Tanzania ta dage haramcin da ta ƙaƙaba wa jiragen saman Kenya
Tanzania ta ɗage haramci da ta ƙaƙaba wa kamfanonin jiragen saman Kenya.
Sanarwar da ma'aikatar sufurin jiragen saman Tanzania ta fitar, ta ce ta ɗage haramcin kuma nan take ta amince jiragen su ci gaba da hada-hada tsakanin ƙasashen biyu.
Matakin na zuwa ne kwana guda bayan Kenya ta ware Tanzania cikin ƙasashen ƙetare da za su killace kansu na kwana 14 saboda annobar korona idan sun shiga ƙasar ta.
Tanzania yanzu ta shiga sawun ƙasashen 146 da ƴan ƙasar za su iya shiga Kenya ba tare da killace kai ba.







