Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe makarantu da wuraren shaƙatawa

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Korona a Najeriya: Mutum uku sun mutu, 501 sun kamu ranar Lahadi

    Corona

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 501da suka kamu da cutar korona a ranar Lahadi.

    Kazalika, ƙarin wasu mutum uku sun mutu sakamakon cutar.

    Jihar Legas ce ke da adadi mafi yawa da mutun 218, yayin da Abuja ke bi mata da mutum 112.

    Koronar ta kuma kama mutum 53 a Kaduna, sai Plateau mai mutum 24, sai Katsina mai 21.

    Jihar Kano na da 16 sai kuma Yobe mai mutum 14. A Ondo an samu mutum 10 sai Ogun 9, Edo 7, Bayelsa 5.

    Jihohin Rivers da Borno na da 4-4, yayin da Osun da Ekiti suka rufe jadawalin da mutum 2-2 kowannensu.

    A jimillance adadin mutunen da cutar ta kama tun daga bullarta zuwa yanzu sun kai 78,434, yayin da 68,303 suka warke aka kuma samu asarar rayuka 1,221.

  2. Fatan kun wayi hantsi lafiya

    Ku biyo ni Umar Mikail a wannan shafi domin karanta labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya a Nijar da maƙwabtansu.

    Barkanku da wannan lokaci tare da fatan an kammala hutun ƙarshen mako lami lafiya.