Wannan shafi ne da ke kawo muku abarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sasssan duniya a ranar da muka shiga sabuwar shekarar 2021.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Imam Saleh
Rufewa
Bayani kan maƙala
Marubuci, Imam Saleh
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu ta wannan shafi a nan muka zo ga ƙarshen kawo muku labaran duniya kai tsaye a wannan rana ta Litinin.
Da fatan za ku kasance tare da mu gobe Laraba domin kawo muku wasu sabbin labaran.
Za ku iya dubawa ƙasa, domin samun dukkanin labaran da muka wallafa tun daga safiyar wannan rana har zuwa yanzu.
Imam Saleh ke cewa mu kwana lafiya, daga nan sashen Hausa na BBC.
Masana sun fara nazarin sabon nau'in cutar korona da ya ɓulla a Afrika ta kudu
Asalin hoton, Coronavirus
Masana kimiyya na nazarin wani nau’in kwayar cutar korona da aka fara ganowa a Afrika ta Kudu domin ganin ko zai iya takaita tasirin alluran riga-kafi.
Kwararru sun ce sabn nau'in cutar na rikida sosai ta yadda zai sa sa karancin jin magani na tasirin allurar riga-kafi da ke bunkasa garkuwar jiki.
Ana jin cutar tafi sauran yaduwa amma babu tabbaci ko tana haifar da rashin lafiya mai tsanani fiye da nau'in da aka sani.
Wakilin BBC ya ce masanan na gudanar da gwaje-gwaje na gaggawa kuma sun ce za su samu sakamako cikin 'yan makonni masu zuwa”.
Amurka ta nuna takacinta kan hana miƙa mata mai Wikeleaks da kotu ta yi
Asalin hoton, Getty Images
Ma’aikatar shari’a ta Amurka tace ta ji matukar takaici kuma zata daukaka kara kan hukuncin da wata kotu a Burtaniya ta yanke na cewa ba za a mika ta mai shafin kwarmata bayanai na Wikileaks Julian Assange ba.
Mista Assange yana fuskantar tuhume-tuhume da dama ciki har da zargin wallafa wasu bayanan sirri na soji da na diflomasiyya.
Alkalin kotun ya ce ya damu game lafiyar kwakwalwar Mista Assange da kuma yiwuwar zai iya kashe kansa a gidan yarin Amurka.
Lauyan Mista Assange ya ce lokaci ya yi da sauran kasashe za su hada hannu don kare mutumin da yace ana musguna masa, saboda kawai ya wallafa wasu bayanai”.
An fara bincikar tsohon shugaban Afrika ta tsakiya kan yunƙurin hamɓarar da gwamnati
Asalin hoton, Getty Images
Masu gabatar da kara a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun fara gudanar da bincike kan tsohon shugaban kasar Francois Bozize, inda suke zarginsa da ayyukan tayar da zaune tsaye da kuma ingiza ‘yan tawaye.
A watan da ya gabata, gwamnatin ta zargi Bozize da yunkurin juyin mulki yayin da gamayyar ‘yan tawaye suka yi tattaki a Bangui, babban birnin kasar, gabanin babban zaben kasar.
Mista Bozize, wanda aka haramta masa tsayawa takara a zaben, ya musanta zargin amma ya ce yana goyon bayan 'yan tawayen.
Wakilin BBC yace ‘yan tawayen Seleka sun yi yukurin karbe iko da Bangui, bayan da aka ki amincewa da takarar Bozize a zaben Shugaban Kasar da aka gudanar.
Ƴan tada ƙayar bayan sun kai sabon hari a Mozambique
Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga arewacin Mozambique na cewa ƴan tayar da ƙayar baya sun kai hari wata tashar sarrafa iskar gas wanda kamfanin makamashi na Faransa ke gudanarwa dake wani ƙauye.
Jami’an tsaron sun ce sun yi nasarar fatattakar ƴan bindigar bayan gumurzun da aka kwashe sa’o’i ana yi a ƙauyen Quitunda mai nisan kilomita daya daga filin jirgin kamfanin.
A makon da ya gabata, kamfanin Total ya kwashe wasu ma’aikata sakamakon hare-haren masu ikirarin jihadi da ke kusa da inda kamfanin yake.
Boko Haram ta kashe mutane a yankin Arewa mai nisa na Kamaru.
Asalin hoton, AFP
Wasu da ake zargin ƴan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane uku a yankin kan iyaka na Kiliari, Nguetchewe da ke yankin Arewa mai Nisa na Kamaru.
A cewar basaraken gargajiya kuma magajin garin Mozogo, Mahamat Chetima Abba, maharan sun kai harin ne da safiyar Litinin inda suka kashe mambobin wata ƙungiyar kare kai.
Ya ce masu iƙirarin jihadin sun tsallaka iyaka ne daga Najeriya.
Ita dai ƙungiyar Boko Haram ta yawaita kai hare-hare a yankin Arewa mai Nisa na Kamaru a baya bayan nan.
Ko da a ranar Asabar, sai da maharan suka kashe wani malamin makaranta a ƙauyen Ouzal da ke Mayo Moskota.
Yawaitar hare-haren na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Shugaba Paul Biya ya shaida wa ƴan Kamaru a cikin jawabinsa na sabuwar shekara cewa jami'an tsaron ƙasar sun yi matuƙar rage tasirin ƴan tada ƙayar baya.
Kotu ta hana yin gwajin budurci a Pakistan
Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Pakistan ta bayyana cewa gwajin tabbatar da budurci abu ne da baya bisa ka’ida kuma ya saɓawa kundin tsarin mulki na kasa.
Babbar Kotun da ke birnin Lahore ta ce yin gwajin ba shi da wani amfani a shari'ar fyade da cin zarafin mata.
Alkalin ya umarci gwamnatin Pakistan da ta ɗauki matakai don tabbatar da cewa ba a kara aiwatar da gwajin ba.
Masu rajin kare hakkin dan adam sun dade suna neman a kawo karshen gwajin budurci inda suka ce ba shi da wani tushe a kimiyyance.
Zulum ya rattaba hannu kan kasafin kudin Borno na 2021
Asalin hoton, ISAH GUSAU
Bayanan hoto, Gwamna Zulum
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya rattaba hannu kan kasafin kudi na shekarar 2021 wanda majalisar dokokin jihar Borno ta amince da shi.
Sai dai an ƙara kasafin daga Naira Biliyan 208, zuwa Biliyan 248 biliyan,da zummar samar da masana'antar sarrafa roba, da kuma katafaren otal na ƙasa da kasa ga jihar.
Yayin da yake sanya hannu kan kasafin a ranar a dakin taro na gidan gwamnati da ke Maiduguri, gwamna Zulum ya umarci dukkan ma’aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati da su bi ka’idojin kasafin.
Ya kuma umurci mambobin majalisar zartarwarsa su duƙufa wajen hidimtawa al'ummar jihar wajen samar musu da ayyukan raya ƙasa da aka tanada a cikinsa.
Gwamnan ya bayyana cewa a wannan shekarar, 2021, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko kan tsaro, da ilimi, da Kiwon lafiya, da noma, da samar da ruwan sha da sake gina wuraren da yan tada ƙayar baya suka lalata.
Iran ta ƙwace jirgin ruwan Koriya ta kudu
Asalin hoton, Reuters
Kafofin watsa labaran Iran sun ce dakarun yuyin-yuya halin ƙasar sun kama wani jirgin ruwa ɗauke da tutar Koriya ta Kudu a yankin tekun fasha.
Tun da farko an bayar da rahoton cewa jirgin ya sauya hanya ba tare da bayani daga hanyar da ya bi tsakanin Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa ba.
Wasu majiyoyin Iran din sun ce jirgin na ɗauke da sinadarai masu nauyin tan dubu bakwai da dari biyu.
Ranar Talata za a ƙaddamar da shirin ɗaukar 'yan Najeriya 774,000 aiki
Asalin hoton, @NGRPresident
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin ƙaddamar da shirin ɗaukar mutum 774,000 ɗauki a faɗin ƙasar.
Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.
"Shugaba Muhammadu Buhari ya sahale ƙaddamar da shirin Special Public Works na ɗaukar 'yan Najeriya marasa aikin yi guda 774,000 aiki," in ji ministan.
Ya ƙara da cewa "za a fara aikin ne daga gobe Talata, 5 ga Janairun 2020. Duka ofisoshin hukumar ɗaukar aiki (NDE) na jihohi sun shirya tsaf domin fara shirin."
Gwamnati ta tsara ɗaukar mutum 1,000 aiki daga kowace ƙaramar hukuma 774 na ƙasar domin rage yawan matasa marasa aikin yi a ƙasar.
An sha ce-ce-ku-ce tsakanin Mista Keyamo da 'yan Majalisar Wakilan Najeriya game da wanda ya kamata ya aiwatar da shirin, inda suke neman a ba su wani kaso na mutanen da za a ɗauka.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, Kotu ta umarci a ci gaba da tsare Omoyele Sowore a gidan yarin Kuje
Asalin hoton, Omoyele Sowore
Wata kotun majistire a Abuja ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare Omoyele Sowore, ɗan gwagwarmayar nan kuma tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya, a Gidan Gyara Hali na Kuje da ke Abuja.
'Yan sandan birnin Abuja sun gurfanar da mawallafin jaridar Sahara Reporters ɗin ne tare da wasu mutum huɗu a gaban kotu saboda zargin yin taro ba tare da izini ba da kuma uzura wa mutane.
Dukkanin mutanen sun musanta zargin da ake yi musu, kuma za a ci gaba da tsare su har zuwa gobe Talata domin sauraron ƙudirin neman beli.
An kama Sowore ne bayan ya jagoranci wata zanga-zanaga ranar Alhamis a Abuja.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Kotu ta hana tasa ƙeyar Julian Assange zuwa Amurka
Asalin hoton, Reuters
Kotu a birnin Landan ta yi hukuncin cewa ba za a tasa ƙeyar Julian Assange ba zuwa Amurka.
Alƙalin kotun ya yi watsi da buƙatar ce saboda damuwar da ake da ita kan lafiyar Mista Assenge da kuma fargabar zai iya kashe kansa a Amurka.
Ana neman mai shekara 49 ɗin ne sakamakon wallafa dubban bayanan sirrrin gwamnati a 2010 da 2011.
Amurka ta ce bayanan da ya saki sun karya doka kuma sun saka rayuwar mutane cikin haɗari. Mista Assenge ya ƙalubalanci tasa ƙeyar tasa, yana mai cewa maƙarƙashiya ce irinta siyasa.
Amurka na da kwana 14 domin ɗaukaka ƙara kuma ana sa ran za ta yi hakan.
Yanzu za a mayar da Assenge gidan yarin Belmarsh, inda ake tsare da shi, sannan a fara yunƙurin neman belinsa ranar Laraba.
Ministar Harkokin Mata ta Najeriya Pauline Tallen ta warke daga korona
Asalin hoton, @PaulineKTallen
Ministar Harkokin Mata ta Najeriya Pauline Tallen ta warke daga cutar korona bayan ta killace kanta sakamakon kamuwa da cutar.
Ministar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar yau Litinin, tana mai shawartar 'yan Najeriya da su ci gaba da bin dokoin kariya daga cutar.
Tallen wadda gwaji ya nuna ta warke a jajiberin sabuwar shekara, ta ce ta yi murna tare da roƙon al'umma su kiyaye kansu da iyalansu.
Misis Tallen ta bayyana kamuwa da cutar ne a ranar 27 ga watan Disamba cikin wani saƙon Twitter, inda ta ce sauran iyalan gidanta ba su kamu ba bayan gwajin da suka yi.
Atiku na zargin Buhari da karya masa harkokin kasuwanci
Asalin hoton, AFP
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya sayar da hannun jarinsa a kamfanin Integrated Logistics Services Limited (Intels), yana mai zargin gwamnatin Buhari da neman karya kamfanin.
Mai magana da yawun jigon na jam'iyyar adawa ta PDP kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, Paul Ibe, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.
Ya ce an tilasta wa Atiku ɗaukar matakin ne saboda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari "ta matsu ta karya kamfanin" tun 2015.
Atiku ya kafa kamfanin na Intels tare da wani ɗan ƙasar Italiya mai suna Gabriele Volpi, wanda yake yi wa kamfanoni ayyuka musamman na man fetur da iskar gas.
"Atiku ya sha sayar da hannun jarinsa na kamfanin Intels a baya amma abin ya yi ƙamari ne daga 2015 saboda burin wannan gwamnatin shi ne ta karya kamfanin da ke samar wa dubban 'yan Najeriya aiki kawai saboda siyasa," in ji sanarwar.
"Ya sayar da hannun jarinsa na Intels kuma ya mayar da kuɗinsa wasu ɓangarorin na tattalin arziki domin samun riba da samar da ayyukin yi. Ya kamata a riƙa bambanta siyasa da kasuwanci."
A shekarar 2010 ne kamfanin ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da hukumar kula da gaɓar ruwan Najeriya ta Nigerian Ports Authority (NPA), inda zai riƙa karɓar haraji a madadin hukumar game da wasu daga cikin ayyukanta.
Sai dai a 2017 Ministan Shari'a Abubakar Malami ya ce yarjejeniyar ta saɓa wa doka kuma gwamnati ta soke ta.
Kazalika, an sha zargin kamfanin da ƙin biyan haraji da kuma gaza biyan dala miliyan 48 ga gwamnatin Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An kashe sojojin Aljeriya uku a yaƙi da ta'addanci
Ma'aikatar Tsaro ta Aljeriya ta ce an kashe sojojinta uku a wani yaƙi da ta'addanci da ta ƙaddamar a Tipaza da ke arewacin ƙasar.
An fara aikin ne ranar Asabar yayin da "aka kashe soja biyu da 'yan ta'adda huɗu", a cewar ma'aikatar.
An sake kashe wani soja ranar Lahadi tare da wasu 'yan bindigar biyu.
Ta ƙara da cewa an ƙwace bindiga ƙirar Kalashnikov guda biyu da harsasai daga hannunsu
Gwamnati ta ƙaddamar da shirin ne domin zaƙulo tare da kawar da 'yan bindiga daga yankin Tipaza.
Tuni maƙwabtanta irinsu Nijar da Mali suke fama da 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi, waɗanda hukumomi suka zarga da kashe mutum fiye da 100 a Jihar Tillaberi a ƙarshen makon da ya gabata.
Miliyoyin ɗalibai sun koma makaranta a Kenya bayan wata tara
Asalin hoton, Reuters
Miliyoyin yara ne ke komawa makaranta a ƙasar Kenya yayin da aka sake buɗe sakandare da firamare bayan wata tara.
'Yan shekarar ƙarshe sun ci gaba da karatu a azuzuwa a watan Oktoba kafin su yi hutun sabuwar shekara.
Ma'aikatar lafiya ta gindaya wasu sharuɗɗa domin daƙile yaɗuwar cutar korona, wadda ta jawo rufe makarantun tun farko.
Daga ciki har da shawartar malamai da su yi amfani da duk wani fili da suke da shi, ciki har da karatu a ƙarkahsin bishiyoyi domin bayar da tazara.
An umarci iyaye su saya wa yaransu takunkumi, ita kuma gwamnati ta yi alƙawarin raba wa marasa ƙarfi takunkumin kyauta.
Malaman da suka zarta shekara 58 da haihuwa da kuma waɗanda ke da wasu cutuka, an nemi su yi aiki daga gida ko kuma su koyar a buɗaɗɗun wurare.
Shugaban Ƙasa Uhuru Kenyatta ya tsawaita dokar hana fita ta dare har zuwa wata uku nan gaba.
Jumillar mutum 96,802 ne suka kamu da cutar a Kenya tare da 1,685 da suka mutu daga cikinsu, a cewar ma'aikatar lafiya.
Mutanen da ake zargi da fashi sun tsere daga ofishin 'yan sandan Edo
Asalin hoton, AFP
Wasu tsararru da ake zargi da laifukan da suka haɗa da fashi da garkuwa da mutane sun gudu daga ofishin 'yan sanda a Jihar Edo.
Jaridar Premium Times ta ruwaito mutanen sun tsere ne daga caji ofis na sashen binciken manyan laifuka wato SCID a hedikwatar rundunar da ke babban birnin jihar, Benin.
Rahoton ya ce an tsare duka 'yan sandan da suke a bakin aiki lokacin da lamarin ya faru bisa umarnin Kwamishinan 'Yan Sanda Johnson Kokumo.
Duk da cewa babu cikakken adadin waɗanda suka tsere, majiyoyi sun bayyana cewa ana tsare da mafi yawansu ne kan laifin fashi da kuma garkuwa da mutane waɗanda aka kama su cikin wata biyu da suka wuce bayan zanga-zangar EndSars.
Wani ɗan sanda da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce lamarin ya faru ne a daren Asabar.
Sai dai Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Ajala Ayoola, ya ce ba a daren Asabar abin ya faru ba, yana mai cewa a jira bayani a hukumance.
Kwamishinan 'yan sandan da kuma kakakin rundunar ba su amsa kiraye-kirayen da jaridar ta yi musu ba game da labarin.
Ronaldo ya zama na biyu da ya fi kowa cin ƙwallo a tarihi
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Portugal Christiano Ronaldo ya zarta Pele wurin zira ƙwallaye a raga, inda ya zama na biyu a tarihin adadin ƙwallayen da wani ɗan wasa ya ci.
A jiya Lahadi ne ya ci wa Juventus ƙwallo biyu sannan ya bayar aka ci ɗaya, ƙwalonsa ta 14 kenan cikin wasa 11 kacal da ya buga a gasar Serie A ta bana.
Kazalika, ƙwallo ta 758 kenan da ɗan wasan mai shekara 35 ya zira a sana'ar wasansa ta kulob da ƙasarsa kuma saura ƙwallo ɗaya tal ya kamo Josef Bican a matsayin wanda ya fi cin ƙwallaye da 759.
Haka nan ya zarta Lionel Messi wanda ke da 742, sai dai Ronaldo ya fi Messi buga wasa da guda 200.
Josef Bican ya kafa nasa tarihin ne a shekarun 1930 zuwa 1950 lokacin da ya buga wasa a ƙungiyoyin Slavia Prague da FC Vítkovice da Rapid Vienna da Admira da FC Hradec Králové.
A baya-bayan nan ne Messi ya zarta Pele a matsayin ɗan wasan da ya fi zira ƙwallaye a ƙungiya ɗaya da 644.
An sake zaɓar Nancy Pelosi Kakakin Majalisar Wakilan Amurka
Asalin hoton, Getty Images
Yan Majalisar Wakilain Amurka sun sake zaar Nancy Pelosy, yar jam'iyyar Democrat, a matsayin Kakakin Majalisar.
An gudanar da zaen a matakai daban-daban bisa bin a'idojin da aka gindaya na yai da annobar korona.
Da ma dai an yi hasashen Pelosi za ta sake yin nasara duk da koma-bayan da 'yan Democrat suka samu bayan zaen watan Nuwamba da aka gudanar.
Waɗanda suka mutu a harin Nijar sun kai 100
Jami'ai a Jamhuriyar Nijar sun ce kimanin mutum 100 ne suka mutu a wani hari da aka kai wasu kauyuka biyu a kasar, wanda ake zargin masu ikirarin jihadi da kaiwa.
Wani basaraken gargajiya ya ce kusan mutum 70 aka kashe a kauyen Cho-ma Bangu sannan aka kashe 30 a Zaro-madare.
Ya ce gwamman masu ikirarin jihadi ne suka kutsa yankin a kan babura.
Kauyukan suna yankin Jihar Tillaberi kusa da iyakar kasar da Mali, wurin da ya yi fice da ayyukan masu ikirarin jihadi.
An aika wasu dakarun gwamnati na musamman zuwa yankin.