Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin samar da aikin yi ga mutum 774,000

Wannan shafi ne da ke kawo muku abarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sasssan duniya a ranar da muka shiga sabuwar shekarar 2021.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Ƴan sanda sun kama mutum 71 a gidajen rawa kan karya dokar hana yaɗuwar Covid-19

    lagos

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An hana taruwar jama'a da dama saboda hana yaduwar cutar korona

    Ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya sun kai samame wuraren rawa na dare da dama, inda suka kama mutum 71 kan zarginsu da laifin take dokokin hana yaɗuwar Covid-19.

    Ƴan sandan sun ce an kai samamen ne a unguwannin Lekki da Surulere kuma za a tuhumi dukkan waɗanda ake zargin kan laifin take dokokin da gwamnati ta sanya na daƙile yaɗuwar cutar korona.

    Mai magana da yawun ƴan sanda Olumuyiwa Adejobi, ya shaida wa BBC cewa masu zuwa gidan rawar sun take dokar nan da aka sanya ta haramta taruwar mutane da yawa da sake buɗe gidajen rawa da kuma take dokar hana fita da daddare.

    Hukumomi sun ce za su tsaurara kai samamen don tabbatar da cewa an bi dukkan dokokin da aka sanya.

    Kamen na zuwa ne a yayin da Najeriya ke ƙara samun hauhawar masu kamuwa da cutar korona a kullum.

    A ranar Litinin Hukumar Da ke Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta NCDC, ta sanar da cewa san samu ƙarin mutum 1,204 da suka kamu da cutar a ranar ɗaya, irin yawan da ba a taɓa samu ba tun da cutar ta ɓulla.

    A yanzu dai jumullar waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar sun kai 91,351 inda mutum 75,699 suka warke, sai kuma mutum 1,318 da suka mutu.

    Jihar Legas ce cibiyar cutar a Najeriya.

  2. A gudanar da muhimmin zaɓen kujerar sanatoci biyu a Amurka

    Joe Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Sakamakon zaben zai fayyace yadda Biden zai iya cimma manufofinsa a majalisar dokoki idan ya shiga Fadar White House

    Yanzu haka ana gudanar da wani muhimmin zabukan kujerar sanatoci biyu zagaye na biyu a jihar Georgia ta Amurka, jihar da zababben shugaban kasar Joe Biden ya lashe da kuri’u dubu goma sha daya kacal a watan Nuwambar bara.

    Sakamakon zaben dai zai fayyace yadda Biden zai iya cimma manufofinsa a majalisar dokoki idan ya shiga Fadar White House.

    Jam’iyyar Democrats tilas sai ta kwace kujerin sanatocin biyu kafin ta samu iko da majalisar dattijai, kasancewar ko da kujera daya jam’iyyar Republican ta lashe a zaben to zasu haifarwa da Mista Biden cikas wajen aiwatar da manufofinsa a majalisar.

    Daya daga cikin ‘yan takarar ya ce "ina son duk wanda bai je ya kada kuri’arsa ba a Georgia a wannan muhimmin zaben mai cike da tarihi, da ya fita ya je a dama da shi."

  3. MDD ta tura ƴan gudun hijirar Habasha 56,000 Sudan

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta fara tura wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar Habasha dubu hamsin da shida da ke Sudan zuwa wani sabon sansani kasancewar wanda ake da shi ya kusa cika.

    Hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta ce an kafa isassun tantuna ga mutum dubu biyar a sabon sansanin, sannan za a kafa wasu nan da kwanaki masu zuwa.

    Bayanai na cewa 'yan gudun hijirar na ci gaba da tserewa zuwa gabashin Sudan, inda tuni mutum dari takwas suka isa yankin tun farkon sabuwar shekarar nan, inda mutanen ke bayyana irin ukubar da suka sha sakamakon tashe-tashen hankulan da ke ci gaba da wanzuwa.

  4. Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin samar da aikin yi ga mutum dubu 774

    A yau ne gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani shiri na samar da aikin yi ga mutum dubu 774 da ke fadin kasar.

    An dai zabi mutum dubu ɗai-ɗai ne, masu sana'ar hannu a kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomin kasar 774, wadanda za a biya su naira 20,000 na tsawon wata uku.

    Ku latsa alamar lasifikar da ƙasa don sauraron rahoton Ibrahim Isa:

    Bayanan sautiRahoton Ibrahim Isa kan aikin gwamnati na mutum 774,000
  5. Norway ce ƙasar da ta fi sayen motoci masu amfani da lantarki

    Kasar Norway ta zama kasa ta farko da yawan sayen motoci masu amfani da lantarki a shekara ya fi wadanda ke amfani fetur ko man dizal.

    Alkaluma sun nuna cewa kusan sama da kashi hamsin da huɗu cikin dari na sabbin motocin da aka siya a ƙasar Norway bara masu amfani lantarki ne.

    A 2019, kasuwar hada-hadar motocin ta kai kashi arba'in da biyu cikin dari.

    Norway dai ta cirewa motoci masu amfani da lantarki haraji, a wani mataki na kawo karshen motoci masu amfani da fetir zuwa shekarar 2025.

    An cire haraji a kan motocin da ba sa fitar da hayaki sannan aka fitar da wani tsari na kwaɗaitarwa don amfani da motocin ciki har da rangwame na kudin fakin da rage harajin bin wasu tituna.

  6. Ɓarayi sun sace dubban ƙwanƙwalatai a kamfanin barasa

    kwalaben barasa

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A makon da ya gabata ne gwamnati ta ƙaƙaba sabon haramci kan sayar da barasa

    Ƙungiyar kamfanonin da ke samar da barasa a a Afirka Ta Kudu ta yi gargaɗi kan yiwuwar bazuwar barasar jabu a ƙasar bayan da ƴan fashi suka kai hari wani kamfanin yin ta tare da sace dubban ƙwanƙwalatai.

    Shugaban ƙungiyar ta Salba ya yi amannar an sace ƙwanƙwalatan ne don wataƙila a yi amfani da su wajen rufe kwalaben barasar jabu da za a iya samar wa a gida a sayar wa mutane.

    Ƙungiyar ta ce ɗaya daga cikin mambobinta ne ya bayar da sanarwar fashin da aka yi ranar 30 ga watan Disamban da ya gabata a kamfanin da ke birnin Durban mai tashar jiragen ruwa.

    Shugaban Salba, Sibani Mngadi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, ya buƙaci hukumomin da ke yaƙi da miyagun laifuka da su tsaurara wajen magance sayar da barasar jabu da samar da su.

    A makon da ya gabata ne gwamnati ta ƙaƙaba sabon haramci kan sayar da barasa har sai zuwa tsakiyar watan Janairu.

  7. Ma'aikata na zargin gwamnatin jihar Kano da rage musu albashi

    Ma’aikatan gwamnati a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun zargi gwamnati da biyansu albashin watan Disambar bara kan tsohon tsarin mafi ƙarancin albashi na 18,000.

    Wannan na zuwa ne kasa da makonni uku da kungiyar ƙwadago a jihar ta gargadi gwamnatin ta Kano da kar ta kuma datse wa ma'aikatan albashinsu na watan Disambar 2020, inda har ta yi barazanar tafiya yajin aiki idan aka sake taɓa musu albashi.

    To sai dai gwamantin jihar Kanon ta ce yanke albashin ma’aikatan ya biyo bayan yadda cutar korona ta shafi kudaden da jihar ke samu ne, tare da tattalin arzikin Najeriya, shi ya sa ba za ta iya biyan ma’aikatan kan mafi karancin albashin na naira 30,000 ba.

    Ga dai rahoton Khalifa Shehu Dokaji:

    Bayanan sautiRahoton Dokaji kan biyan ma'aikata albashi kan tsohon tsari
  8. Ba mu yi ƙarin kuɗin wutar lantarki ba - NERC

    Hukumar samar da hasken wutar lantarki a Najeriya ta nemi kafofin watsa labarai a ƙasar cewa su janye rahotannin da suka buga cewa hukumar ta yi ƙarin kudin wuta da kashi hamsin cikin dari.

    Hukumar a wani sako da ta wallafa a shafinta Twitter ta ce karin da aka yi bai wuce na naira biyu zuwa hudu ba; kana kuma ya hau kan wasu rukunoni ne.

    Hukumar kula da harkokin wutar lantarki a Najeriya ta Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC) ta ce ƙarin kuɗin wutar da ta yi bai shafi waɗanda ke shan wutar a matakin D da E ba.

    Waɗanda ke kan kan layin na D da E na samun lantarki ne ta ƙasa da awa 12 a kowace rana kuma hukumar ta ce ƙarin na kashi 50 cikin 100 bai shafe su ba.

    Hukumar ta yi ƙarin bayanin ne a matsayin martani ga rahoton da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa ƙarin zai shafi kowa da kowa, saɓanin wanda ta yi a watan Nuwamban 2020, inda aka kasa biyan kuɗin gida-gida.

    Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, NERC ta ce har yanzu na waɗanda ke kan matakin D da E za su ci gaba da samun rahusa tun bayan ƙarin da ta yi.

    Sai dai a yanzu an ƙara naira biyu kan kowane KW guda ɗaya, inda waɗanda ke kan matakin A da B da C

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya tambayi Malam Ibrahim Sani Shawai, shugaban sashen hulda da jama’a da watsa labarai na kamfanin rarraba hasken wutar lantarki a jihohin Katsina da Kano da kuma Jiagawa, kan ko ina gaskiyar rahotanni da ke yawo cewa sun kara kudin wutar lantarkin?

    Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron hirar:

    Bayanan sautiRahoton Elleman kan ƙarin kuɗin wutar lantarki
  9. Rikicin Habasha: An rusa masallacin da sahabbai suka gina

    Masallacin Najashi

    Asalin hoton, Kafofin Sada zumunta

    Gwamnatin Habasha ta yi alkawarin gyara wani masallaci da ya shafe daruruwan shekaru, wanda aka rusa a rikicin watan jiya a yankin Tigray.

    Rahotanni sun ce an harbawa masallacin Najashi bom. An lalata hasumiyar masallacin da kuma kaburburan wasu jagororin Musulunci.

    Gwamnati ta ce za ta kuma ta gyara wata coci mai makwaftaka da masallacin, wacce ita ma aka lalata.

    Mazauna yankin sun yi amanna cewa sahabban Manzon Allah SAW da suka yi hijira zuwa Habasha su ne suka gina masallacin.

    Sun gujewa cuzgunawa ne da cin zarafin da mutanen Makka suke yi musu a lokacin, kuma Najashi ya ba su mafaka a masarautar Aksum a lokacin.

    Mazauna yankin sun yi amanna cewa awai kaburburan sahabbai 15 a wurin da aka lalata.

    Sun kuma yi imani da cewa masallacin ne mafi tsufa a Afirka, sai dai wasu sun ce wani masallaci a Masar ya fi shi dadewa.

  10. Saudiyya da Qatar sun sasanta

    Saudiyya da Qatar

    Asalin hoton, Reuters

    Shugabannin ƙasashen yankin Tekun Fasha sun rattaba hannu kan wani daftari yayin wani taron ƙoli a Saudiyya da nufin kawo karshen rikicin difilomasiyya tsakanin ƙasashen da kuma Qatar.

    Lokacin da suka isa wurin taron Sarkin Qatar Sheikh Tamin bin Hamad al-Thani da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, sun rungumi juna a wani mataki na sasantawa.

    Wannan ne karon farko da Sheikh Tamim ya halarci taron tun bayan da Saudiyya da Daular Larabawa da Bahrain suka ƙaƙaba wa ƙasarsa takunkumi kan zarge-zargen goyon bayan 'yan ta'adda.

    'Yar ƙaramar ƙasar mai arzikin man fetur ta musanta zargin sannan ta yi watsi da jerin sharuɗɗan da maƙwabtan nata suka gindaya mata, ciki har da katse hulɗa da Iran da kuma gidan talabijin na Aljazeera da take gudanarwa.

    Nan gaba za a sanya hannu kan yarjejeniya ta ƙarshe wadda da za ta warware taƙaddamar baki ɗaya.

  11. Gobara ta kashe mutum 134 a Kano a 2020

    Gobara

    Asalin hoton, AFP

    Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce mutum 134 ne suka rasa rayukansu a 2020 sakamakon gobara 786 da suka tashi a wuri daban-daban a jihar.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Saidu Muhammad, mai magana da yawun hukumar, yana bayyana cewa kazalika an rasa dukiyar da ta kai naira miliyan 635 a tsawon shekarar.

    Haka nan, hukumar ta ceto ran mutum 1,077 da kuma dukiya naira biliyan 2.56.

    "Akasarin gobarar sun faru ne sakamakon ganganci wurin aiki da tukunyar gas da amfani da wayoyin lantarki marasa inganci," a cewarsa.

    Ya ƙara da cewa hukumar za ta ƙara horas da ma'aikatanta guda 350 a 2021 domin kyautata aiki kuma ya shawarci magidanta da "su riƙa kulawa da kyau yayin amfani da wuta" domin guje wa tashin gobara.

  12. Yanzu na gamsu za mu yi nasara a yaƙi da ta'addanci - Sanata Ali Ndume

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku ji hira da Ali Ndume

    Shugaban kwamiitin sojojin ƙasa na Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ali Ndume, ya faɗa wa BBC cewa yanzu suna da ƙwarin gwiwar samun nasara a yaƙi da ta'addanci a ƙasar saboda ƙarin kayan yaƙi da sojoji suka samu.

    Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce binciken da ya yi ya nuna cewa dakarun sojan sama na Najeriya sun samu sabbin jiragen helikwafta fiye da 20.

    Ndume na cikin waɗanda ke yawan sukar yadda gwamnatin jam'iyyarsu ta APC ke tunkarar yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a lokuta daban-daban a jiharsa ta Borno da yankin arewa maso gabas.

    Ya ce kiran da suka daɗe suna yi na ƙara yawan sojoji ya samu karɓuwa, "yanzu za a ɗauki mutum kusan 8,000 saɓanin 4,000 zuwa 5,000 da ake ɗauka".

  13. Osinbajo na miƙa wa Buhari rahoton tattalin arziƙi

    Osinbajo da Buhari

    Asalin hoton, @NGRPresident

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi rahoton tattalin arziki daga Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo game da shirin gwamnatinsu na haɓaka rayuwar 'yan ƙasar.

    Shugabannin biyu sun haɗu ne a Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock Villa a yau Talata, inda Buhari ya karɓi rahoto kan shirin Economic Sustainability Plan.

    Gwamnati ta ce ta ƙirƙiri shirin ne domin rage wa mutane raɗaɗin da annobar cutar korona ta saka su a ciki.

    Wannan na zuwa ne yayin da Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo ya ce za a fara aiwatar da shirin ɗaukar mutum 774,000 ɗauki a yau Talata.

    Gwamnati ta tsara ɗaukar mutum 1,000 aiki daga kowace ƙaramar hukuma 774 na ƙasar domin rage yawan matasa marasa aikin yi a ƙasar.

    An sha ce-ce-ku-ce tsakanin Mista Keyamo da 'yan Majalisar Wakilan Najeriya game da wanda ya kamata ya aiwatar da shirin, inda suke neman a ba su wani kaso na mutanen da za a ɗauka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. An sake ƙara kuɗin lantarki a Najeriya da kashi 50 cikin 100

    Lantarki

    Asalin hoton, Nigeria Electricity

    Hukumar kula da farashin wutar lantarki a Najeriya ta Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC) ta amince da fara aiki da wani sabon ƙarin kuɗin wutar da kashi fiye da 50 cikin 100.

    Wannan na zuwa ne wata biyu kacal da yin irin wannan ƙarin kuma na yanzu zai shafe na watan Nuwamba da aka yi.

    Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito wata takardar umarni da sabon shugaban hukumar mai suna Injiniya Sanusi Garba ya sanya wa hannu ranar 30 ga watan Disamba na cewa ƙarin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2021.

    Hukumar ta ce ta yi la'akari ne da tashin farashin kaya na kashi 14.9 cikin 100 a watan Nuwamba, da faɗuwar darajar naira zuwa N379 kan dala ɗaya ya zuwa watan Disamba, da ƙarfin samar da wutar lantarkin, kafin ta yi ƙarin kuɗin.

    Wannan ƙarin zai shafi kowane aji na masu amfani da wutar, saɓanin na Nuwamba, wanda bai shafi masu shan wutar a mataki mafi ƙarancia ba.

    Ƙarin da aka yi a watan Satumba na - iya kuɗinka iya shagalinka - ya jawo tayar da jijiyoyin wuya daga 'yan ƙasa da kuma ƙungiyoyin ƙwadago, abin da ya sa gwamnati ta jingine shi kuma ta shiga tattaunawa da gamayyar ƙungoyiyin.

    Sai dai an ƙaƙaba wa mutane ƙarin ya zuwa watan Nuwamba bayan kamfanonin lantarkin sun rage farashin ga masu samun wutar awa 12 a kowace rana.

    A gefe guda kuma, waɗanda suke samun ta ƙasa da awa 12 a kowace rana, ba a yi musu ƙarin ba, in ji hukumar NERC.

    • Kuna iya karanta yadda aka karkasa tsarin biyan kuɗin wutar a nan
  15. Labarai cikin minti ɗaya

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Minti Daya da BBC na Safe 05/01/2021
  16. Gwamnatin Kamaru ta dakatar da ganawa tsakanin jami'an gwamnati na shekara-shekara

    Wa niu yaunkri na daƙile yaɗuwar cutar korona, gwamnatin Kamaru ta dakatar da gaisuwar al'ada da aka saba yi tsakanin jami'an gwamnati.

    Gwamnati ta dakatar da ganawa tsakanin jakadun da ke wakiltar ƙasashensu a Kamaru da kuma wasu manyan jami’an hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Bugu da kari har da Majalisar Ministoci da sauran jami’an ɓangarori zantarwa da na shari’a na cikin gida.

    Bisa al’ada a duk farkon sabuwar shekara jami’an diplomasiyya kan tattauna da Shugaban kasa ta hanyar gabatar da jawabai dangane da al’amuran da duniya ta fuskanta a cikin shekarar da ta gabata da yadda ake tunkarar matsalolin da suka addabi duniyar domin a samu hanyoyin warwaresu.

  17. Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kashe sojojin Faransa a Mali

    Sojojin Faransa

    Asalin hoton, Getty Images

    Reshen ƙungiyar Al-Qaeda na ƙasar Mali mai suna Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) ta yi iƙirarin cewa ita ce ta kai harin bam da ya yi sanadiyyar kashe sojojin Faransa guda biyu ranar Asabar.

    Magoya bayan ƙungiyar sun yaɗa saƙon iƙirarin ne a dandalin zumunta na Telegram.

    Sojan Faransar biyu sun mutu ne a Mali lokacin da bam ya tashi da abin hawansu a Menaka.

    Dakarun sun je garin ne domin tattara bayanai, a cewar fadar shugaban ƙasar Faransa.

    Hatsarin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu sojojin uku sun mutu ta irin wannan yanayi.

    Faransa na da dakaru 5,100 a yankin Sahel da ke yaƙi da 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi tsawon kusan shekara 10.

    Ya zuwa yanzu an kashe sojan Faransa 50 a yankin na Sahel.

  18. Amotekun ta kama mutum 120 da zargin fashi a Jihar Ondo

    Amotekun

    Asalin hoton, Others

    Sabuwar rundunar hukumar tsaro ta Amotekun reshen Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta kama mutum 120 waɗanda ake zargi da aikata laifuka.

    Da yake magana da manema labarai a birnin Akure, kwamandan hukumar Adetunji Adeleye ya ce an kama mutanen ne a lokaci 15 yayin da suke aikata fashi da makami, a cewar rahoton jaridar Vanguard.

    Ya ce: "Tun bayan fara aikin Operation Clean-Up wata ɗaya da ya wuce, mun kama mutum kusan 120 kuma zaman lafiya na dawowa a jihar.

    "Wasu daga cikin miyagun an miƙa su ga 'yan sanda, wasu kuma wurin NSCDC, wasu kuma DSS domin bincike da gurfanarwa a gaban kotu."

    Ya ce sun fara wannan aiki ne da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro bayan zanga-zangar EndSars kuma hakan ya sa sun samu nasarar kama mutum 15 da suka aikata fashi a jihar Ondo cikin wata ɗaya.

  19. Yau za a ci gaba da tattaunawar sulhu da ƙungiyar Taliban

    Taliban

    Asalin hoton, Reuters

    Tawagar wakilan gwamnatin Afghanistan ta shirya barin Kabul zuwa Qatar domin fara zagaye na biyu na tattaunawa da 'yan Taliban da nufin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi na shekara da shekaru.

    An soma tattaunawar cikin watan Satumba a birnin Doha amma kuma yaƙi ya ci gaba da ƙazanta.

    Gwamnatin Afghanistan na neman a tsagaita wuta amma kungiyar Taliban ta ce za a yi sulhu ne kaɗai idan aka samu ci gaba a tattaunawar.

    Masu taimaka wa zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden sun bayyana ƙarara cewa suna son ganin muhimmin ci gaba idan Amurkar za ta janye ragowar dakarunta nan da watan Mayu.

  20. Cutar korona a Najeriya: Mutum bakwai sun mutu, 1,204 sun kamu ranar Litinin

    Cutar korona

    Asalin hoton, NCDC

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 1,204 da suka kamu da annobar korona ranar Litinin.

    Ƙididdigar da hukumar ta NCDC ta wallafa a shafinta na intanet ta bayyana cewa cikin sa'a 24 da suka gabata, mutum bakwai ne suka mutu sanadin cutar a ƙasar.

    Jihar Legas ce ke da kaso mafi yawa na mutanen da suka kamu cikin kwana ɗayan da mutum 654 sai Abuja, babban birnin Najeriyar da mutum 200.

    Jihar Plateau na da mutum 60, Kaduna 54, Kano kuma 40. A jihar Rivers, mutum 30 aka gano sun kamu da cutar a ranar Litinin inda a Edo aka samu ƙarin mutum 28 masu fama da annobar.

    Nassarawa na da mutum 25, Kebbi kuma mutum 19 yayin da Bauchi ke da mutum 18. Oyo 13, Akwa Ibom 12 sai Bayelsa mai mutum 11.

    A Ogun ma mutum 11 aka gano sun kamu da koronar inda Delta ke da mutum 9 sai Abia mai mutum 8.

    Sauran jihohin da aka samu ƙarin masu ɗauke da cutar cikin sa'a 24 da ta wuce, akwai Benue da mutum 5, Imo na da mutum 3 sai Borno mai mutum 2 yayin da Sokoto da Osun aka samu mutum 1 kowannensu.

    Hukumar NCDC ta ce a ranar Litinin kaɗai, mutum 655 ne suka ware daga cutar har ma an sallame su daga asibiti.

    A jumulla, a Najeriya an samu mutum 91,351 da suka kamu da cutar sai mutum 75,699 da suka warke da kuma mace-mace sau 1,318 tun bayan ɓullar cutar a ƙasar.