Makomar Henderson, Kurzawa, Meunier, Onana
Golan Manchester United Dean Henderson, wanda yanzu haka yake zaman aro aSheffield United,zai sabunta kwangilarsa a Old Trafford ne kawai idan aka ba shi tabbacin cewa shi ne mutum na faro da za a rika sanya wa a wasa.Chelsea da Tottenham suna sha'awar daukar dan wasan na Ingila mai shekara 23.(Manchester Evening News)
Paris St-Germain ta bai wa dan wasan Faransa Layvin Kurzawa, mai shekara 27, sabuwar kwangilar shekara hudu, a yayin da Arsenal da Chelsea suke zawarcinsa.(France Football - in French)
Barcelona ta rage farashin da ta sanya kan Philippe Coutinho daga £100m zuwa £63m, ko da yake tsohuwar kungiyarsaLiverpoolba ta sha'awar sake ayen dan wasan mai shekara 28 dan kasar Brazil.(Mirror)
Dan wasan Arsenal Matteo Guendouzi, mai shekara 21, ya harzuka dan wasanBrightonNeal Maupay, mai shekara 23, a kan albashinsu lokacin wasansu ranar Asabar, inda dukkan 'yan wasan na faransa biyu suka yi ta caar-baki a karshen wasan.(Mail)

Asalin hoton, Getty Images


