɗauki kan ciro gawar ɗan yawon buɗe ido a Tafkin Victoria

    Victoria Fall

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Zimbabwe ta roƙi kamfanoni masu zaman kansu da suke da kayan aiki na zamani da su taimaka wajen gano gawar wani ɗan yawon buɗe ido da ya zame ya faɗa cikin Mafaɗar Ruwa ta Victoria Fall, kamar yadda jaridar Heralda ta ruwaito.

    Ministan Yawon Buɗe Ido na Zimbabwe Mangaliso Ndlovu ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin neman gawar sai dai akwai ƙalubale wajen kayan da za a yi amfani da su.

    Ya ce zuwa yanzu gwamnati ta iya gano wani kamfani ɗaya ne kawai da yake da irin kayan aikin da ake buƙata.

    Ministan ya aika saƙon ta’aziyya ga iyalan mutumin wanda har yanzu gawarsa ke wajen mafaɗar ruwan.

    An ga hoto na ƙarshe da mutumin ya ɗauka yayin da yake tafiya a kusa da ruwan da ke gudana.

    Ganau sun ce mutumin na ɗaukar hotuna a wjaen yawon uɗe idon ne a lokacin da ya zame.

    Minista Ndlovu ya ce lamarin wani mummunan abu ne na taƙaici.

    “Za a ɗauki dukkan matakan kare faruwar irin hakan nan gaba,” kamar yadda ya ce a wata sanarwa da jaridat ta ambato.

    Ya kuma ƙara da cewa ana samun cikas wajen ciro gawar ne saboda kasa gano inda ainihi take.

  18. Amurka na tattaunawa da Sudan kan yafe mata bashi

    Sudan economy

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Tattalin arziƙin Sudan na fuskantar koma baya, inda ake samun hauhawar farashin kayayyaki

    Sakataren Baitil Malin Amurka Steven Mnuchin ya je Sudan domin tattaunawa kan tattalin arziki, biyo bayan matakin da ƙasarsa ta ɗauka a bara na cire Sudan ɗin daga jerin ƙasashen da ke goyon bayan ta’addanci.

    Gwamnatin Sudan ta ce Mista Mnuchin zai tattauna kan sauƙaƙa basukan da Amurka ke bin ta da kuma agajin da Amurkar za ta ba ta nan gaba na kimanin dala biliyan ɗaya.

    Tattalin arziƙin Sudan na fuskantar koma baya, inda ake samun hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin isassun kuɗaɗe.

    Amurka ta cire Sudan daga jerin ƙasashen da ke goyon bayan ta’addanci a watan Disamba, bayan shiryawar ƙasar da Isra’ila.

  19. Tarayyar Turai ta amince da amfani da riga-kafin korona na biyu

    Riga-kafi

    Asalin hoton, Moderna

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da fara amfani da riga-kafin cutar korona da kamfanin Moderna na Amurka ya samar a ƙasa 27 na ƙungiyar.

    Ita ce ta biyu da hukumar European Medicines Agency (EMA) ke amincewa da ita bayan ta amince da ta sahale amfani da ta Pfizer-BioNTech.

    "Wannan riga-kafin za ta ba mu damar shawo kan matsalar cikin gaggawa," a cewar shugaban EMA, Emer Cook, a cikin wata sanarwa.

    Ana buƙatar a saka hannu kan amincewar a hukumance, kuma ana sa ran yin hakan nan gaba a yau.

    Tana buƙatar ajiyewa a cikin yanayin ma'aunin sanyi na -20C yayin rarraba ta - kamar dai sanyin ƙaramin firji.

    Ita kuwa riga-kafin Pfizer-BioNTech a gefe guda, tana buƙatar aƙalla yanayin sanyi -75, abin da ke jawo wahalhalu wurin jigilarta.

  20. Najeriya za ta karɓi riga-kafin korona a watan Janairu

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Najeriya na sa ran samun riga-kafin cutar korona nan da ƙarshen watan Janairu yayin da take ƙoƙarin kare kashi 40 cikin 100 na al'ummarta daga cutar a wannan shekarar da kuma kashi 30 a shekara mai zuwa.

    Zubin farko zai ƙunshi allurar guda 100,000 ta Pfizer-BioNTech, wadda wani shirin Majalisar Ɗinkin Duniya zai samar mai suna Covax.

    Da farko ƙasar za ta fara yi wa ma'aikatan lafiya riga-kafin da masu kai agajin gaggawa da shugabanni da mutanen da ke da wasu cutuka da kuma tsofaffi, a cewar shugaban hukumar lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib.

    Ƙasar na fatan samun guda miliyan 42 da za ta ishi ɗaya bisa biyar na jama'arta, a cewarsa.

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ƙaddamar da shirin Covax ne domin taimaka wa ƙasashe marasa ƙarfi saboda fargabar ƙasashe masu arziki za su wawashe ta.

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya faɗa a makon da ya gabata cewa ƙasarsa za ta karɓi riga-kafin ta shirin Covax nan da tsakiyar 2021 bayan ta fara biyan miliyan 283 na kuɗin ƙasar (dala miliyan 19).

    Mutanen da suka harbu da cutar korona a Najeriya sun kai 92,705 sannan an sallami mutum 76,396 daga asibiti bayan an tabbatar sun warke, yayin da 1,319 suka mutu tun bayan ɓullar cutar a ƙasar.