Biden ya lashe Michigan, kuma ya ce ya kusan lashe zaɓen Amurka

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan zaben Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. Facebook da Twitter sun ɗauki mataki kan Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Facebook ya mayar da martani game da iƙirarin da Trump ya yi maras tushe na lashe zaɓe.

    Mai magana da yawun Facebook ya faɗa wa NBC News cewa: "Daga sanda Trump ya fara iƙirarin nasara, mun fara ɗago sahihan bayanai zuwa saman shafin Facebook da Instagram ta yadda kowa zai san cewa har yanzu fa ana tsaka da ƙirga ƙuri'a kuma ba a bayyana wanda ya yi nasara ba."

    Har yanzu ana cigaba da ƙirga miliyoyin ƙuri'u a jihohin da fafatawar ta fi zafi kamar Pennsylvania da Michigan da Wisconsin da kuma sauran waɗanda ka iya sauya sakamakon zaɓen.

    Jami'an zaɓe sun ce za a iya ɗaukar kwanaki nan gaba ba a sanar da wanda ya yi nasara ba a waɗannan jihohin.

    Tun farko Twitter ya ɗauki irin wannan matakin domin daƙile maganganun Trump marasa tushe game da zaɓen.

    Shafin ya maƙala gargaɗi a jikin saƙon da Trump ya ce - ba tare da wata hujja ba - "suna ƙoƙarin sace ƙuri'u".

  2. Matannan huɗu da ke yawan rigima da Trump sun lashe zaɓensu

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗazun nan muka kawo muku cewa Ilhan Omar - baƙar fata Musulma 'yar asalin Somalia - ta sake lashe zaɓen kujerar Majalisar Wakilan Amurka.

    Bugu da ƙari, CNN ta ruwaito cewa dukkanin mata huɗu baƙaƙen fata 'yan Majalisar Wakilai da ake wa laƙabi da Squad sun sake lashe zaɓensu, wanda Ilhan Omar na cikinsu.

    Shigarsu majalisar, matan huɗu sun gauraye shafukan sada zumunta tare da jawo ce-ce-ku-ce tsakaninsu da Donald Trump.

    Matan huɗu su ne: Ilhan Omar daga Minnesota, Alexandria Ocasio-Cortez daga New York, Rashida Tlaib daga Michigan da kuma Ayanna Pressley daga Massachusetts.

    Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter, Ilhan Omar ta taya 'yan tawagar tata ta "Squad" murna, waɗanda ta kira su 'yan uwa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Me ya hana a samu sakamakon zaɓen har yanzu?

    Annobar korona ta sa mutane yin zaɓe da wuri tun kafin ranar zaɓen ta hanyar zuwa da kansu ko kuma aikawa ta akwatin gidan waya.

    Kuri'un da aka kaɗa ta akwatin gidan waya kan ɗauki lokaci kafin a ƙidaya su domin sai an tantance, kamar sa hannu da kuma tabbatar da adireshi.

    Kazalika, kowacce jiha cikin 50 na ƙasar na da dokokinta game da lokacin da ya kamata a fara tantancewa da ƙirga ƙuri'unb akwatin gidan waya, inda jihar Florida ce kaɗai ke fara ƙirga ƙuri'un kwana ɗaya kafin ranar zaɓe.

    Yawanci sakamakon a bayyane yake a daren zaɓen

    Jihohi da dama suna kammala zaɓe a lokuta mabambanta. Abin da ke biyo baya shi ne yawan kuri'u kamar yadda aka ruwaito a kowace jiha.

    Ba a kammala ƙidayar kuri'un a daren da aka yi zaɓe - wannan dama haka yake - amma kuri'un da aka samu za su iya tabbatar da wanda ya yi nasara.

    Kafofin yaɗa labaran Amurka na iya hasashen wanda ya yi nasara a jihar idan har sun tabbatar da wanda ke kan gaba.

    Ba wannan ba ne sakamakon ƙarshe amma kuma yana tabbata idan an kammala ƙidayar kuri'un zaɓen.

    Ba ƙuri'un jama'a ba ne da suka kaɗa ke tantance makomar zaɓen Amurka, yawan kuri'un wakilai na kwalejin zaɓe ne ke tantancewa, waɗanda kowacce jiha ke da nata adadin.

  4. Biden ya lashe Jihar Hawaii

    Sakamakon zaɓe

    Kamar yadda ake iya gani a sama, Joe Biden na jam'iyyar Democrat ya lashe Jihar Hawaii, abin da ke nufin ya samu ƙarin ƙuri'un kwalejin zaɓe guda huɗu (4) - jumilla 224.

    Hakan ya sa ya ƙara bai wa Shugaba Trump na Republican tazarar maki 11.

    Yanzu haka Trump na da jumillar ƙuri'un kwalejin zaɓe 213.

  5. Sai kuma me yanzu?

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Har yanzu babu amsa game da tambayr wane ne zai zama shugaban Amurka.

    Akwai yiwuwar sai an kwana biyu za mu san amsar: Fafatawar za ta koma wurin ƙuri'un da aka kaɗa ne ta gidan waya, waɗanda har yanzu ba a kai ga ƙirgawa ba a jihohi kamar Michigan da Wisconsin da Pennsylvania.

    Abin zai iya kaiwa ga shari'a: Donald Trump ya yi barazanar kai ƙara Kotun Ƙoli domin neman a dakatar da ƙirga ƙuri'u. Hakan na nufin za a iya ɗaukar makonni.

    Rashin tabbas ka iya kawo tashin hankali: Tabbas za a yi zaman rashin tabbas. Sai dai tun da Amurkawa sun bayyana zaɓinsu a akwatin zaɓe, ba lallai ne a samu wata hatsaniya ba - amma fa tuni aka fara zanga-zanga.

    Ya zuwa yanzu, an samu sakamakon jiha 40 cikin 50 na Amurka kuma Joe Biden na jam'iyyar Democrat ne kan gaba da ƙuri'un wakilai na kwalejin zaɓe guda 220, shi kuma Trump na Republican na da 213.

  6. Ilhan Omar ta sake cin zaɓe zuwa Majalisar Wakilan Amurka

    Ilhan Omar

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yar Majalisar Wakilan Amurka Ilhan Omar ta sake lashe zaɓe a karo na biyu daga Minneapolis ta Jihar Minnesota.

    Baƙar fatar kuma Musulma, Ilhan mai shekara 38 ta doke abokin takararta baƙar fata na jam'iyyar Republican, Lacy Johnson, inda ta samu kashi 64.6 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, a cewar kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

    Ilhan Omar ce 'yar asalin Somalia da ta zama 'yar Majalisar Wakilai kuma ɗaya daga mata Musulmai guda biyu da aka taɓa zuwa majalisar a 2018.

    Tana ɗaya daga cikin wata tawaga da ake kira “Squad” ta mata guda huɗu da suka je majalisar a karon farko daga jam'iyyar Democrat.

    Matan su ne: Rashida Tlaib da Detroit, Alexandria Ocasio-Cortez daga New York City, Ayanna Pressley daga Boston.

  7. 'Yan Republican ba su ji daɗin kalaman Trump ba

    Da yawa daga cikin 'yan jam'iyyar Trump ta Republican ba su ji daɗin iƙirarin da ya yi ba - maras tushe - na samun nasara.

    Da yake magana da ABC News, tsohon Gwamnan New Jersey kuma mai bai wa Trump shawara Chris Christie ya siffanta jawabin nasa da cewa kuskure ne - a siyasance da kuma matsayinsa na shugaban ƙasa.

    Shi ma Rick Santorum, tsohon sanata daga Pennsylvania, ya ce kalaman na Trump sun saka shi cikin damuwa.

    "Mutum ya yi amfani da kalmar zamba...ina ganin kuskure ne," ya faɗa wa CNN.

  8. Zanga-zangar adawa da Trump ta ɓarke

    Zanga-zangar adawa da Trump ta ɓarke

    Asalin hoton, Reuters

    Yayin da ake ƙara shiga tsakar dare a Amurka tare da ƙirga ƙuri'u, zanga-zanga ta ɓarke domin nuna adawa da Trump a titunan birnin Washington DC, abin da ya jawo hatsaniya.

    Ɗaruruwan mutane ne suka fantsama titunan, inda suke rufe tituna da kuma yin wasan tartsatsin wuta.

    Wasu daga cikinsu na ihun cewa: "Idan ba mu samu adalci ba, su ma ba za su zauna lafiya ba!"

    Akasarin zanga-zangar ana yi ne cikin kwanciyar hankali, amma akwai rahotannin arangama a kusa da Fadar White House.

    An kama mutum uku, a cewar rahoton NBC Washington.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Labarai da dumi-dumi, Trump zai garzaya Kotun Ƙoli

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Donald Trump ya yi iƙirarin cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka duk da cewa har yanzu ba a kammala ƙirga ƙuri'a ba.

    Kazalika ya ce zai kai ƙara kotu domin ya nemi a dakatar da ƙirga dukkanin ƙuri'un da aka kaɗa.

    "A bayyane take mun yi nasara a zaɓen nan," a iƙirarinsa, yayin da yake magana cikin wani yanayi.

    Ya yi iƙirari - ba tare da wata hujja ba - cewa an aikata maguɗi.

    "Wannan abin kunya ga ƙasarmu," in ji shi, yana mai cewa zai garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon.

  10. Tawagar Trump ta mayar da martani ga Twitter

    Tawagar kamfe ɗin Donald Trump ta mayar da martani game da alamar da Twitter ya sanya wa saƙon da shugaban ya wallafa a matsayin "mai ɓatar da mutane", bayan ya nuna cewa 'yan adawa na ƙoƙarin sauya sakamakon zaɓen.

    Babban Daraktan Kamfe, Tim Murtaugh ya ce: "Cibiyar Silicon Valley na ci gaba da aniyarta ta tantancewa tare da rufe bakin shugaban ƙasar Amurka."

    Trump wanda ya sha sukar ingancin zaɓen, har yanzu bai taɓa fito da wata hujja ba game da zargin nasa.

  11. Minnesota za ta fada hannun Biden

    Ana saran jihar Minnesota za ta zabi Joe Biden.

    Jihar wacce ta kwashe shekaru 60 tana zaben jam’iyyar Democrats a wannan karon ma bata canza zani ba.

    Hakan na nufin cewar jam’iyyar Republican sai dai ta hari gaba a wannan jihar.

    Zaben Amurka
  12. Zuwa yanzu kuri'u bakwai ne suka raba-gardama

    Shugaban Amurka Donald Trump ya rage tazarar da Joe Biden ya yi masa a wajen samun kuri'un kwalejin masu kada kuri'a.

    Zuwa karfe bakwai da rabi na safiyar Laraba, bambancin da ke tsakanin 'yan takarar biyu bai kai kuri'u 10 ba.

    Ana bukatar kuri'u 270 domin lashe zaben.

    Zaben Amurka
  13. Biden ya bai wa Trump tazara

    Zaben Amurka
  14. Ana sa rai Biden zai yi nasara a Rhode Island

    Rhode Island

    Aana sa rai Joe Biden zai yi nasara a jihar Rhode Island. Jihar, wadda ita ce maf kankanta a Amurka ta dade tana zaben jam'iyyar Democrat – tun 1988 take zabar jam'iyyar.

  15. Twitter ya taka wa Trump birki

    Shafin sada zumunta na Twitter ya bayyana wani abu da shugaba Trump ya wallafa a shafinsa matsayin watakila ‘babu cikakken gaskiya kan zabe’ inda shafin ya bukaci jama’a su nemi sahihan bayanai.

    Trump ya wallafa cewa ‘Zamu samu babbar nasara amma suna kokarin sace mana zabe, amma ba zamu barsu ba’.

    Zaben Amurka
  16. Trump zai ci zaben jihar Iowa

    Iowa

    Ana sa ran Donald Trump zai yi nasara a jihar Iowa.

    Jihar wadda ake gumurzu a cikinta tana hannun Democrats daga 1988, ko da yake ta fada hannun Republican shekara hudu da suka wuce lokacin da Trump ya tsaya takara.

  17. Ni ne zan yi nasara a zaben Amurka - Biden

    Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan takarar shugaban Amurka a jam'iyyar Democrat Joe Biden ya ce shi ne zai lashe zaben kasar.

    "Mun san cewa mu za mu yi nasara, amma babu wanda ya san abin da lamarin zai kai zuwa gobe da safe ba, ko fiye da haka!" a cewar Biden, a jawabin da ya yi daga Delaware.

    "Muna da kwarin gwiwa kan yadda abubuwa ke kasancewa. Na zo nan a daren yau domin na gaya muku cewa muna kan hanyar yin nasarar lashe wannan zabe."

    Ya kara da cewa: "Yaki bai kare ba sai kowa ya kada kuri'arsa kuma an kidaya."

  18. Tsohon ɗan sama-jannati Mark Kelly 'ya lashe zaɓen Sanata'

    Tsohon dan sama-jannati da ya yi aiki da hukumar Nasa Mark Kelly ya lashe zaben Sanata a jihar Arizona a karkashin jam'iyyar Democrat, inda ya kayar da 'yar majalisa daga jam'iyyar Republican Martha McSally.

    "An kidaya kuri'u, kuma za mu kammala aikin da muka soma," a cewarsa. Gidan talbijin na Fox News ya yi hasashen cewa shi ne zai yi nasara.

    Ya kara da cewa: "Daren yau dare ne da za mu yi murna. Dare ne da za mu soma aiki."

    Kelly sabon dan siyasa ne wanda mai dakinsa, Gabrielle Giffords, tsohuwar 'yar majalisa ce wadda aka harba a ka lokacin tana ganawa da mutane a mazabarta a 2011.

  19. Biden zai yi jawabi nan gaba kadan

    Ana sa ran dan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Democrat Joe Biden zai yi jawabi daga Cibiyar Chase a Wilmington da ke jihar Delaware nan da mintuna kadan masu zuwa.

    A yayin da sakamakon zabe ke ci gaba da fitowa, sannan har yanzu ba a san wanda zai yi nasara a jihohin da ke yanke hukunci kan wanda ya yi nasara, ana sa rai Biden ba zai yi magana kan yin nasara ko shan kaye ba.

    A gefe guda, ana sa ran Trump zai yi jawabi a daren yau. Zai gudanar da taro a fadar White House wanda mutum 400 za su halarta.

  20. Jihar da ake kira raba-gardama watau Ohio – ta fada a hannun Trump

    Zaben Amurka

    Ana saran shugaba Trump zai samu galaba a jihohin Ohio da Idaho.

    Jihar Ohio ta kasance jihar da ake 'kare jini biri jini' a cikin shekaru masu rayawa a zaben shugaban kasar Amurka kuma bisa dukkan alamu Trump zai lashe kuri’un kwalejin zabe.

    Babu wani abun mamaki kan jihar Idaho wacce ke zaban jam’iyyar Republican saboda a wannan karon ma launin já ne a kan gaba – watau alamar jam’iyyar Republican.

    ‘Yan takarar jam’iyyar Republican ne suka lashe zabe a zabuka 13 a jere.