Bushehr port: Jiragen ruwan Iran bakwai sun kama da wuta

An wallafa

A kalla jiragen ruwa bakwai ne suka kama da wuta a wajen tsayawar su a tashar jiragen ruwa ta Bushehr da ke kudancin Iran, a cewar kafar yada labaran kasar.

Shugaban kungiyar magance bala'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Irna cewa an shawo kan wutar kuma babu asarar rayuka.

Ba a san abin da ya haddasa gobarar ba, amma ita ce ta baya-baya a jerin gobarar da ke ta faruwa a 'yan makonnin nan da ba a san musabbabin su ba a kasar.

Masifun da ke faruwar sun hada da fashewar abubuwa da gobara a wata cibiyar rokoki da tashar lantarki da wani asibiti da kuma cibiyar makaman nukiliya.

Lamuran sun jawo zarge-zarge kan cewa zagon kasa ne.

A ranar Litinin, an samu tashin gobara a wani yanki na masana'antu kusa da birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin kasar. Jami'ai sun ce tankunan adana iskar gas shida ne suka kama da wuta, daya kuma ya yi bindiga.

A ranar Lahadi kuma gobara ce ta tashi a wana kamfanin man fetur a kudu maso yammacin yankin Mahshahr wadda aka ce yoyon man fetur ne ya jawo.

A ranar Asabar kuma wasu tulunan iskar gas ne da dama suka fashe a wani gini a birnin Tehran, kamar yadda jami'ai suka fada.

Jami'ai a Iran sun ce suna duba yiwuwar ko zagon kasa ne na kasashen yamma ko kuma masu adawa na cikin gida ne suke da hannu a abin da ya haddasa gobarar a cibiyar makamashin uranium na Natanz a ranar 2 ga watan Yuli, da kuma wanda ya faru a cibiyar makaman kare dangi ta Khojir a ranar 26 ga watan Yuni.

A shekarar 2010, an yi amanna cewa an yi amfani da wata manhajar komfuta aka kai hari Natanz da sa hannun Amurka da Isra'ila.