Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe makarantu da wuraren shaƙatawa

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin da muke kawo muku a wannan shafin.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan kara kasancewa tare da ku a gobe a wannan shafin idan Allah ya kai mu.

  2. Wata kotu a Najeriya ta ba da umarnin a saki Mubarak Bala

    BBC

    Wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin a saki Mubarak Bala, kamar yadda jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito.

    Ana dai zargin Bala ne da amfani da shafinsa na Facebook ya yi ɓatanci ga Annabi Muhammad.

    Bala, wanda shi ne shugaban kungiyar wadanda ba su yarda da addini ba ta Najeriya, an kamashi ne a gidansa da ke Kaduna a watan Fabrairu, biyo bayan korafin da wasu lauyoyi suka shigar na zarginsa da yin batanci ga Annabi Muhammad a shafinsa na Facebook.

    Daga baya kuma ‘yan sanda sun mayar da shi Kano a ranar 2 ga watan Mayun 2020.

    La’akari da ginshikan ‘yancin ɗan adam da Bala yake da shi ya sanya lauyansa, Mai shari’a Inyang Ekwoya yanke hukuncin cewa kama Bala da kuma tsare shi da aka yi take masa ‘yanci aka yi, kuma yana da damar ya tafi inda yake so, da ya yi tunani yadda ya ga dama da kuma ‘yancin fadin albarkacin baki.

    “Hana shi ganin lauyansa wani babban take hakki ne da ya ci karo da sashe na 34 na kundin tsarin mulki na 1999.”

    Alkalin ya umarci ‘yan sanda su biya kudi naira 250,000 tamkar wata diyya don ta zama izina kan abin da suka aikata.

    Mubarak Bala ya yi kaurin suna wajen sukar addini bayan sanar da ficewarsa daga addinin musulunci a 2014.

  3. An kama 'yar tsohon Firaiministan Ethiopia Meles

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Meles Zenawi ya shugabanci Ethiopia daga 1991 har zuwa lokacin da ya mutu a 2012

    Matar tsohon firaministan Ethiopia Meles Zenawi ta shaida wa BBC cewa an kama ɗiyarta a arewacin birnin Mekelle.

    Semhal Meles ta je yankin na Tigray ne don daukar wani shirin fim game da mahaifinta, wadda babban jigo ne a cikin dakarun yantar da yankin Tigray kuma ya shugabanci Habasha fiye da shekaru ashirin.

    Sojojin gwamnatin dai suna gwabza kazamin fada da dakarun kungiyar a Tigray, tun a watan da ya gabata, kuma yanzu haka suna iko da birnin na Mekelle.

  4. Labarai da dumi-dumi, Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe makarantu da wuraren shaƙatawa

    .

    Asalin hoton, NIGERIAN PRESIDENTIAL TASK FORCE

    Kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona, ya sake bayar da umarni ga ma'aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa ƙasa da su zauna a gida har nan da makonni biyar.

    A cewar kwamitin wanda ke ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, duka makarantu a faɗin ƙasar za su zama a rufe har zuwa watan Janairun 2021.

    Kwamitin ya bayyana cewa gidajen rawa da wuraren shan barasa da kuma wuraren motsa jiki za su ci gaba da zama a rufe a ƙasar.

    Kwamitin ya bayar da umarnin rufe gidajen abinci

    Haka kuma gwamnatin ta saka takunkumi kan taruka irin na addini inda kwamitin ya ce ko wane wuri kada ya ɗauki sama da kashi 50 cikin 100 na mutanen da yake ɗauka a baya.

    Gwamnatin ta kayyade tarukan addini su zama kasa da kashi 50 na inda wuraren ibada ke ɗauka, domin tabbatar da ba da tazara da kuma sanya takunkumi.

    Boss Mustapa ya ce dukkan taron da za a yi ya wuce mutum 50 to a tabbatar da an yi shi a buɗaɗɗen waje mai makon a ɗakin taro.

    Haka na ababan hawa su ɗauki kashi 50 na fasinjan da suke iya ɗauka domin bin dokar ba da tazara.

    Ya ƙara da cewa an ɗauki bayanan matafiyan da suka shigo ƙasar daga waje su 163,818 kuma an wallafa a shafin gwamnatin.

  5. EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 32 a Legas

    EFCC

    Asalin hoton, EFCC

    Hukumar yaƙi da cinhanci da yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta ce ta kama mutum 32, wadanda ake zargi da ayyukan damfara ta intanet.

    Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter EFCC ta ce ta kama mutanen ne a wani samame da ta kai gida mai lamba 12, titina 2, a rukunin gidaje na Goodnews, Lagos a safiyar litinin.

    Biyo bayan wasu sahihan bayanai da ta samu na leken asiri kan abubuwan da ake aikatawa na laifi shi yasa ta kai wannan samane tare da nasarar kama mtanen.

    Dama dai ana zargin mutanen ne da ayyukan damfarar mutanen da basu ji ba su gani ba gabanin kama su.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Hukumar ta ce za ta gabatar da su gaban kotu da zarar ta gama bincikenta.

  6. Najeriya ta tsawaita wa'adin yin rijistar lambar NIN

    .

    Asalin hoton, TWITTER

    Gwamnatin Najeriya ta tsawaita wa'adin yin rijistar lambar katin ɗan ƙasa ta NIN ga waɗanda za su yi a wayoyinsu.

    Wannan bayani na cikin wata sanarwa ne da ma'aikatar harkokin sadarwa ta ƙasar ta fitar a ranar Litinin.

    Bayan wani taro da ya gudana tsakanin ministan sadarwa Isa Ali Pantami da wasu masu ruwa da tsaki kamar shugaban NCC, da shugabannin MTN da Airtel da Glo da DG-NITDA da Smile da kuma 9Mobile.

    "Biyo bayan amincewar da gwamnatin Najeriya ta yi shi yasa muka dauki wannan mataki:

    "Ƙarin makonni uku ga masu yin rijistar da suke da lambar katin ɗan ƙasa daga 30 ga watan Disamba 2020 zuwa 19 ga watan Janairun 2021.

    Sai kuma sati shida ga waɗanda ba su da lambar kwata-kwata daga 30 ga watan Disamba zuwa 9 ga watan Fabirairun 2021."

  7. An ƙara kashe wani ɗan jarida a Afghanistan

    TOLONEWS

    Asalin hoton, TOLONEWS

    An ƙara kashe wani ɗan jarida a Afghanistan.

    Rahmatullah Nikzad tsohon ma'aikacin kamfanin dillancin labarai na AP ne, shi ne kuma shugaban ƙungiyar 'yan jarida ta gabashin birnin Ghazni kuma an kashe shi ne a kusa da gidansa.

    Ya tsallake irin wannan harin a shekarar da ta gabata.

    tare da kashe wasu 'yan jarida hudu da aka yi a watanni biyu, ana kara nuna damuwa kan ƙaruwar kashe-kashe kan 'yan jaridar da masu fafutukar kare hakkin dan adam da kuma manyan jami'an gwamnati.

    Mafi yawan hare-hare babu wata kungiya da ke daukar nauyinsu, a na baya-bayan nan ma Taliban ta musanta daukar nauyin harin.

  8. Masu yi wa ƙasa hidima 11 sun kamu da korona a Najeriya

    NYSC Facebook

    Asalin hoton, NYSC Facebook

    Masu yi wa ƙasa hidima 11 sun kamu da korona a sansaninsu da ke Sibre na kusa da Jalingo a Jihar Taraba da ke Najeriya.

    Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Innocent Vakkai ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a Jalingo.

    Jaridar Punch ta ƙasar ta ruwaito kwamishinan na cewa mutane 11 da aka tabbatar sun kamu da cutar ana musu magani a cibiyar keɓe mutane.

    Kwamishinan ya ce an killace su a wani otel saboda lalata gine-ginen sansanin da aka yi a lokacin zanga-zangar EndSARS.

    "Ina da tabbacin lokacin da za a rufe sansanin za su samu lafiya kuma su sake haɗuwa da iyalansu," in ji shi.

    Kwamishinan ya yi kira ga mutanen jihar da su riƙa zama a gida su daina shiga taruka babu gaira babu dalili, musamman lokacin bukukuwan kirsimeti.

  9. 'Yan bindiga sun ɗauke wata mata da ɗanta a Kano

    BBC

    Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun sace wata mata da ɗanta, tare da kashe direban 'yan sanda da ke sitnitiri a garin Falgoren na karamar hukumar Rogo a Kano a arewa maso yammacin Najeriya.

    Rahotanin sun nuna cewar yan bindigar sun kai hari ne a cikin daren jiya, kuma akan hanyarsu ta fita daga garin ne suka yi arangama da ‘yan sandan.

    Wannna dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da al’ummar kasar ke ci gaba da murnar ceto daliban makarantar Ƙanƙara da ke Jahar Katsina.

    Wani mazunin garin Falgore ya shaida wa BBC ce wa " 'yan bidigar sun nufi gidan wani mutumi ne da ake kira Alhaji Usuhu mai taki Falgore kai tsaye ne kuma a nan ne suka saci matarsa da ɗansa wanda ba a jima da yayewa ba.

    Akan hanyarsu ta barin garin ne suka yi ido huɗu da 'yan sanda masu sintiri kuma nan take suka buɗewa 'yan sandan wuta kuma suka ƙona motar ma'aikatan".

    Mutumin ya shaida wa BBC cewa yawan maharan yakai 50, kuma sun kwashe kimanin akwanni suna abin da suka ga dama.

    BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar 'yan sanda jihar ta Kano amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba.

  10. Ƙasashen Turai sun amince da riga-kafin korona na Pfizer-BionTech

    Hukumar kula da magunguna ta Tarayyar Turai, ta amince da amfani da riga-kafin Pfizer-BionTech a ƙasashen na Turai.

    Hukumar ta ce ta tabbatar da riga-kafin na aiki da kashi 95 cikin 100 kuma za a iya yi wa mutane daga ɗan shekara 16 zuwa sama.

    Tuni dai wasu ƙasashe irin su Birtaniya da Amurka suka soma amfani da riga-kafin, bayan amincewar gaggawa da aka yi

  11. An sake gano wani nau'in cutar korona a Afirka ta Kudu

    Cutar korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Masana kimiyya a Afirka ta Kudu sun ce suna aiki tare da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) don bincike kan wani sabon nau'in cutar korona me suna 501.V2 wadda ke saurin yaduwa.

    Sun ce da alama ba shi da alaka da nauu'in da aka gano a kasar Burtaniya.

    Sai dai masanan da ke aiki a cibiyar bincike ta Kwazulu Natal Reseach Innovation, sun ce kwayar cutar tana da kamanceceniya da ta Birtaniyar ta yadda take mannewa a jikin dan Adam.

    A cewar masanan, cutar tana da saurin yaduwa, kodayake har yanzu suna tattara bayanai a kan ta.

    An fara gano sabuwar nau'in kwayar cutar a lardin Eastern Cape kuma tun daga lokacin ne ta bazu zuwa yankin Kwazulu-Natal.

  12. 'Yan sandan Interpol sun kama 'yan bindiga da dama a yankin sahel

    'Yan bindiga

    Asalin hoton, AFP

    Hukumar ‘yan sandan kasa da kasa, Interpol, ta ce ta kama wasu da ake zargi ‘yan 'yn bindiga ne dauke da bindigogi da harsasai a yankin sahel.

    Haka nan an kama su da man fetur da suk samu ba bisa ka’ida ba yayin wani aikin hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya a yankin na Sahel.

    A cewar hukumar, abin fashew fiye da 40,000 wadanda ake amfani da su wajen hakar zinare ba bisa ka’ida ba aka kwace daga hannunsu.

    Interpol ta ce hakar zinare ba bisa ka’ida ba wata sabuwar hanya ce da kungiyoyi masu dauke da makamai ke samun kudade a yankin da kuma daukar ma’aikata.

    Samamen wanda aka shafe tsawon mako ana yi, ya shafi filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa da kan iyakar kasashen Burkina Faso da Ivory Coast da Mali da kuma Nijar.

  13. Ana zargin Saudiyya da UAE da yi wa ma'aikatan Aljazeera kutse a wayoyinsu

    Alajzeera

    Asalin hoton, Getty Images

    An yi wa gomman ma'aikatan gidan talabijin na Aljazeera kutse a wayoyin salularsu ta hanyar amfani da manhajar leken asiri ta kasar Isra'ila, a cewar kwararru kan tsaron intanet.

    An wallafa bayanan kutsen ne a shafin Citizen Lab da ke Jami'ar Toronto ta kasar Canada.

    Ta ce an yi amfani ne da raunin da manhajar wayar iPhone ke da shi wurin kutsawa cikin wayoyin nasu.

    Kamfanin NSO Group wanda ya samar da manhajar ya karyata zargin, yana mai cewa "babu wata hujja".

    Masu bincike na cibiyar Citizen Lab sun ce suna da tabbacin cewa mutum biyu da suka aikata kutsen sun yi ne a madadin gwamnatin Saudiyya da ta Daular Larabawa wato UAE aiki.

    Saudiyya ta sha matsa wa kasar Qatar lamba kan ta rufe gidan talabijin din na Aljazeera tun bayan da dangantaka ta yi tsami, abin da ya jawo dakatar da alaka kwatakwata tsakanin kasashen na yankin Gabas ta Tsakiya.

  14. Yayin da ake shirin zaben shugaban kasa a Nijar...

    Jamhuriyar Nijar

    A ranar Lahadi mai zuwa ne 'yan Nijar za su fita rumfunan kada kuri'a domin zabar sabon shugaban kasa da kuma 'yan majalisar dokoki.

    BBC Hausa ta shirya tsaf domin kawo muku yadda zaben zai kasance a lokacin da abubuwan ke faruwa.

    Jumhuriyar Nijar kamar sauran kasashen Afirka, ta samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Farnsa a ranar 3 ga watan Agusta na shekarar 1960.

    A yau kasar na da al’ummar da yawanta ya kai kimanin milyan 20 da kuma ta kunshi manyan kabilu na kasar guda 10.

    Kabilun kasar ta Nijar sun hada da: Hausawa, Zabarmawa, Fulani, Azinawa, Kanuri, Tubawa, Gurmawa, Buduma, larabawa, Tigidal.

    Bayan wadannan kabilu guda 10 manya-manya na kasar da ke magana da harsunan su na asili, Harshen Faransanci ya kasance harshe na farko da ake amfani da shi a cikin kasar wajen tafiyar da harkokin gwamnati da kuma a makarantun boko.

    Al’ummomin kasar ta Nijar sun kunshi Musulmai da Kiristoci da masu addinin gargajiya da ma wadanda ba su da wani addini.

    Sai dai sama da kashi 90 cikin 100 na al’ummar kasar Musulmai ne.

  15. Labarai da dumi-dumi, Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudin 2021

    Majalisar Najeriya

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudin 2021 a zamanta na musamman a yau Litinin.

    Majaliar ta amince da naira tiriliyan 5.6 a matsayin kudin ayyukan yau da kullum da tiriliyan 4.1 na manyan ayyuka da tiriliyan 3.3 na biyan bashi.

    Kazalika, an ware naira tiriliyan 4.1 a matsayin gudummawar da za a tattara domin gudanar da manyan ayyuka.

    Jumilla, majalisa ta amince da kudi naira tiriliyan 13.5, karin biliyan biyar kenan a kan wanda Shugaba Buhari ya gabatar mata a watan Oktoba na tiriliyan 13.

    Bayan kammala yi wa kasafin karatu na uku a yau, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya nuna jin dadinsa kan yadda suka amince da kasafin kafin tafiya hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

    "Bari na fara yi mana murnar yin aiki tukuru wurin ganin mun amince da kasafin 2021 a kan lokaci kafin tafiya hutun Kirsimeti," in ji shi.

    Tun farko Buhari ya gabatar da kunshin kasafin naira tiriliyan 13 (13,082,420,568,233), wanda ya zarta na 2020 da tiriliyan 2.28, inda na baran ya kasance naira tiriliyan 10.805.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Amurka ta ware dala biliyan 900 na tallafin korona ga 'yan kasar

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan shafe watanni ana hayaniya, 'yan majalisar Amurka sun amince da dala biliyan 900 - malala gashin tinkiya - a matsayin kudin tallafin korona ga Amurkawa.

    Kudin wani bangare ne na dala tiriliyan 1.4 da za a kashe wurin tafiyar da ayyukan gwamnati a cikin wata tara masu zuwa.

    Sabon tsarin ya kunshi bai wa kowane mutum na mafi yawan 'yan kasa dala 600 - sama da naira 200,000 - sannan a kara yawan adadin da ake bai wa marasa aikin yi da dala 300 duk mako.

    Kazalika, an ware dala biliyan 300 domin tallafa wa masu sana'o'i da kuma kudin aikin rarraba allurar riga-kafi da gyara makarantu da sauransu.

    Da yawa daga cikin tanade-tanaden gwamnati na tallafin korona da take bayarwa a yanzu za su daina aiki nan da karshen wata.

    Amurkawa kusan miliyan 12 ne ke fuskantar hadarin rashin samun tallafi da ake bai wa marasa aikin yi.

    Ana sa ran Majalisar Wakilai da ta Dattawa za su kada kuri'a kan kasafin a yau Litinin. Daga nan kuma sai Shugaba Donald Trump ya saka hannu kafin ya zama doka.

    • 'Yan gudun hijirar Afirka ta Tsakiya da ke komawa gida sun ragu

      ‘Yan gudun hijira na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na ci gaba da komawa kasashensu tare da taimakon hukumar da ke kula da su a Kamaru.

      Duk da ce sai wanda yake so ne zai koma, yunkurin na zuwa ne a lokacin da tashin hankali ke karuwa a wasu sassan kasar da ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa.

      Shekarar 2020 ce ke da mafi karancin 'yan gudun hijirar da suka koma gida daga Kamaru, inda aka samu kasa da mutum 30 ne kacal.

      Ana sa ran gudanar da babban zaben kasar a ranar 27 ga Disambar nan.

    • Saudiyya ta rufe kasarta saboda bullar sabuwar cutar korona

      Saudiyya

      Saudiyya ta dakatar da saukar jiragen kasashen waje a kasarta na tsawon mako daya biyo bayan rahotannin bullar wani sabon nau'un cutar korona a kasashen Turai.

      Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ruwaito cewa kasar ta rufe dukkanin iyakokinta na kasa da na ruwa.

      Kazalika, ana sa ran za a iya tsawaita matakin na ko-ta-kwana da karin mako daya bayan ma'aikatar lafiya ta yi nazari.

      Sauran matakan sun hada da:

      • Duk wanda ya je Saudiyya daga Turai ko kuma kasar da sabon nau'in ya bulla bayan 8 ga Disamba, sai ya kilace kansa na mako biyu, sannan sai an rika yi masa gwajin cutar korona duk kwana biyar
      • Wajibi ne ga wanda ya je ko ya wuce ta Turai ko kuma kasar da sabon nau'in ya bulla cikin wata uku da suka wuce ya yi gwajin korona
    • Kotu ta umarci wata mata ta yi bayanin yadda ta tara dukiya ko a kwace

      Kotun Kolin Birtaniya ta ce wajbi ne wata mata da ta kashe makudan kudade wurin sayayya a wani kanti a Landan ta yi bayanin yadda ta tara dukiyar tata ko kuma a kwace ta.

      Zamira Hajiyeva - matar wani mai laifi dan kasar Azerbaijan da aka daure bisa laifin rashawa - akwai yiwuwar a kwace mata dukiyar da ta kai dala miliyan 27 idan ta gaza yin bayani.

      Daga cikin abubuwan da za ta rasa har da gidanta da ke unguwar masu hali ta Knightsbridge da kuma wani filin wasan golf.

      An ce Mrs Hajiyeva ta kashe fiye da dala miliyan 20 a kantin Harrods tsawon shekara 10.

      Ita ce mutum na farko a Birtaniya da aka fara aiwatar da dokar yin bayanin yadda mutum ya tara dukiya, wadda hukumar tattara laifuka ta kasa (National Crime Agency) ta ba ta.

    • 'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban karamar hukuma a Jihar Kogi

      'Yan sandan Najeriya

      Asalin hoton, Getty Images

      Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban Karamar Hukumar Olamaboro ta Jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya mai suna Isaac Emmanuel Ekpa.

      Makusantantan honorabul din sun bayyana cewa an dauke shi ne ranar Juma'a da ta gabata a Ochadamu ta Karamar Hukumar Ofu a lokacin da yake komawa gida.

      Rahotanni sun ruwaito cewa Ekpa na shirin binne mahaifinsa ne bayan ya rasu a lokacin da lamarin ya faru.

      Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito kakakin rundunar 'yan sandan Kogi, Williams Ayah, na cewa wasu 'yan sandan sintiri ne suka tsinci mota babu kowa cikinta a kan titin Ochadamu.

      Bayan sun bincika motar ne kuma suka tsinci katin shaida mai dauke da sunan Emmanuel Isaac Ekpa, a cewarsa.

      Rahotanni na cewa masu garkuwar sun nemi a biya su kudin fansa naira miliyan 25, inda aka ce wani dan uwansa na tattaunawa da su domin neman ragi kan abin da suka nema.