Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An saki Ibrahim Magu dakataccen shugaban EFCC

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Mun zo ƙarshe

    Nan muke saka aya a rahotannin da muke kawo muku kai tsaye a wannan shafi.

    Umar Mikail ne ke cewa mu haɗu gobe da safe cikin ikon Allah.

    Idan kuka duba ƙasa za ku ga labarai kamar haka:

    • Matar El-Rufai ta jagoranci maci zuwa Majalisar Wakilai kan yawaitar fyaɗe a Najeriya
    • Za a kori likitocin da suka ƙi jingine yajin aiki a Akwa Ibom
    • Majalisa za ta yi bincike kan murabus ɗin sojoji 365 a Najeriya
    • Ma'aikatan lafiya 140 ne korona ta kashe a Iran
    • Ministan Afirka ta Kudu ya kamu da cutar korona
    • Yawan al’umar duniya 'zai ragu, na Najeriya zai ƙaru'
    • Buhari ya kaɗu da mutuwar Tolulope Artile
    • Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a India
    • 'Yan Habasha da suka maƙale a Yemen kukan matsin rayuwa
    • An kashe Fahim Saleh mai kamfanin Gokada a New York
    • Jirgin kai kayan agaji ya fadi a Somaliya
  2. Matar El-Rufai ta jagoranci maci zuwa Majalisar Wakilai kan yawaitar fyaɗe a Najeriya

    Wata ƙungiyar mata da ke yaƙi da fyade a arewacin Najeriya ta mika kokenta game da kazancewar aikata fyade ga Majalisar Wakilan ƙasar.

    Ƙungiyar Movement Against Rape And Sexual Violence ta miƙa kokenta ne ga Kakakin Majalasar Wakilai, Honorabul Femi Gbajabiamila da tsakar ranar Laraba.

    Matar gwamnan jihar Kaduna, Aisha Ummi El-Rufai ce ta jagoranci ƙungiyar, inda suka dangaen da zauren majalisar kuma suka gabatar da abin da ke ci musu tuwo a ƙwarya.

  3. Za a kori likitocin da suka ƙi jingine yajin aiki a Akwa Ibom

    Gwamnatin Jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya ta umarci ma'aikatan lafiya da ke yajin aiki a jihar da su koma bakin aiki ko kuma ta kore su daga aikin nasu.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ambato kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Mista Charles Udoh yana bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

    Mista Udoh ya ce yajin aikin da likitocin ke yi a ƙarƙashin ƙungiyarsu mai suna Joint Health Workers Union (JOHESU) "na cike da manufofi na siyasa kuma sam ba ya kan tsari".

    Ya ƙara da cewa: "Buƙatar da suka gabatar ta a biya su kashi 50 cikin 100 na albashinsu a matsayin fansar hatsarin da suke shiga a irin wannan lokaci na matsin tattalin arziki babu tunani a ciki."

    Kwamishinan ya ce ana ta yabon ƙoƙarin da gwamnatinsu take yi game da lafiya a Najeriya, "saboda haka gwamnati na ganin wannan yajin aiki ba ya kan doka".

  4. Majalisa za ta yi bincike kan murabus ɗin sojoji 365 a Najeriya

    'Yan Majalisar Wakilan Najeriya sun jaddada bukatar gudanar da bincike a kan wani wasu sojoji 365 da suka ajiye aikinsu lokaci ɗaya.

    Hukumomin sojin ƙasar dai sun ce akan ba wa sojoji masu buƙata damar yin irin wannan murabus din daga lokaci zuwa lokaci mma `yan majalisar sun musanta, suna cewa ba a taɓa samun sojojin da yawansu ya kai bataliya sun yi ritaya karo ɗaya ba.

    Hon Muhammad Tahir Monguno babban mai tsawatarwa a majalisar kuma shi ne ya gabatar da kudurin da majalisar ta amince don gudanar da bincike, ya shaida wa BBC cewa matsaloli ne kawai suke tilasta wa sojojin yin murabus.

    A ƙarshen da ya gabata ne rahotanni suka ambato cewa sojoji 350 za su ajiye aikinsu na soja saboda sun gaji da aikin bisa wasu dalilai na rashin gamsuwa da shugabancin rundunar.

    Haka kuma ƙarancin albashi da rashin kayan aiki da ma rashin karfafa masu gwiwa na daga cikin batutuwan da ƙananan sojojin da ke yaƙi da Boko Haram suka koka a kai.

  5. Labarai da dumi-dumi, An saki Ibrahim Magu

    'Yan sanda a Najeriya sun saki Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa, a cewar rahoton jaridar intanet ta Premium Times.

    Jaridar ta ce an saki Magu ne a yammacin Laraba.

    A makon da ya gabata ne 'yan sanda suka tsare Ibrahim Magu kuma tun daga wannan lokaci ne wani kwamitin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa ya fara bincikarsa.

    Gwamnati ta zargi Magu da gaza bayar da lissafin kuɗaɗen da hukumarsa ta yi iƙirarin ƙwatowa daga hannun waɗanda ta zarga da aikata cin hanci da rashawa.

    "Kudi kimanin dalar Amurka biliyan 46 ne Ibrahim Magu ya ce an ƙwato amma biliyan 37 aka tarar a banki," in ji Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Buhari.

  6. Za a fara cininkin 'yan kwallo a Premier League daga 27 ga Yuli

    An tsayar da ranar 27 ga watan Yuli zuwa 10 ga watan Oktoba domin bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a gasar Premier League da EFL, amma sai idan Fifa ta amince da hakan.

    Haka kuma akwai kasuwar cikin gida tsakanin Premier League da EFL da aka tsayar za ta fara daga 5 zuwa 16 ga watan Oktoba.

    "A wannan lokacin kungiyoyin Premier za su ci kasuwa tsakaninsu da wanda ke gasa kasa da ta Premier League, ko dai a bayar da dan kwallo aro ko a saya gabaki daya,'' in ji wata sanarwa daga Premier.

    ''Ba cinikin da za a yi tsakanin kungiyoyin Premier League a tsakanin wannan lokacin''.

    Hukumar da ke kula da kungiyoyin da ke buga gasar kasa da ta Premier League ta ce duk dan kwallon da ta saya a lokacin, ba zai buga wasa ba sai a farkon kakar 2020-21.

  7. Jiragen ruwan Iran bakwai sun kama da wuta

    A kalla jiragen ruwa bakwai ne suka kama da wuta a wajen tsayawar su a tashar jiragen ruwa ta Bushehr da ke kudancin Iran, a cewar kafar yada labaran kasar.

    Shugaban kungiyar magance bala'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Irna cewa an shawo kan wutar kuma babu asarar rayuka.

    Ba a san abin da ya haddasa gobarar ba, amma ita ce ta baya-baya a jerin gobarar da ke ta faruwa a 'yan makonnin nan da ba a san musabbabin su ba a kasar.

  8. Ma'aikatan lafiya 140 ne korona ta kashe a Iran

    Iran ta ce ma'aikatan lafiya 140 ne suka rasa rayukansu zuwa yanzu sakamakon annobar cutar korona ƙasar.

    "Rayukammu baki ɗaya fansa ce ga rayuwarsu kuma domin cimma hakan, wajibi ne mu bi shawarwarin masana harkar lafiya," in ji Sima Sadat Lari, wani jami'in ma'aikatar lafiya.

    Iran ta sake fuskantar ƙaruwar masu kamuwa da cutar korona a 'yan kwanakin nan bayan ta sassauta dokokin kulle.

    Ya zuwa yanzu, akwai mutum 264,561 da suka kamu da cutar da kuma 13,410 da suka mutu tun bayan ɓarkewarta a ƙasar, a cewar alƙaluma daga Jami'ar Johns Hopkins.

    Ƙwararru a harkar lafiya sun ce babu mamaki yawan yi wa mutane gwajin cutar ne ya sa ake ƙara samun masu ɗauke da ita a ƙasar.

    Kazalika sun ce mutane ba sa bin dokokin bayar da tazara ko kuma nesa-nesa da juna.

  9. Coronavirus: Rwanda ta kara tsawaita dokar kulle a wasu yankuna

    Ministan cikin gida na Rwanda ya ba da umarnin a kara tsawaita dokar kulle a wasu zababban yankuna a kudu maso yammacin kasar daga ranar Laraba bayan an samu karuwar masu cutar.

    An sanya dokar hana zirga-zirga ta mako biyu a yankunan Nyamasheke da lardin Nyamagabe ciki har da sansanin 'yan gudun hijira da ke dauke da dubban 'yan kasar Congo.

    Hukumomi sun ce matakan da aka dauka a yankunan sun biyo bayan bayanan da jami'an tsaro suka bayan kan karuwar cutar a yankunan.

    A makon jiya ne, aka kara mako biyu a wasu yankunan babban birnin kasar bayan karuwar masu cutar.

    An hana kowa fita sai masu ayyuka na musamman wadanda suka hadar da jami'an lafiya da shagunan abinci.

    A kwanaki 10 baya, An samu mutuwar masu korona 324 a rana guda wanda ya kai adadin wadanda suka mutu a kasar sanadiyya cutar 1,416.

  10. UNICEF ya yi gargaɗi ga Najeriya

    Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa Najeriya na cikin tsaka mai wuya saboda rashin yi wa yara allurar riga-kafi cututtuka a wannan lokaci na annobar korona.

    Asusun ya ce an samu raguwar yi wa yara allurar riga-kafi a fadin duniya sakamakon korona wanda wannan ba karamin koma baya ba ne.

    Kuma kashi 30 cikin 100 na yaran da ba a yi wa allurar rigakafi ba a duniya 'yan kasa da shekara 5 suna rayuwa ne a Najeriya.

    Asusun da Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce ci gaban da aka samu wajen kason da ya karu cikin shekara 10 da ta gabata suna cikin hadari.

    Peter Hawkins shi ne wakilin UNICEF a Najeriya, ya ce akwai jan aiki a gaba yana cewa aikin riga-kafin cutuka wadanda suka hadar da cutar kyanda mai kisa na hadarin karewa.

    A Najeriya, yadda aka gudanar da allurar riga-kafi a watannin shidan farko na wannan shekarar nan ya gaza idan aka kwatanta da wanda aka yi a shekarun baya.

    A 2019, kusan kananan yara miliyan 14 a fadin duniya ba su samu ko wacce irin riga-kafi ba kama daga ta kyanda da tetanos da dai sauransu.

  11. Yawan al’umar duniya 'zai ragu, na Najeriya zai ƙaru'

    Wani bincike da masana daga Jami’ar Washington suka gudanar ya yi gargaɗin cewa ƙasashen duniya ba su shirya ba game da raguwar al’umar duniya da za a samu, wanda kuma ka iya “haifar da damuwa”.

    Masanan sun bayyana cewa kusan kowacce ƙasa za ta fuskanci raguwar adadin al’umarta nan da ƙarshen ƙarni na 21.

    Sai dai binciken ya ce abin ba haka zai kasance ba a Nahiyar Afirka, inda za a samu ƙaruwar jama’a kusan ninki uku na abin da ake da shi a yanzu nan da shekara ta 2100.

    Yawan al’umar Najeriya zai iya kai wa miliyan 800, abin da zai sa ta zama ta ƙasa ta biyu a yawan al’umma a duniya bayan Indiya.

    A cewar binciken, ƙasashe irinsu Spain da Italiya da Poland da Japan da kuma Thailand za su fuskanci raguwa a yawan al’umarsu da kusan rabi. Hatta China za ta rasa kashi 25 cikin 100 na jama’arta.

    An bayyana ƙarancin ilimi ga mata da kuma yawan amfani da ƙwayoyin hana ɗaukar ciki a matsayin manyan dalilan da za su jawo hakan.

    Hakan ba siyasar duniya kaɗai zai shafa ba, wajibi ne ƙasashe su yi duba na tsanaki game da tsarin ci-rani da haraji da kuma tsarin kula da yara.

    Ganin cewa ‘yan sama da shekara 80 za su fi ‘yan ƙasa da shekara 5 yawa, wajibi ne kuma a samar da hanyoyin kula da dattijai fiye da na baya.

  12. Habasha ta fara tara ruwa a madatsar ruwa ta GERD

    Habasha ta fara tara ruwa a sabuwar madatsar nan ta Grand Ethiopia Renaissance Dam (GERD) wadda ta gina kan kogin Nil, kamar yadda Sileshi Bekele, ministan albarkatun ruwa da makamashi ya shaida wa EBC - tashar talabijin mallakin gwamnatin kasar.

    Mista Sileshi ya tabbatar da sahihancin wasu hotuna da aka ɗauka daga tauraron ɗan Adam da ke nuna ƙaruwar ruwa a madatsar.

    Madatsar ruwan - wadda aka kashe dala biliyan 5 wajen gina ta - za ta samar da lantarki mai dumbin yawa ga ƙasar, sai dai ta janyo wata babbar matsala tsakanin Habasha da Masar da kuma Sudan.

    A ranar Litinin kasashen uku suka kammala wata tattaunawa da zummar warware matsalar wadda suka shafe shekara 10 suna gutsuri-tsoma tsakaninsu.

    An kuma ƙulla yarjejeniya kan muhimman batutuwan da Masar da Sudan suka ce ba za su sabu ba a shekarun baya.

    An ɗauki sababbin hotunan ne tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yuli, kuma sun nuna yadda ruwa ke ƙara yawa sannu a hankali cikin makekiyar madatsar.

  13. 'Yar shekara 12 ta auri mutum biyu a wata ɗaya

    ‘Yan sanda a Kenya sun ceto wata yarinya mai shekara 12 da aka aurar da ita ga maza biyu cikin wata ɗaya.

    Mahaifin yarinyar da ke zaune a garin Narok na yammacin babban birnin ƙasar Nairobi, shi ne ya tilasta mata auren wani mutum mai shekara 51.

    Bayan ta gudu ne kuma aka sake aurar da ita ga wani mai shekara 35 kafin daga bisani wasu masu fafutikar kare haƙƙi da jami’an gwamnati su ceto ta.

    Aurar da ‘yan ƙasa da shekara 18 laifi ne a Kenya.

    Wani mai kare haƙƙi ya ce ya samu labarin yarinyar ne yayin da yake tsaka da ceto wata yarinyar daban.

    “Mahaifinta ya bayar da ita ga wani dattijo.

    Ba ta da wani zaɓi illa ta auri wanda bai kai shi tsufa ba,” in ji Joshua Kaputah na ƙungiyar the Narok County Peace Association.

  14. An mayar da intanet a Habasha bayan mako biyu

    An mayar da intanet a wasu sassa na Habasha bayan mako biyu na rikicin da ya barke bayan kisan Hachalu Hundesa - wani mawaƙi ɗan ƙabilar Oromo mai farin jini a birnin Addis Ababa.

    Ƴan ƙasar na iya shiga shafukan intanet har ma da waɗanda ke buƙatar intanet mai sauri kamar sauko da bidiyo.

    Hukumomin ƙasar sun kare matakin da suka ɗauka na doɗe intanet - wanda shi ne mafi tsawo da aka taɓa samu tun da firai minista Abiy Ahmed ya hau karagar mulki a watan Afrilun 2018 - inda tace za a yi amfani da intanet din ne wajen rura wutar rikicin kabilanci.

    Gwamnatin ƙasar ta ce matsalar ta fara ne bayan da wasu matasa daga yankin Oromia suka kafe sai an karkatar da gawar mawaƙi Hachalu da aka dauko daga Addis Ababa zuwa mahaifarsa ta Ambo domin a binne ta. Sun ce sun fi so a binne gawar a babban birnin.

    Hukumomin ƙasar sun ce an kashe fiye da mutum 200 yayin rikicin, ciki har da wasu jami'an tsaro. An kuma kama akalla mutum 5,000.

    Hare-haren ƙabilanci sun kasance masu matuƙar muni da rashin imani, kamar rahoton da jaridar Mail and Guardian ta Birtaniya ta wallafa.

    Wani ɗan jaridar ƙasar waje a Habasha ya wallafa wani bidiyo da ke nuna irin ɓarnar da aka yi a Shashamene, wani gari da ke Oromia wanda ke da nisan kilomita 250 kudu da Addis Ababa.

  15. Za a sake fasalin kamfanin jirgin saman Afrika ta Kudu

    Masu hannun jari a kamfanin jirgin sama na Afrika ta Kudu sun yarda a sake fasalin ayyuka domin kamfanin ya ci gaba da aiki.

    Sake fasalin zai lakume kudin da suka kai dalar Amurka miliyan 600 kuma sama da rabin ma’aikatan jirgin 5,000 ne za su rasa ayyukansu.

    Gwamnatin Afrika ta Kudu ta ce matakin zai kasance kyakkyawan sakamako ga ma’aikata maimakon a ce kamfanin ya durkushe baki daya.

    Kungiyar ma’aikatan ta yi maraba da wannan mataki mara dadi.

  16. Buhari ya kaɗu da mutuwar Tolulope Artile

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya matukar dakuwa da mutuwar Tolulope Artile matukiyar helikwaftan yaki ta farko a Najeriya.

    Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan kar harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar ya ce Shugaba Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan Tolulope Artile wadda ya ce samun irinta a kasa ba karamin ci gaba ba ne ga bangare tsaro da zaman lafiya.

    Shugaban ya jinjina wa Arotile saboda kwazonta a filin yaƙi domin kare kasarta daga 'yan tada kayar baya, yana mai cewa ba za a taba mantawa da gudunmawar da ta bayar ba.

    Shugaban ta cikin sanarwar ya kuma mika ta'aziyyarsa ga rundunar sojin saman Najeriya da abokan aikinta da 'yan uwa da kuma kasar ba ki daya.

    Hakan Shi ma mai taimakawa shugaban na musamman kan kafofin yada labarai Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa shugaban ya yi addu'a ga iyalanta na fatan jurewa wannan babban rashi da su ka yi.

    Matukiyar ta rasu ne a ranar Talata bayan gamuwa da hatsarin mota inda ta samu munanan raunika a Kaduna.

  17. Shugaban Zambiya ya musanta daukar nauyin 'yan da'addan Rwanda

    Shugaba Zambiya Edgar Lungu ya musanta zargi cewa shi ne ke daukar nauyin ‘yan tawayen Rwanda wanda kakakinsu ke hannu tun 2018.

    Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa tsohon kakakin kungiyar Callixte Nsabimana ya shaida wa babbar kotun Rwanda a ranar Litinin cewa shugaba Lungu ya yi alkawarin bayar da dalar Amurka Milyan daya domin hambarar da gwamnatin Rwandan

    Kamfani Dillancin ya ce, kakakin ya ce tuni shugaba Lungu ya tura dala 150,000 domin taimakawa hare-haren ‘yan tawayen.

    Amma mai magana da yawun shugaban ya ce wadannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne, kuma kamata ya yi a kalle su a matsayin “kokarin bata suna”.

    “Mutanen Zambiya da Rwanda na ci gaba da jin dadin alaƙa da ke tsakanin kasashen biyu,” in ji kakakin shugaban kasar Isaac Chipampe cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

    Mista Nsabimana na fuskantar tuhume-tuhume 17, in ji wasu rahotanni.

    Ciki harda kafa kungiyar ‘yan tada kayar baya, harda shiga harkokin ‘yan ta’adda da suka hadar da kisan kai da garkuwa da mutane tare da musanta hannu cikin kisan kare dangi da aka yi a kasar a 1994.

  18. Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a India

    Akalla mutum 50 sun mutu sannan fiye da mutum miliyan biyu suka tagayyara sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a jihar Assam da ke arewa maso gabashin India, a cewar jami'ai.

    An nuna bidiyon wani minista a kasar yana nutso a ruwa a yunkurin ceto mutanen da lamarin ya shafa.

    Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shatata ya lalata dubban kauyuka. An bude daruruwan sansanonin da mutanen da suka rasa gidajensu za su fake.

    Ba wani sabon abu ba ne yin ambaliyar ruwa a yankin, a yayin da India ke kokarin dakile yaduwar Covid-19.

    Ministan da aka gani a bidiyon, Mrinal Saikal, ya taimaka wa wasu kananan yara biyu da wata mace fita daga gidansu a kan kwale-kwale.

  19. 'Yan Habasha da suka maƙale a Yemen na kukan matsin rayuwa

    Hukumar lura da ‘yan ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban ‘yan ci-rani ne suka maƙale a Yemen kuma yawancinsu ‘yan kasar Habasha ne.

    Hukumomin sun ce akalla ‘yan Habasha 14,500 ne suka maƙale a Yemen ba tare da samun abubuwan more rayuwa ba kamar su asibiti da ruwan sha mai tsafta.

    Kulle iyakokin ƙasar da aka yi sakamakon annobar korona ya tilasta wa ‘yan ci-ranin koma wasu yankunan ƙasar waɗanda suka hadar da Aden da Marib da Lahj da kuma Sa’ada in da rayuwa kuma ta ke matuƙar yi musu wahala, in ji hukumar.

    Ta kuma ƙara da cewa dora lafin yaduwar cutar kan ‘yan ciranin tare da nuna musu wariya a zahiri.

    “A matsayin wani mataki na tunkarar annobar korona, ‘yan ci-rani a Yemen na fuskantar muzguna wa ta baki ko kuma ta zahiri ta yadda ake tsare su da hana musu yawo da dai sauransu.”

    Dubban ‘yan ci-rani ne ke tsallakawa Yemen daga Habasha ko wacce shekara sai dai a wannan shekarar korona ta dagula al’amarin.

    A bara, Hukumar lura da ‘yan ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ‘yan ci-rani 138,000 suka tsallaka Yemen daga gabashi Afrika aka sarinsu daga Habasha, a ƙokarinsu na shiga Saudiyya.

  20. Jirgin kai kayan agaji ya fadi a Somaliya

    Wani jirgin sama dauke da kayan agaji daga Djibouti ya fadi a filin jiragen sama na Beledweyne da ke tsakiyar Somaliya.

    Duka matuka jirgin na cikin koshin lafiya babu wanda ya ji rauni, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka a Somaliya ta ambata.

    Ta ce jirgin wani bangare ne na kokarin samar da taimakon abinci a Somaliya.

    "Hatsarin ya faru ne a lokacin da jirgin yake karasa sauka bayan ya dira a kasa," in ji sanarwar.

    Hukumar tabbatar da amincin jiragen sama ta Kenya da ke bibiyar hadari ta wallafa hoton jirgin a shafinta da ke nuna wani bangaren jirgin na ci da wuta.