'Yan Najeriya kusan 1,000 sun koma gida daga ƙasashen waje
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Rahoto kai-tsaye
Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin kenan
Nan muka kawo ƙarshen rahotanni kai-tsaye a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu haɗu gobe idan Allah ya kai mu da lafiya.
Amma kafin nan, idan kuka yi ƙasa za ku karanta labarai kamar haka:
An ɗaure wata mata saboda ta yi rubutu cikin salon ayar Kur'ani a Facebook
Karon farko cikin wata huɗu, ba a samu wanda ya mutu ba saboda korona a Belgium
Jihar Legas ta shuka bishiya miliyan bakwai
Amurika ta aiwatar da hukuncin kisa karon farko cikin shekara 17
‘Yan sandan Najeriya bakwai sun mutu a haɗarin mota
Za a yi ɗaurin rai da rai ga masu garkuwa da mutane a Najeriya
Sudan ta sanya dokar ta ɓaci a Darfur
'Yan bindiga 'sun sace akalla mutum 30' a Kaduna
Mutum miliyan 690 ne 'ke fama da yunwa a fadin duniya'
Coronavirus: Malaman makaranta sun koma sana'ar akwatin gawa a Uganda
'An sace mutum fiye da 60 a Kamaru'
Covid-19: An ƙara wa likitoci albashi a Faransa
'Yan Najeriya kusan 1,000 sun koma gida daga ƙasashen waje ranar Talata
Asalin hoton, @nidcom_gov
Ƙarin 'yan Najeriya 305 da suka maƙale a birnin Dubai na Daular Larabawa sun isa Abuja babban birnin ƙasar da tsakar ranar Talata.
Wani saƙo da Hukumar 'Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje ta wallafa a Twitter ne ya tabbatar da hakan, inda ta ce jirgin Emirate Airlines ne ya sauka da mutanen a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Jirgin ya sauka da misalin ƙarfe 1:00, a cewar sanarwar.
Har wa yau, an kwaso wasu 261 daga Birtaniya a jirgin Air Peace, inda su ma suka sauka Nnamdi Azikiwe.
Kazalika jirgin Air Peace na biyu ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Jiuhar Legas da ƙarfe 8:00 na daren Talata.
Hukumar ta ce gwaji ya nuna dukaninsu ba sa ɗauke da cutar kafin jiragen su taso.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Abin da ya sa ba mu ɗauki mataki ba kan auren ɗan Ministan Shari'a – Gwamnatin Kano
Asalin hoton, Facebook/ABBAVILLA PHOTOGRAPHY
Gwamnatin Kano ta shaida wa BBC cewa babu wanda ya kai korafin cewa mutane sun karya ka'idojin da aka gindaya don kaucewa kamuwa da korona a bikin dan ministan shari'a Abubakar Malami wanda aka gudanar a makon da ya gabata, shi ya sa ba su dauki mataki ba.
Hotunan bidiyo da aka rinka wallafawa a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda mutane cunkus ke ta rakashewa suna liki da kudi a bikin Abdulazeez Malami da Khadija Dambata, wanda hakan ya saba sharuddan da gwamnatin tarayya da ta jihar ta gindaya wa mutane don dakile yaduwar annobar korona.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Muhammad Garba ya ce, bangaren shagalin bikin da gwamnatin Kano ta shirya a fadarta an bi umarnin bai wa juna tazara sosai.
Amurika ta aiwatar da hukuncin kisa karon farko cikin shekara 17
Asalin hoton, AFP
An zartar da hukuncin kisa kan mutumin nan da ya aikata kisa a Amurika - Daniel Lewis Lee - 'yan awanni bayan Kotun Ƙoli ta sahhale yin hakan kan fursunonin Gwamnatin Tarayya cikin shekara 17.
An dakatar da aiwatar da hukuncin kisa kan mutane da dama bayan wani alƙali ya ce har yanzu akwai ƙararrakin da ba a yanke hukunci kansu ba a ranar Litinin.
Fursunonin da aka yanke wa hukuncin sun koka cewa yi musu allurar guba na nuna "rashin tausayi da kuma wata hanyar horarwa da ba a saba gani ba".
Sai dai alƙalan Kotun Ƙolin sun jefa ƙuri'a cewa "za a iya aiwatar da hukunce-hukuncen kamar yadda aka tsara".
An ɗaure wata mata saboda ta yi rubutu cikin salon ayar Kur'ani a Facebook
Asalin hoton, Getty Images
An ɗaure wata mata a ƙasar Tunisia mai wallafa bayanai a intanet tsawon wata shida a gidan yari bayan ta wallafa wani saƙo kan cutar korona ta hanyar kwaikwayon salon wata ayar Ƙur'ani.
An kama Emna Charqui mai shekara 28 a watan Mayu bayan ta wallafa saƙo a Facebook tana mai shawartar mutane da su bi hanyoyin kariya cikin salon ayar Kur'ani - littafi mai tsarki kuma mafi girma ga Musulmai.
Charqui ta bayyana a wata hira ta baya-bayan nan cewa ba ta yi niyyar tsokanar kowa ba amma saƙon da ta wallafa ya birge ta.
Wata kotu ta same ta da laifin "haifar da ƙiyayya tsakanin addinai".
Zuwa yanzu ba a garƙame ta a gidan yarin ba sakamakon aniyarta ta ɗaukaka ƙara.
A ranar 2 ga watan Mayu, Charqui ta saka wani saƙo a shafinta na zumunta tana kwaikwayon ayar Kur'ani. A ciki ne kuma ta yi kira ga mutane da su riƙa wanke hannu da kuma yin nesa-nesa da juna domin kauce wa kamuwa da cutar korona.
Karon farko cikin wata huɗu, ba a samu wanda ya mutu ba saboda korona a Belgium
Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Belgium ta ce ba a samu wanda ya rasu ba sakamakon cutar korona a cikin awa 24 da suka wuce, karon farko kenan da aka samu hakan tun bayan ɓarkewar annobar a watan Maris.
Jumillar waɗanda suka mutu a ƙasar sun kai 9,787 ya zuwa Talata, adadi na 12 kenan mafi girma a faɗin duniya.
Lokaci na ƙarshe da ba a samu wanda ya mutu ba a ƙasar tun ranar 9 ga watan Maris, a cewar jami'an lafiya - 'yan kwanaki kenan kafin ayyana dokar kulle a ƙasar daga ranar 14 ga wata.
Jihar Legas ta shuka bishiya miliyan bakwai
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Jihar Legas ta ce ta shuka bishiya fiye da miliyan 7.5 a cikin shekara tara da suka gabata domin tattaliin mahalli.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito Kwamishinan Mahalli da Ruwan Sha, Mista Tunji Bello yana bayyana hakan ranar Talata yayin wani shiri da aka kira Ranar Shuka Bishiya a Legas ta 2020 a Asibitin IDH Yaba.
Mista Bello ya ce a shekarar 2008 gwamnatin Babatunde Fashola ta sanya ranar kowacce 14 ga watan Yuli a matsayin Ranar Shuka Bishiya a Legas.
Kwamishinan ya ƙara da cewa wannan alhakin hukumar kula da wuraren shaƙatawa ne ta Jihar Legas wato Lagos State Parks and Gardens Agency (LASPARK) da ke ƙunshe a kundin dokokinta na shekarar 2011.
"Zuwa yau ɗin nan, sama da bishiya miliyan 7.5 aka shuka tun daga sanda aka ƙirƙiri LASPARK a 2011.
‘Yan sandan Najeriya bakwai sun mutu a haɗarin mota
Asalin hoton, Nigeria Police
‘Yan sandan Najeriya bakwai sun mutu a haɗarin mota a kan hanyarsu
ta zuwa jihar Katsina domin yaƙi da ‘yan fashin daji.
Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ya fitar,
ta ce jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne lokacin da motarsu ƙirar bas ta yi
haɗari a garin Jaji da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya.
Sanarwar ta ce a yanzu haka sauran ‘yan sanda 11 da ke cikin
motar suna asibiti ana yi musu magani.
Mummunan haɗarin ya auku ne a ranar Lahadin da ta wuce.
Za a yi ɗaurin rai da rai ga masu garkuwa da mutane a Najeriya
Asalin hoton, @DrAhmadLawan
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a kasar.
A baya dai ana yanke hukuncin daurin shekara 10 ga mutanen da aka kama da laifin.
Haka kuma majalisar ta soke bambanci jinsi maza ko mata kan laifin fyade.
Wannan matsaya da majalisar da cimma ta biyo bayan tsallake karatu na uku da kudurin ya yi tare da sauya dokar manyan laifuka ta kasar, ta 2004."
'Yar majalisa da ke wakiltar jihar Legas ta tsakiya Sanata Oluremi Tinubu ne ta nemi a kara tsaurara dokar da kuma cire banbanci a tsakanin jinsi a lokacin hukunci kan fyade.
Kudurin ya cire wa'adin gabatar da kara kan cin zarafi a kasar baki daya.
Idan kudurin ya zama doka, hukuncin cin zarafin zai zama za a iya aiki da shi a ko wanne lokaci.
Afrika ta Kudu ta yi ahuwa ga fursunonin kasar Mozambique
Asalin hoton, Getty Images
Afrika ta Kudu ta yi wa 'yan gidan yari 183 da suka fito daga Mozambique afuwa tare da fitar da su daga kasar a wani mataki na rage cinkoson gidajen yarin kasar saboda annobar korona.
Ya zuwa yanzu kasar ta tabbatar da mutum 280,000 kuma 4,000 suka mutu.
Wadanda aka mayar sun isa kasarsu ne ranar Litinin ta iyakar Ressano Garcia kamar inda rahotanni daga Mozambique suka bayyana.
Wannan ne rukuni na biyu na 'yan gidan yarin Mozambique da aka mayar Afrika ta Kudu a wani matakin dakile cutar korona.
Rukunin farko na mutum 439 da aka mayar a tsakiyar watan Mayu. Kuma biyu daga cikinsuan gwada su an tabbatar suna dauke da cutar.
Korona ta kashe dan jaridar da aka daure a gidan yari a Masar
Asalin hoton, Getty Images
Fitaccen dan jaridar nan na Masar ya mutu sakamakon cutar korona, in ji 'yarsa.
An kama Mohamed Monir a makon jiya bayan ya bayyana a tashar Al-jazeera ta kasar Qatar, wadda gwamnatin Masar ta yanke hulda da ita.
An tuhume sa ne da shiga kungiyar 'yan ta'adda, da yada labaran karya, da amfani da kafafen sada zumunta, kamar yadda kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta bayyana, wadda ta ce Monir ya mutu a wata cibiyar killace masu korona a ranar Litinin bayan ya kamu da rashin lafiya.
Masar ce kasa ta 166 cikin kasashe 180 a wani jerin kasashe da kungiyar Reporters Without Borders, wato rukunin karshe cikin kasashen da ke take hakkin 'yan jarida a duniya, wadda kuma kungiyar ta ce "daya ce daga cikin kasashen da aka fi daure 'yan jarida a duniya".
Kasar da na da kimanin mutum 4,000 da suka mutu sakamakon cutar kuma 83,000 suka kamu tun lokacin da cutar ta bulla, kamar yadda bayanan jami'ar Johns Hopkins suka bayyana
'Yan bindiga 'sun sace akalla mutum 30' a Kaduna
Asalin hoton, Facebook/Nasir El-rufai
Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya, na cewa wasu `yan bindiga sun sace akalla mutum 30 a yankin Danbushiya da ke karamar hukumar Chikun.
Kazalika `yan bindigar sun kashe mutum daya daga cikin wadanda suka sace bayan ya yi runkurin tserewa.
Wasu mazauna yankin, sun bayyana cewa lamarin dai ya faru ne tun a ranar Lahadin da ta wuce da daddare, a lokacin da mazauna kauyukan da ke kewaye suke ribibin komawa gida.
Wani mazaunin yankin ya ce `yan bindigar sun badda-kama ne ta hanyar sanya kayan damara, sannan suka datse wata babbar gadar da ke kan hanyar da ta hada garuruwan yankin da unguwar Millenium City da kuma garin Kaduna.
Ya ce: "Wadannan mutane suna sanye ne da kayan sojoji, wasu kuma suna sanye da kayan `yan sanda. Kuma sun tsaya a hanya n suna tambayar face-mask. In sauka tambaya ina face-mask din ka, idan babu sai ce ka yi nan."
"Da ma sun rabu biyu ne. wasu suna kan hanya wasu suna gefe. In ka tafi wurin wadanda suke gefe sai su sa ka ka kwanta. Sun yi ta`adi sosai. Har sun harbi mutum daya, nan take ya rasa ransa. Kuma sun tafi da mutane. Har zuwa yanzu dai ba mu san adadin mutanen da suka tafi da su b a. Wannan da suka kashe ma, lokacin da ya fahinci ba jami`an tsaro ba ne ya yi yunkurin ya gudu, sai suka harbe shi nan take.
Sai dai mutanen yankin sun bayyana cewa jami`an tsaro sun hanzarta wajen kai dauki, kasancewar ganin su ma ya sa `yan bindigan suka bazama daji.
Amma duk da haka sai da suka tafi wasu daga cikin mutanen da suka kama.
Wannan lamari dai, kamar yadda wani mutum ya ce ya tayar da hankalin mazauna yankin.
“Gaskiya al`umar wannan wuri muna cikin dardar, kasantuwar ba a taba samun da ya faru irin wannan ba a a wannan yankin. Yanzu tun kafin karfe hud z aka wani yana neman ya dawo gida. Har yanzu dai mutane suna cikin halin firgici. Gonakinmu, kasan saboda faruwar irin wannan abun ba a iya zuwa gonaki masu nisa sai na kusa da gari irin su Danbushiya da da dokan maijama`a nan ake zuwa. To dalilin faruwar wannan abu mutane ma sun kaurace wa gonakin nasu. Rokon da muke so mu yi ga hukumomi shi ne a kara zage-dantse wajen ganin an yi tattalin zaman lafiya a wajen nan.
Har zuwa dai `yan bindigar ba su waiwayi `yan uwan mutanen da suka sace ba, ballantana a kai maganar fansa.
Mun tuntubi kakakin rundunar `yan sanda a jihar Kaduna ta waya, amma ba mu yi nasara ba.
Kazalika babu wata sanarwa ta bangaren gwamnatin jihar game da wannan satar mutane da `yan bindiga suka yi.
Kodayake mahukunta a da jami`an tsaro sun sha yin alwashin bakin kokarinsu wajen kare rayuka da dukiyar jama`a.
'Mutum miliyan 690 ne ke fama da yunwa a fadin duniya'
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum miliyan 690 ne ke fama da yunwa a fadin duniya, kimanin kashi 9 cikin 100 na yawan mutanen duniya.
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ne ya bayyana hakan a shafinsa na tuwita, yana cewa wasu karin mutane ka iya kara tsintar kansu cikin halin yunwar a wannan shekarar.
"Dole mu samar da tsarin abinci mai dorewa tare da kara lafiya wanda kowa zai iya samu a ko ina."
Masana na ganin halin da duniya ta tsinci kanta a ciki na da alaka da annobar korona da ta mamaye kusan ko ina a duniya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Mutum 55 sun kamu da cutar korona a wata makaranta a Ghana
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin lafiya a Ghana sun ce dalibai da ma'aikata 55 sun kamu da cutar korona a makarantar sakandare ta Accra Girls Senior High School da ke babban birnin kasar.
A watan jiya ne hukumomin kasar ta Ghana suka amince dalibai da ke ajin karshe su koma makaranta domin samun damar rubuta jarrabawar karshe.
Ranar Litinin aka soma samun daliban da suka kamu da cutar ta korona.
Makon jiya Shugaba Nana Akufo-Addo ya killace kansa a matsayin riga-kafi bayan wasu ma'aikatansa sun kamu da cutar korona.
Ku saurari labaran duniya cikin minti daya
Bayanan sautiMinti Daya Da BBC Na Rana 14/07/2020
Mataimakin shugaban kasar Ivory Coast ya ajiye aikinsa
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A 2017 ne aka nada shi a matsayin mataimakin shugaban kasar
Mataimakin shugaban kasar Ivory Coast Daniel Kablan Duncan ya sauka daga mukaminsa.
Murabus din nasa na zuwa ne bayan wata mutuwar kwatsam da Firaiminista Amadou Gon Coulibaly ya yi a makon jiya.
Sakataren gwamnatin kasar Patrick Achi ya ce Mista Kablan Duncan ya ajiye mukamin nasa ne bisa radin kansa wanda kuma bai bayyana dalili ba.
Tun a watan Fabrairu ne mataimakin shugaban kasar ya aike da takardar ajiye aikinsa ofishin shugaban kasar Alassane Ouattara, in ji Mista Achi.
"Bayan wasu jerin tattaunawa, wadda aka yi ta karshe a ranar Talata 7 ga watan Yuli na 2020, shugaban kasar ya san da wannan matakin kuma a shirye yake ya sanya hannu kan takardar," in ji Mista Achi cikin wata sanarwa da ya fitar.
Mista Kablan Duncan ya zama mataimakin shugaban kasar a 2017, wanda kuma shi ne mutum na farko da ya taba rike matsayin da aka kirkiro shekarun baya bayan sauraren ra'ayoyin mutane.
A baya kuma ya rike matsayin Firaiministan kasar.
Covid-19: An ƙara wa likitoci albashi a Faransa
Asalin hoton, EPA
Hukumomi a Faransa sun amince a kara albashin da ya kai €8bn ga ma'aikatan lafiya, a yayin da gwamnati ta yaba musu kan namijin kokarinsu wajen yaki da cutar korona.
An sanya hannu kan takardar karin albashi ne ranar Litinin tare da kungiyoyin kwadago bayan an kwashe makonni ana tattaunawa, kuma hakan na nufin kowanne likita zai samu akalla karin €183 a wata.
'Yan kasar suna fitowa bainar jama'a suna yaba wa ma'aikatan lafiyar tun da annobar korona ta barke.
Amma sun ce suna so yabon ya wuce wanda jama'a ke yi musu ind suka yi zanga-zanga domin nemin kara musu albashi da kuma inganta yanayin asibitotin kasar.
Mutum fiye da 200,000 suka kamu da cutar korona a Faransa inda kum ta yi ajalin mutum 30,000.
City za ta rike Guardiola, Madrid ranta na kan Mbappe
Asalin hoton, Getty Images
Manchester City za ta sabunta kwangilar kocinta Pep Guardiola mai tsoka bayan ta yi nasara da karar da ta daukaka kan haramta mata buga gasar zakarun Turai.(Mirror)
Dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, yana cikin 'yan wasan da ake ganin Guardiola zai dauko domin gyra bayansa.(Telegraph - subscription only)
Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya yi watsi da yiyuwar dan wasan Paris St-Germain da Brazil Neymar, mai shekara 28, zai dawo Nou Camp amma ya ce yana diba yiyuwar dauko dan wasan gaba na Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22.(TV3 via Mundo Deportivo - in Spanish).
Ku karanta cikakken tsegumi kan kasuwar 'yan wasa da koci-koci a nan:
'An sace mutum fiye da 60 a Kamaru'
Rahotanni daga Jamhuriyar Kamaru na cewa an sace mutum sama da 60 a yankin renon
ingila.
Wakilin BBC a Yaounde, babban birnin kasar Mahaman Babala, ya ce ba a bayyana su waye suka sace mutanen ba, kuma babu wata kungiya da ta dauki alhakin haka.
Amma kuma tuni aka zargi masu
fafutuka da ke yunkurin ballewa daga kasar da sace mutanen.
Sai dai gwamnati ta ce ta soma gudanar da bincike kan lamarin.
Coronavirus: Malaman makaranta sun koma sana'ar akwatin gawa a Uganda
Asalin hoton, Getty Images
Wasu malaman makaranta masu zaman kansu a Uganda sun fara komawa aikin haɗa akwatin gawa domin samun abin da za su sanya a bakinsu, bayan an rufe makarantun saboda annobar korona.
An ruwaito wasu malaman na cewa sun fara komawa wasu kananan ayyuka kamar tuka babur da motocin haya da aikin kafinta da sayar da abinci da gawayi da wasu ayyukan cikin gida.
Kasar ta rufe dukkan makarantu a watan Maris a wani kokari na daukar matakan shawo kan yaduwar annobar korona.
Shugaban kungiyar makarantu masu zaman kansu, Hasadu Kirabira, ya nemi gwamnati da ta kawo wa malaman dauki.
Ministan cikin gida na kasar ya ce babu abin da gwamnati za ta iya yi musu saboda abin ya shafi kowanne bangaren kasuwanci.
Makarantu masu zaman kansu sun dogara ne kan kudaden da suke samu su biya malamansu ba kamar sauran makarantun gwamnati ba.