Cutar korona a Najeriya: Mutum tara sun mutu, 917 sun kamu ranar Lahadi

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce mutum 917 ne suka kamu da cutar korona a kasar ranar Lahadi.
A cewar bayanan da NCDC ta wallafa a shafinta na intanet, mutum tara ne cutar ta yi ajalinsu cikin sa'a 24 da suka gabata.
Daga cikin karin mutanen da suka kamu da cutar, akasarin su sun fito ne daga Abuja, babban birnin kasar inda aka samu mutum 222.
Jihar Legas ce ta biyu da mutum 214 sai Kaduna wadda take ta uku a jadawalin da mutum 119. Akwai kuma jihar Plateau da aka samu mutum 92.
A Nassarawa, an samu mutum 50 da suka kamu da korona cikin kwana daya da ya gabata. A Oyo kuma, mutum 41 aka gano sun kamu da cutar cikin sa'a 24 da ta wuce.
Adamawa na da mutum 33 sai Ondo mai mutum 32. Abia (28), Ogun (19), Rivers (17), Kano (16).
Yobe (14), Edo (8), Anambra (6), Ekiti (5) sai Jigawa mai mutum daya.
Hukumar ta NCDC ta ce a jumulla, cutar ta korona ta harbi mutum 90,080 a Najeriya inda aka sallami mutum 75,044 daga asibiti bayan sun warke daga cutar yayin da adadin mutum 1,311 ne suka mutu tun bayan da cutar ta bulla a kasar.
