Biden ya lashe Michigan, kuma ya ce ya kusan lashe zaɓen Amurka

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan zaben Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. Labarai da dumi-dumi, Ana sa ran Biden zai lashe zaben jihar Virginia

    Virginia

    Ana sa ran Joe Biden zai yi nasara a jihar Virginia.

    A baya dai jam'iyyar Republican ce take cin zaben shugaban kasa a jihar, sai dai masu kada kuri'a sun mayar da hankali kan Democrats a zabuka uku da suka gabata.

  2. Kun san yadda sakamakon yake kawo yanzu ?

    Zaben Amurka

    A yankin yammacin Amurka sakamakon farko na nuna cewa manyan ‘yan takarar biyu na ci gaba da kan-kan-kan a wurare da dama.

    Dan takara na bukatar kuri’u 270 na kwalejin masu zabe domin lashe zaben shugaban kasa.

    A yanzu haka Joe Biden na da kuri’u 192 a yayin da Donald Trump ke da kuri’u 114.

    Ga yadda hasashe yake a tsakanin manyan ‘yan takarar:

    ·Joe Biden ana saran zai lashe jihohi 14 ciki harda birnin Washington DC. Jihohin su ne Vermont, Delaware, Maryland, Massachusetts, New Jersey, New York, Connecticut, Colorado, New Mexico, New Hampshire, Illinois, California, Oregon, Jihar Washington da kuma Washington DC

    ·Donald Trump ana saran zai lashe jihohi 17. Jihohin su ne Indiana, Kentucky, Oklahoma, Tennessee, West Virginia, Arkansas, South Dakota, North Dakota, Alabama, South Carolina, Louisiana, Nebraska and Nebraska 3rd District, Utah, Missouri, Kansas, Wymong, da kuma Mississippi.

  3. Biden ya yi babban kamu a California

    Dan jam’iyyar Democrat, Joe Biden zai yi babban kamu a California saboda jihar na da wakilan kwalejin zabe 55 kuma duka kuri’unsa ne.

    Ana saran zai lashe jihar wacce a shekarun baya ta kasance ta ‘yan Republican amma kuma daga shekarar 1992 ta sauya ta koma hannun ‘yan Democrat.

    Oregon da Washington ma ana saran za su fada hannu Biden.

    Zaben Amurka
  4. Trump zai lashe Kansas da Wyoming

    Ana saran Donald Trump zai lashe karin jihohi biyu

    Bisa dukkan alamu jihar Kansas za ta zabi Donald Trump. A cikin fiye da shekaru 80, sau daya tal watau a shekarar 1964 ne aka zabi jam’iyyar Democrats a wannan jihar.

    Haka kuma Trump ne ke gab da lashe jihar Wyoming. Jihar ta kasance ta ‘yan jam’iyyar Republican na tsawon shekary. A cikin shekaru 70, Lyndon B Johnson ne kadai a jam’iyyar Democrat ta lashe zabe a wannan jihar

    Zaben Amurka
  5. Jihar Illinios ta faɗa hannun Joe Biden

    Ana sa ran jihar Illinois za ta zabi Joe Biden

    Jihar wacce ke yankin yamma ta tsakiyar Amurka wacce ta kunshi birnin Chicago, ta kasance jihar da ke zaben jam’iyyar Democrat a zaben shugaban kasa tun daga shekarar 1992.

    Tsohon shugaban Amurka, Barack Obama ma ya lashe zabe a wannan jihar.

    Zaben Amurka
  6. Barkanmu da wannan safiya

    Daga nan Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da wannan safiya.

    Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da ake ciki game da sakamakon zaben Amurka, wanda aka gudanar ranar Talata.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta da muhawara a BBC Hausa.