Amitabh Bachchan ya ƙaryata warkewarsa daga korona

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin.

    • Trump zai aika dakarun soji 'don maganin tsageru a jihohi'
    • A karon farko an ga Shugaba Buhari sanye da takunkumi
    • An yi nasarar yi wa Sarki Salman na Saudiyya tiyatar mafitsara
    • An yi jana'izar Tolutope Arotile
    • Kamfanin ƙera jirgi na Airbus zai kori ƙarin ma'aikata 900
    • Facebook zai samar da intanet mai arha a Afrika
    • Amitabh Bachchan ya ƙaryata labarin cewa ya warke daga korona
    • Karnuka sun fara gano masu korona

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Ana zargin Rasha da harba makami daga tauraron ɗan adam

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka da Birtaniya suna zargin Rasha da harba makami mai linzami daga tauraron ɗan adam a sararin samaniya.

    A wata sanarwa da ta fitar, Birtaniyar ta bayyana cewa "Mun damu matuƙa dangane da yadda Rasha ta yi gwajin ɗaya daga cikin tauraron ɗan adam ɗinta inda ta harba wani abu mai sifa ta makami."

    Sanarwar ta bayyana cewa irin waɗannan lamuran za su kawo barazana ga amfani da sararin samaniya.

    A baya sai da Amurka ta nuna damuwarta kan tauraron ɗan adam ɗin Rasha.

  3. An buɗe filin jirgin ƙasa da ƙasa na Bagadaza

    ..

    An buɗe filin jirgin Bagadaza a ranar Alhamis, watanni huɗu bayan da aka rufe filin jirgin sakamakon cutar korona.

    Wani mai magana da yawun hukumar kula da filayen jirage na Iraƙi ya bayyana cewa duka fasinjojin da za su je filin jirgin sai sun yi gwajin korona sa'o'i 48 kafin su yi tafiya.

    An kuma bayyana cewa dole ne a gwada zafin jikin fasinjoji kafin su shiga filin jirgin.

    A ranar Alhamis, waɗanda suka kamu da cutar korona a Iraƙi sun zarta 100,000. Sama da mutum 4,122 suka mutu tun bayan ɓullar cutar.

  4. Mutum miliyan 14 za su faɗa cikin talauci a ƙasashen Larabawa – MDD

    ..

    Asalin hoton, Stepfeed

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa annobar korona za ta yi illa matuƙa ga ƙasashen Larabawa inda kusan mutum miliyan 14 za su faɗa cikin talauaci.

    A wani rahoto da MDD ta fitar, ta bayyana cewa mutum miliyan 17 suka rasa ayyukansu a watannin da suka gabata.

    Ta ce tattalin arziƙin wasu ƙasashe zai ragu da kusan kashi 13 cikin 100, kuma wannan asarar a yankin za ta kai ta sama da dala biliyan 150.

    Rahoton ya kuma ce yunƙurin da ake yi na daƙile annobar zai haifar da matsaloli da za a daɗe ana fama da su a yankin.

  5. Karnuka sun fara gano masu korona

    ..

    Asalin hoton, MEDICAL DETECTION DOGS

    Masu bincike a Jamus sun ce sun yi nasara wurin horas da karnuka da za su iya shinshino cutar korona.

    A wani bincike da jami'ar da ake horas da kiwon lafiyar dabbobi ta Hannover tare da haɗin gwiwar rundunar soji ta Jamus, sun bayyana cewa bayan wani horo na mako guda, karnuka takwas a halin yanzu za su iya tantance samfurin gwajin masu korona da waɗanda ba su da ita a kusan kashi 94 cikin 100.

    Masu binciken sun nuna cewa wannan ci gaban zai taimaka wurin gano masu cutar a wurare da suka haɗa da filayen jirgin sama da kuma dandalin wasanni.

  6. Amitabh Bachchan ya ƙaryata labarin cewa ya warke daga korona

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Shahararren ɗan wasan fim ɗin Indiya Amitabh Bachchan ya musanta wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu na talabijin da ke cewa ya warke daga cutar korona.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Amitabh ya ce labarin da ake wallafawa kansa na ƙarya ne.

    A ranar Asabar 11 ga watan Yuli ne aka kwantar da Amitabh Bachchan asibiti sakamakon cutar korona.

    An kuma kwantar da wasu daga cikin makusantansa a asibiti sakamakon su ma sun kamu da cutar

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Facebook zai samar da intanet mai arha a Afrika

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin sada zumunta na Facebook ya bayyana cewa hannun jarin da ya zuba kan intanet zai jawo wa nahiyar haɓakar tattalin arziƙi da kusan dala biliyan 60 zuwa 2024.

    A wani rahoto da kamfanin ya fitar, ya bayyana cewa ƙaruwar mutane a shiga intanet zai sa kuɗin intanet ɗin ya ragu a nahiyar.

    Kamfanin na Facebook ya ce yana zuba kuɗi wurin samar da kayayyakin haɓaka intanet ɗin wanda hakan zai bada dama ga mutane masu zama a kudu da hamadar sahara su samun intanet cikin sauƙi.

    A halin yanzu, kamfani na Facebook ya samar da wi-fi ta intanet a ƙasashe bakwai ga kusan mutum miliyan huɗu a Uganda da Najeriya.

    Sama da rabin mutanen da ke kudu da hamadar sahara ba su da damar shiga intanet, kuma intanet ɗin na da tsada idan aka haɗa da sauran nahiyoyi.

  8. Kamfanin ƙera jirgi na Airbus zai kori ƙarin ma'aikata 900

    ..

    Asalin hoton, Airbus.com

    Dubban 'yan ƙasar Sifaniya da ke aiki a kamfanin ƙera jirgin sama na Airbus na zanga-zanga kan yunƙurin da kamfanin ke yi na korar ma'aikata.

    Kamfanin na Airbus zai kori ma'aikatansa kusan 900 da ke aiki a Sifaniya, ƙari kan 700 waɗanda aka sanar da korar su a watan Fabrairu.

    Kamfanin ya bayyana cewa matsin da annobar korona ta ɓullo da shi ne ya sa suke wannan korar.

    A jumulla dai, kamfanin Airbus zai kori ma'aikata kusan 15,000 a faɗin duniya, ciki har da ma'aikata 5,000 da ke a Jamus da Faransa.

  9. An yi jana'izar Tolutope Arotile

    Tolulope Arotile

    An yi jana'izar Tolulope Arotile, matukiyar jirgin saman yakin Najeriya ta farko, wacce ta mutu sanadin bangajewar da mota ta yi mata a jihar Kaduna a makon jiya.

    Manyan jami'an rundunar sojin sama da jami'an gwamnati ciki har da gwamnan jihar Kogi, mahaifar Ms Arotile ne suka halarci jana'izar tata da aka yi a babbar makabartar sojin Najeriya da ke Gudu a Abuja.

    An bayyana marigayiyar da cewa ta bayar da gudunmuwa sosai a yaki da ƴan bindiga masu fashin daji a jihar Neja inda ita ce ke tuka jiragen rundunar Gama Aiki.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina mata bisa sadaukarwar da ta yi wajen ci gaban kasar.

    Babban hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar ya ce mutuwar jami'ar babban rashi ga rundunar tare da jajanta wa iyalanta a madadin dukkanin jami'an rundunar sojin sama na Najeriya.

    Sakamakon binciken farko da runduar sojn kasar ta fitar ya nuna cewa wasu tsoffin abokan karatunta ne suka buge ta da mota ta baya lokacin da suka gan ta kwatsam a yayin da suka yi kokarin juyawa domin isa gare ta.

    Tolutope Arotile
  10. An yi nasarar yi wa Sarki Salman na Saudiyya tiyatar mafitsara

    Sarkin Saudiyya Salman Bn Abdul'aziz

    Asalin hoton, BBC ARABIC

    An yi nasarar yi wa Sarkin Saudiyya Salman Bn Abdul'aziz tiyatar mafitsara a asibitin King Faisal da ke Riyadh, babban birnin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya sanar a ranar Alhamis.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa Sarki Salman zai shafe wasu kwanaki a asibitin don ci gaba da kula da lafiyarsa bisa shawarar tawagar lafiyar da ta duba shi.

    A ranar Litinin 20 ga watan Yulin nan ne Saudiyyar ta sanar da batun kwantar da Sarki Salman a asibitin Riyadh inda ake yi masa gwaje gwaje.

    Bayanai sun ce Sarkin mai shekara 84 na fama ne da rashin lafiyar da ta shafi mafitsara.

    Tun 2015 Sarkin ke mulki a Saudiyya - kafin zamansa Sarki ya shafe shekara kusan biyu a matsayin Yarima mai jiran gado kuma ya taba rike mukamin mataimakin firimiya a 2012.

    Ya kuma shafe sama da shekaru 50 a matsayin gwamnan Riyadh.

  11. Za a sake bude zirga-zirgar jiragen sama a Jamhuriyar Nijar

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun amince a sake bude sararin samaniyar kasar domi jirage su ci gaba da zirga-zirga zuwa kasashen duniya nan da kwanaki masu zuwa.

    Kamar sauran kasashen duniya, Nijar ta rufe filayen jiragen samanta da iyakokin kan tudu a watan Maris a yunkurin dakile annobar korona.

    A wata sanarwa da ta fitar, gwamatin ta ce bayan ta yi nazari kan halin da ake ciki, yanzu za a ci gaba da zirga-zirga zua kasashen duniya ranar 1 ga watan Agustan 2020.

    Sai dai sun ce za su dauki matakan kiwon lafiya a filayen jiragen saman cikinsu har da gwada zafin jikin mutane.

  12. Labarai da dumi-dumi, A karon farko an ga Shugaba Buhari sanye da takunkumi

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa kasar Mali domin yin sulhu kan rikicin siyasar kasar.

    Sai dai ba isarsa kasar ce ta ja hankali jama'a ba, illa dai ganinsa da aka yi sanye da takunkumin rufe fuska.

    Bayanai sun nuna cewa wannan ne karon farko da Shugaba Buhari ya sanya takunkumin rufe fuska tun da cutar korona ta bulla a kasar a watan Maris.

    Gwamnatin Najeriya ta wajabta sanya takunkumin rufe fuska a bainar jama'a, sai dai shugaban kasar bai taba sanya shi ba duk da yake ya sha gudanar da taruka a bainar jama'a.

    Tafiyar ta shugaban ƙasa ta biyo bayan tattaunawarsa da Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu shiga tsakani daga ƙungiyar Ecowas da suka je Mali domin sasanta rikicin siyasar kasar.

    'Yan adawar kasar ta Mali sun kwashe kwana da kwanaki suna zanga-zanga inda suka bukari Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta ya sauka daga mulki saboda gaza shawo kan rikicin 'yan bindiga, da na tattalin arziki da kuma zaben da ake takaddama a kan sakamakonsa.

    Buhari

    Asalin hoton, Buhari Sallau

  13. Majalisar wakilan Najeriya za ta maka Akpabio a kotu

    Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya bukaci Akawun majalisar ya gurfanar da ministan ma'aikatar Naija Delta Godswill Akpabio a gaban kotu bisa zargin yi wa 'yan majalisa kazafi.

    Mr Gbajabiamila ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter ranar Alhamis bayan wa'adin da ya bai wa Mr Akpabio na bayyana sunayen 'yan majalisar da ya yi zargin suna karbar kwangila daga ma'aikatarsa ya wuce.

    "Da safiyar yau, na umarci Akawun Majalisar Wakilai ya dauko lauyoyi, sanna ya bukace su da su shigar da karar da ta shafi aikata laifi kan Ministan (Naija Delta). A lokaci guda, za mu duba yiwuwar umartar layoyinmu su maka shi a kotu kan bata mana suna," in ji Mr Gbajabiamila.

    A farkon mako ne Mr Akpabio ya yi zargin cewa ana bai wa 'yan majalisar dokokin tarayya kashi 60 cikin dari na kwangilolin da ake bayarwa daga hukumar raya yankin Naija Delta, wato NDDC a takaice.

    Lamarin ya bata ran 'yan majalisar inda Mr Gbajabiamila ya ba shi wa'adin zuwa ranar Alhamis ya fallasa 'yan majalisar da ya bai wa kwangila.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Masu dauke da cutar korona sun kusa kai wa 800,000 a Rasha

    Yanzu jimulla mutum 12,892 suka mutu yayin da mutum 795,038 suka kamu da cutar

    Asalin hoton, AFP

    An samu karin mutum 5,848 da suka kamu da cutar korona a Rasha, yayin da mutum 147 suka mutu sanadin cutar cikin awa 24.

    Wadannan sabbin alkaluma sun nuna raguwar cutar idan aka kwatanta da ranar da ta gabace ta inda aka samu mutum 5,862 da suka harbu yayin da ta yi ajalin mutum 165.

    Yanzu jimulla mutum 12,892 suka mutu yayin da mutum 795,038 suka kamu da cutar.

  15. Babu ministan da 'ya fi ƙarfin majalisar dokokin Najeriya'

    Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya ce babu wani mutum da ke karkashin gwamnati da ya fi karfin majalisar dokokin kasar ta gayyace shi domin ya amsa tambayoyi.

    Ahmad Lawan ya bayyana haka ne a zaman majalisar da aka gudanar ranar Alhamis.

    A sakon da ya wallafa a Twitter, Sanata Lawan ya ce: "lokacin da muke tashi daga zaman majalisa na jiya na yi magana kan bukatar da ke akwai ga mutanen da shugaban kasa ya nada kan mukamai su guji ce-ce-ku-ce na babu gaira babu dalili da kwamitocin majalisun dokoki domin kuwa babu wanda ya wuce majalisa ta yi bincike a kansa."

    Ya kara da cewa kwamitocin majalisar suna gayyatar hukumomin gwamnati ne domin gudanar da ayyukan da al'umma suka aike su majalisun su yi kamar yadda tsarin mulkin shekarar 1999 ya gindaya.

    A baya bayan nan dai ana samun takun saka tsakanin ministoci da 'yan majalisa, inda ko a makon da muke ciki sai da ministan yankin Naija Delta Godswill Akpabio ya yi zargin cewa 'yan majalisar suna samun kaso mai tsoka na kwangilolin da ma'aikatarsa ke bayarwa, lamarin da ya harzuka 'yan majalisar.

    A farkon watan nan, minista a ma'aikatar kwadago ya kai ruwa rana da 'yan majalisar game da zargin tsoma bakinsu a kan shirin shugaban kasar na bai wa matasa aikin yi wanda aka fi sani da N-Power.

    Masu lura da lamura na ganin wannan takaddama d ke tsakanin bangarorin biyu abin kunya ne ganin cewa 'yan majalisar da bangaren zartarwa abokan juna ne ta fannin siyasa, sabanin majalisar da ta gabace ta, wacce ake ganin ta hana ruwa gudu a gwamnatin Shugaba Buhari.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Coronavirus: Dubban mace-mace na damun hukumomin Afirka ta Kudu

    Bayanai na fitowa da ke cewa yawan mace-macen da ake samu daga cutar korona a Afirka ta Kudu sun zarce waɗanda alƙalu,an da hukumomin ƙasar ke fitarwa.

    Mutum 572 ne suka mutu a sanadin cutar cikin sa'a 24 da ta gabata.

    Amma masu bincike daga cibiyar binciken magunguna ta Afirka ta Kudu na cewa alƙaluman na waɗanda ake ganin suna mutuwa a sanadin wasu dalilan na ɓoye dubban masu mutuwa daga Covid-19 kuma yana yiwuwa ba a sanya su cikin ƙdiddiga.

    Kawo yanzu alƙaluman na hukuma sun nuna kusan mutum 6,000 ne suka mutu domin Covid-19.

    Amma wani bincike da aka yi cikin mako 10 ya nuna cewa ƙarin mutum 17,000 sun rasa rayukansu - wanda adadin ya zarce yadda aka saba gani a daidai wannan lokacin a shekarun baya.

    Wannan na nufin akwai mace-mace 11,000 da ba a iya tantance dalilan samunsu ba.

    Masu binciken na ganin yawancin mamatan sun mutu ne saboda cutar korona - misali waɗanda suka mutu a gida da kuma wasu da ba a sanar da hukuma mutuwarsu ba.

    Akwai kuma damuwar da suke da ita cewa ƴan ƙasar na ƙauracewa asibitoci saboda ƙarancin gadajen kwanciya ko domin fargabar suna iya kamuwa da kwayar cutar.

    Wannan kuma na nufin akwai wasu masu fama da cututtuka kamar tarin fiƙa da na HIV ko SIDA da ba sa samun kulawar da ta dace.

  17. Arsenal za ta bai wa Aubameyang kwangila mai romo, Gerrard ya ƙi zama kocin Bristol

    Pierre-Emerick Aubameyang

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Pierre-Emerick Aubameyang

    Arsenal ta shirya sabunta kwangilar dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, inda zai rika karbar £250,000 duk mako tare da karin alawus-alawus, a yunkurin da take yi na rarrashinsa ya ci gaba da zama.(Telegraph)

    Borussia Dortmund na son dauko dan wasan Werder Bremen dan kasar Kosovo Milot Rashica, mai shekara 20, a yayin da suke neman wanda zai maye gurbin dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho, wanda ake sa ran zai tafi Manchester United. (Telegraph)

    Kocin Rangers Steven Gerrard, mai shekara 40, ya ki amincewa da tayin da aka yi masa na zama sabon kocin Bristol City.(Bristol Post)

  18. Sudan za ta rage darajar takardun kuɗinta

    Hauhawar farashin kayayyaki da raguwar kuɗaɗen shiga na kashi 40 cikin 100

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Hauhawar farashin kayayyaki da raguwar kuɗaɗen shiga na kashi 40 cikin 100

    Sudan ta ce za ta rage darajar takardun kuɗinta cikin wani shirin yin gyara ga tattalin arzikin da ƙasar ke fama da shi.

    A halin yanzu a kan sauya takardar kuɗin ƙasar ta fam ko jinai 55 ga kowace dalar Amurka ɗaya ne a hukumance, amma ya kan kai jinai 140 a kasuwannin bayan fage.

    Hauhawar farashin kayayyaki da raguwar kuɗaɗen shiga na kashi 40 cikin 100 da gwamnat ke fuskanta ya tilasta ma ta ɗaukan wadannan jerin matakan inji muƙaddashin ministan kuɗin ƙasar.

    Hukumomin ƙasar sun kuma naɗa fararen hula domin su gudanar da jihohin ƙasar 18 a ƙarƙashin wasu gyare-gyare da ake yi na tsawon shekara uku gabanin mayar da ƙasar bisa tafarkin dimokraɗiyya.

    Ranar Talata aka gurfanar da tsohon shugaban ƙasar Omar al-Bashir - wanda aka hambare gwamnatinsa a bara - a wata kotu kan tuhumar da ake ma sa kan juyin mulkin da yayi wa zaɓabbiyar gwamnatin farar hula a 1989.

  19. Kenya: Gobara ta tashi a gandun dajin Tsavo

    Hukumomin gandun dajin Tsavo na ƙasar Kenya sun sanar da tashin gobara a wuri uku.

    Hukumar da ke kula da dazukan Kenya ta ce an sami nasarar kashe ɗaya daga cikin gobarar da ta kama daura da wurin da ake killace namun dawa na Tsavo kafin ta yi ɓarna.

    Amma ta ce ana can ana ƙoƙarin kashe sauran gobara biyun da ke ci yanzu haka a kudancin gandun daji na Tsavo West da wani gandun dajin mai suna Chyulu National Park.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce gobarar ta ƙone bishiyoyi da tsiro masu yawa.

    Jaridar Daily Nationa ta wallafa wani bidiyo na ɗaya daga cikn gobarar:

    Kauce wa YouTube
    Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba. Ana yi samun tallace-tallace YouTube

    Karshen labarin da aka sa a YouTube

  20. Trump zai aika dakarun soji 'don maganin tsageru a jihohi'

    Dakarun AMURKA

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump zai aike da "dumbin" dakarun tsaro na gwamnatin tarayya zuwa jihohin kasar domin yin dirar-mikiya kan 'tsageru.'

    Chicago da jihohi biyu da jam'iyyar Democrat ke mulki na cikin wadanda Shugaba Trump na jam'iyyar Republican zai aike da dakarun, a yayin da ake ci gaba da tarzoma.

    Sai dai dakarun da aka aike Portland, Oregon, sun fuskanci kalubale. Dawo da doka da oda na cikin manyan batutuwan da da Shugaba Trump ya sanya a gaba a fafutukar ganin an sake zabensa a watan Nuwamba.

    Ana gudanar da jerin zanga-zanga a Amurka tun bayan kisan da 'yan sandan kasar suka yi wa wani bakar fata George Floyd a watan Mayu a birnin Minneapolis.

    A gefe guda, an samu rahotannin karuwar hare-hare da bindiga a biranen New York City, Philadelphia, Los Angeles, Chicago da kuma Milwaukee.