Sudan ta sanya dokar ta ɓaci a Darfur

Hukumomi a Sudan sun sanya dokar ta ɓaci a yammacin yankin Darfur, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da rikici ke kara ƙamari tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro bayan shafe makonni ana zanga-zanga.
Kungiyar kasashen Afrika - hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke Darfur ta ce ta aike da wata tawaga zuwa garin Kutum sakamakon rahotannin kona wani ofishin ‘yan sanda da kuma motocinsu.
A ranar Lahadi, jami’an tsaro sun ta amfani da harsashi domin tarwatsa masu zanga-zanga, inda rahotanni suka ce an kashe mutum biyar ciki.
An yi ta zanga-zangar lumana da zaman daɓaro a yankuna da yawa na lardin Darfur, tare da nuna bukatar korar jami’an da aka kama da cin hanci da rashawa da kuma janye sojoji daga birnin da kuma kauyuka.
