Nijar ta yi asarar dala miliyan 50 a badakalar siyan makamai

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Rufewa

    A nan ne muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku kai tsaye a wannan shafin, sai kuma gobe idon Allah ya kai mu, amma yanzu ni Buhari Muhammmad Fagge nake cewe mu kwana lafiya.

  2. An samu girgizar kasa a Mexico

    AFp

    Asalin hoton, AFP

    Girgizar kasa mai karfin gaske ta afkawa gine-gine a birane shida da ke Mexico.

    Kawo yanzu babu rahotannin rasa rayuka ko kuma bayanan asarar da aka yi.

    Da yawan jama'a na aiki ne daga gida saboda kullen Korona, to amma na'urar ko ta kwana da gwamnati ta saka ta ankarar da mutane kafin zuwan girgizar kasar.

    Girgizar kasar na da nauyin maki bakwai kuma ta fi karfi a jahar Ozaka da ke kudu maso yammacin kasar.

    Girgizar kasar na zuwa shekaru uku da aka yi wata irinta da ta kashe daruruwa inda kuma dubbai suka rasa gidajensu.

    AFp

    Asalin hoton, AFP

  3. Kotu ta kama wani dan sanda da laifin kisan kai a Kenya

    @MATHARE_ROOTS

    Asalin hoton, @MATHARE_ROOTS

    Wata Kotu a Kenya ta kama wani dan sanda da laifin kisan wani yaro dan shekara 13 a Nairobi babban birnin kasar.

    An harbe Yassin Hussain a watan Maris a harabar gidansu a lokacin da aka kakaba dokar kulle a kasar saboda cutar Korona.

    To sai dai Dan sanda Patrick Ndiema ya ki amsa laifin kisan kai.

    A farkon watannan ne wata kungiya mai sa ido kan 'yan sanda a Kenya ta sanar da cewa, akalla jam'ian tsaro a Kenyar sun kashe mutun 15 a rangadin da suke yi na tabbatar da dokar kulle.

    Tun bayan zanga-zanga kan kisan bakar fatannan George Floyd a Amurka, masu fafutuka ke kira da a duba ta'asar da 'yan sanda ke yi wa al'umma a Kenya.

  4. Zaman lafiya ne zai kai mu gaci - Peter Mutharika

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Shugaba Peter Mutharika na Malawi ya bukaci da a zauna lafiya, a zaben shugaban kasa da ake sake gudanarwa.

    Shugaban ya zargi yan adawa da tada hankali.

    A bara ne kotun ta soke zaben da Mista Mutharika ya lashe dakyar, bayan da alkalai suka aminta cewa akwai magudi.

    Shugaban na fuskantar babban kalubale daga dan takarar jam'iyyar adawa Lazarus Chakwera.

    Wakilin BBC yace shugaba Peter Mutharika na fuskantar babban kalubale saboda hadewar da jam'iyyun adawa suka yi wuri guda don yakarsa.

    To amma fah duk da haka shi ma yana da magoya baya sosai a Malawi.

    Hukumar kare hakkin bil'adama ta tarayyar Turai ta zargi gwamnatin Malawi da shirya magudi, bayan da ta yi kokarin yi wa alkalin alkalan kasar ritaya lokacin da ake dab da zabe.

  5. Putin - Za a kara haraji ga masu kudi a Rasha

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce zai kara kudin haraji ga masu arziki a Rasha a wani bangare na yakin da kasar ke yi da annobar korona.

    A wani bayani da ya yi wa kasar ta kafar talabiji a yau, Putin ya nemi kara harajin shekara-shekara da ake karba daga kashi 13 zuwa kashi 15 cikin 100 ga wadanda suke iya samun kudin da suka kai dala 72,833 a shekara.

    Wannan ne karon farko da Rasha za ta kara haraji a kasar tun bayan mayar da shi na bai daya da ta yi a 2001.

    Shugaban wanda goyon bayan da yake samu ya ragu sama da yadda ba a taba gani ba, ya ce sauyin zai kara kusan (roubles) biliyan 60 kan kasafin kudin kasar, wanda hakan zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2021.

    A yanzu akwai kimanin mutum 600,000 da aka tabbatar suna dauke da cutar korona a Rasha, kuma tuni aka ruwaito 8,348 sun mutu,.

  6. Birtaniya za ta buɗe wuraren shakatawa da na abinci

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya ce za a bude gidajen abinci da na shakatawa a Ingila daga ranar 4 ga watan Yuli.

    Ya fada wa majalisa cewa daga tazarar mita biyu za a dawo mita daya a inda ya zama dole a ba da tazarar.

    To amma ya ce dole ne masu sana'o'i su dauki matakan kariya daga cutar Korona.

    To sai dai sassaucin bai shafi gidajen rawa ba da na motsa jiki.

    Wannan shi ne sassauci da aka fi maraba da shi a Ingila tun bayan kakaba dokar kulle a watan Maris.

  7. Nijar ta yi asarar dala miliyan 50 a badakalar siyan makamai

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai gabatar da kara a Nijar ya ce akwai kwararan shaidu cewa kasar ta yi asarar kudi kimanin dala miliyan 50 sakamakon badakalar siyan makamai.

    Yana kafa hujja da wani binciken kudi da minisatn tsaron kasar Maman Sayabou Issa ya ce akwai tuhuma da ake yi kan wasu kayayyaki da kuma makaman yakin soji da aka biya a siyo amma ba a kawo ba.

    Wani kwarya-kwaryan bincike da aka gudanar ya gano cewa kudin da aka yi asara ma ya kai ninkin wanda aka sanar.

    Wata sanarwa da mai shigar da karar ya fitar ya nuna shaida kan yaudara, bayanan karya da kumakokarin azurta kai.

    Wannan badakala ta matukar fusata mutanen kasar, wadda ke ci gaba da fuskantar matsalar hare-haren masu tada kayar baya a kudu masu gabashi da kuma yammacin kasar.

  8. Sharudda takwas da Sudiyya ta gindaya kan hajjin bana

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta fitar da wasu sharudda guda takwas da suka shafi aikin hajjin 2020 a wata sanarwa a ranar Talata.

    A ranar Litinin ne Saudiyya ta sanar da cewa mazauna kasar ne kadai - cikin su har da 'yan kasashe daban-daban da ke zaune a cikinta - za a bari su yi aikin Hajjin bana.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar aikin Hajji kasar ta fitar ta ce sun dauki mataki ne bisa la'akari da yadda cutar korona ta yadu zuwa kasahe sama da 180 a fadin duniya, da kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar da wadanda ke dauke da ita da suka kai miliyan bakwai a fadin duniya.

    Ga dai sharuddan a jere kamar yadda ma'aikatar ta fitar:

    1- Za a yi wa alhazan gwajin cutar korona kafin su fara aiki, sannan za a killace su bayan an kammala aikin.

    2- Mazauna kasar da 'yan kasar 'yan kasa da shekara 65 ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana.

    3- Ba za a bar utanen da ke fama da munanan cututtuka kamar su ciwon suga da ciwon zuciya su yi aikin hajjin ba.

    4- Za a dinga sa ido kan yanayin lafiyar kowane mahajjaci.

    5- Za a dinga gudanar da ayyukan matakan aikin hajji rukunu-rukuni na mutane kadan-dkadan saboda tabbatar da dokar yin nesa-nesa da juna.

    6- Yawan wadanda za su yi aikin hajjin bana ba za su haura 10,000 ba.

    7- Babu wanda zai je Saudiyya don yin aikin hajji daga wasu kasashen.

    8- Za a bude asibiti na musamman a Makkah don ayyukan gaggawa.

  9. Novak Djokovic ya kamu da cutar korona

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Dan wasan Tennis na daya a Duniya Novak Djokovic ya kamu da cutar korona - wanda ya zama dan wasa na hudu da ya kamu da cutar bayan buga wasa a Adria tour da ya shirya a Croatia.

    Batun cewa cutar hadin baki ce ga Djokovic ba bakon abu ba ne.

    Ya kuma bayyana ce wa shi yana adawa da rigakafin cutar yayin wata tattaunawar kai tsaye da aka yi da shi a shafin Facebook a watan Afirilu.

    Ya ce " babu wanda ya isa ya tursasa ni a yi mani riga kafi" shin hakan zai iya zama dole ga matafiyi da kuma wanda zai buga gasar.

    Kuma an ta samun masu goya masa baya kan kin amincewa da allurar.

  10. Abin da ya sa aka jibge 'yan sanda a hedikwatar jam'iyyar APC

    APC

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta aike da jami'anta zuwa hedikwatar jami'iyya mai mulki ta APC da ke Abuja saboda daukar matakin gaggawa na tabbatar da zaman lafiya tare da tabbatar da ba a samu yamutsi ba a sakatariya.

    Cikin wata sanarwa da kakkakin rundunar 'yan sanda Frank Mba ya fitar ta ce, zuwan jami'an 'yan sandan ba yana nufin rufe ginin sakatariyar ba ne kamar yadda ake ta yada jita-jita, wani matakai ne na ko ta kwana ganin rikicin da yake ta karuwa a cikin jam'iyyar mai mulki.

    Sanarwar ta ce mambobin majalisar ta APC da sauran ma'aikatansu na da damar ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da gobe a ciki da kuma wajen sakatariyar kamar yadda suke yi ko da yaushe.

  11. An dawo da mukamin Firaiminsta a Burundi bayan shekara 22

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Bunyoni ne ministan tsaron kasar tun 2015

    'Yan majalisar Burundi sun amince da Alain Guillaume Bunyoni a matsayin sabon Firaiministan kasar, wanda zai zama mutum na farko da zai kasance a kan mukamin cikin shekara 22.

    Sabon zababben shugaban kasar Evariste Ndayishimiye ne ya dawo da mukamin, wanda aka rantsar a makon jiya watannin biyu gabannin yadda aka tsara tun farko.

    Haka kuma 'yan majalisar sun amince da Prosper Bazombanza a matsayin sabon mataimakin shugaban kasar.

    Dan shekaru 60 din ya taba zaman mataimakin shugaban kasar a baya - karkashin mulkin Mr Nkurunziza tsakanin shekarar 2014 - 2015.

    Shekara biyar baya, Mista Bunyoni ne ministan tsaron kasar kuma yana da karfin fada a ji a jami'iyya mai mulki ta CNDD-FDD.

    Jami'in mai shekara 48 ya kasance cikin manyan mukarrabar gwamnati, kuma abokin Mista Nkurinziza ne na kud-da-kud na tsawon shekara 15 da ya yi yana mulki.

    Sabon Firaiministan na fama da takunkumin da Amurka ta kakaba masa saboda zarginsa da hannu cikin wani rikicin siyasa da aka keta hakkin bil-adama a 2015.

    Burundi ta fita daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kan martaba kotun a 2017 lokacin da ake tsaka da binciken kan rikicin da ya biyo bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

    • Za a ci tarar shugaban kasa idan bai sanya takunkumin fuska ba

      Getty

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, An ga shugaban na tari a bainar jama'a ba tare da rufe bakinsa ba

      Wani alkali a Brazil ya bai wa shugaban kasar Jair Bolsonaro umarnin rika sanya takunkumi a bainar jama'a a babban brinin kasar Brasilia da sauran wurare a kasar.

      Shugaban mai ra'ayin rikau ya sha fuskantar suka kan yadda yake tunkarar wannan annoba ta korona, wadda tun farkon bullarta ya ce kawai " 'yar karamar mura ce."

      Ya kuma sha bayyana a cikin mutane ba tare da sanya takunkumi ba, kuma ya rika gaisawa da magoya bayansa ba tare da ba da tazara ba.

      An dauke shi hoton bidiyo a wani gangami da ya fita a baya yana tari ba tare da rufe bakinsa ba, haka kuma an kara daukarsa yana atishawa a hannunsa kuma yana gamawa ya gaisa da wata dattijuwa.

      Alkalin babbar kotun Renato Borelli ya ce matukar shugaban da sauran jami'ansa ba za su rika sanya takunkumin ba a bainar jama'a zai rika cin tararsu dala 387 ko wacce rana.

      • Ana fargabar karuwar ci da gumin yara a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

        Getty

        Asalin hoton, Getty Images

        Hukumomi a Jamhuriyar Dimokoradiyyar Congo na kara nuna fargaba kan yadda iyaye ke aike wa da yaransu wajen hakar ma'adanai na Lualaba da ke kudu maso gabashin kasar duk kuwa da hadarin da wajen ke da shi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

        An samu raguwar bukatar karfe a duniya kamar su Cobalt sakamakon annobar korona, wanda hakan ya janyo raguwar abin da masu hakar ke samu, in ji Reuters.

        Ya kara da cewa fitar da nau'in karfe na cobalt ya ragu da kashi 15.2 cikin 100 a watanni ukun farko wannan shekarar idan aka kwatanta da yadda yake a irin lokacin a bara.

        Fargabar da ake da ita ce idon iyayen ba sa samun kudin da zai ishe su bukatunsu na yau da gobe, za su rika fitar da yaransu daga makaranta suna mai da su ayyukan hakar ma'adanai masu cike da hadari.

        "Tattalin arziki ya fuskanci mumunan koma baya yayin wannan matsalar lafiyar da aka samu, wanda hakan zai shafi abin da iyayen ke samu.. sai dai bai kamata wannan ya zama dalilin amfani da yara wajen aikin hakar ma'adanai ba," in ji wani jami'i da ke lura da harkokin tattalin arzikin yankin.

      • Malalar Mai a Najeriya: Ko 'yan Najeriya za su iya kai ƙarar Shell a Burtaniya?

        Oil Spills

        Asalin hoton, Getty Images

        Kotun kolin Burtaniya za ta saurari kara game da ko al'umomi biyu masu yawan jama'a kimanin 42,000 a Najeriya za su iya shigar da karar kamfanin mai na Shell don neman ya biya su diyya game da gurbatar mahalli sakamakon malalalar mai.

        Al'ummomin biyu sun fito ne daga kabilun Billie da Ogale, babbar kotun Landan ta hanasu izinin neman wata kotun Burtaniya ta bi musu kadi.

        Amma lauyoyinsu za su ce an taba yin wata shari'a irin wannan da ta shafi wani kamfanin hakar ma'adanai mai hedikwata a Landan da kuma wasu jama'ar kauye a Zambia inda kotu ta yanke hukuncin da ya bai wa bangarensu gaskiya.

        Al'ummomin biyu da ke yankin Niger Delta sun yi koken cewa sun yi ta fama da gurbatar muhalli na shekaru da dama saboda bututun mai na reshen kamfanin Shell da ke yankinsu.

        Lauyoyinsu za su yi kokarin fahimtar da alkalan kotun kolin biyar cewa ya kamata a saurari shari'ar 'yan Najeriyan a Landan, la'akari da hukuncin da aka yanke bara.

        A watan Afirilun 2019 kotun ta yanke hukuncin cewa kamfanin hakar ma'adanai mai hedikwata a Birtaniya za a iya samunsa da laifin gurbata muhalli wanda reshensa na KCM da ke Zambia ya haddasa kuma za a iya neman sa da ya biya diyya a Landan.

        Sai dai kamfanin mai na Shell ya dage kan cewa kotun Burtaniyan ba ta da hurumi kan wannan shari'a.

        Kutun kolin Burtaniyan ba za ta mayar da hankali ba ne kan ikirarin neman biyan diyyar ba, za ta karkata ne kan ko za a iya sauraren karar al'ummun Najeriyan a Landan.

      • Ku saurari Labaran Duniya cikin Minti Daya Da BBC Hausa

        Bayanan sautiMinti Daya Da BBC Hausa Na Rana 23/06/2020
      • Trump ya dakatar da ba da biza ga ma'aikata 'yan kasashen waje

        Shugaban Amurka Donald Trump ya tsawaita lokacin bayar da takardar zaman dan kasa ta green card tare da dakatar da bayar da biza ga ma'aikata 'yan kasashen waje har sai karshen 2020.

        Wannan doka za ta shafi manyan kwararru a bangaren fasaha da wadanda ke taimaka wa ma'aikatan da raino ko ayyukan gida har da ma manyan ma'aikatan kamfanoni.

        Fadar White House ta ce matakin zai ba da damar samar da ayyukan yi ga Amurkawan da annobar cutar korona ta shafi tattalin arzikinsu.

        Amma masu suka sun ce Fadar White House na amfani da annobar cutar korona wajen tsananta dokokin shigar baki kasar.

        Trump

        Asalin hoton, Getty Images

      • Dan kunar bakin wake ya kai hari a Kwalejin sojin Somalia

        Wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a gaban ƙofar shiga wata makarantar horar da sojoji a Mogadishu babban birnin Somaliya a safiyar Talata, inda a ƙalla mutum biyu suka mutu.

        Ɗan ƙunar baƙin waken ya tayar da bam ɗin ne yayin da jami'an tsaro ke ƙoƙarin kama shi a daidai lokacin da ya ke ƙoƙarin bin layi tare da saɓɓin sojojin da ke ƙoƙarin shiga makarantar horan sojin mallakar Turkiyya.

        Makarantar mai suna TURKSOM, ita ce makarantar horon soji mallakar Turkiyya a ƙasashen waje mafi girma wadda ta shafe kusan shekaru uku tana horas da sojojin Somaliya.

        Ƙungiyar al-Shabab ce ta ɗauki nauyin harin da aka kai a makarantar.

      • Jarirai 'yan uku sun kamu da cutar korona

        Wasu jarirai 'yan uku a Mexico sun kamu da cutar korona, duk da yake ba su yi hulɗa da kowanne mutum da aka san yana da cutar ba.

        Ƙwararru a fannin lafiya sun yi hasashen cewa mai yiwuwa sun kamu da korona ne ta hanyar mahaifar babarsu a lokacin goyon ciki.

        A yanzu ana gwada iyayen, waɗanda hukumomi ke cewa mai yiwuwa suna ɗauke da cutar ba tare da nuna alamominta ba.

        Biyu daga cikin jariran, mace da namiji, na nan lafiya.

        Yayin da ɗaya namijin ke karɓar magani saboda wata larurar numfashi.

        Masana kimiyya sun yi imani lamarin na iya ƙarin haske kan yadda ƙwayar cutar korona ke yaɗuwa.

        jarirai 'yan uku

        Asalin hoton, Getty Images

      • Maniyyata 10,000 ne kawai za su yi aikin hajjin bana

        Hajj

        Asalin hoton, Getty Images

        Kasar Saudiyya ta ce za ta bar maniyyata 10,000 ka dai da ke zaune a kasar domin yin aikin hajjin bana, domin dakile yaduwar cutar korona.

        “Ba daruruwan mutane bane za su yi hajji a bana”, in ji ministan aikin hajji Mohammad Benten.

        Miliyoyin mutane na ziyartar biranen Makkah da Madina yayin aikin Hajjin.

        A lokutan da duniya ke cikin kwanciyar hankali, aikin Hajji na cikin mafi muhimman ayyukan addini ga Musulmin duniya a kowace shekara.

        Saudiyya na da masu dauke da kwayar cutar korona fiye da 160,000, wanda cikinsu fiye da mutun 1,300 sun riga mu gidan gaskiya.

        Ma'aikatar aikin Hajjin ta Saudiyya ta sanar da cewa an dauki wannan matakin ne a matsayin kiyaye maniyyata kamuwa da cutar ta korona.

        A Gabas ta Tsakiya, Iran da Turkiyya ne kawai suka fi Saudiyya yawan masu fama da cutar korona.

      • Kotu ta soke sammacin kama Jacob Zuma

        ZUMA

        Asalin hoton, EPA

        Babbar kotun a kasar Afrika ta Kudu ta soke sammacin kama tsohon shugaban kasar, Jacob Zuma bayan da lauyoyinsa suka mika wa kotun takardar shaidar rashin lafiyarsa.

        A cikin wata Fabarairu ne kotu ta bada sammacin kama Mr Zuma bayan ya ki bayyana a gabanta.

        Lauyoyinsa sun ce tsohon shugaban kasar a wancan lokacin yayi balaguro zuwa kasar Cuba domin karbar magani.

        A yau aka ci gaba da sauraron karar a shari’ar da ake masa bisa zargin ya karbi cin hanci a wajen wani kamfanin kasar Faransa shekaru 20.

        An dage sauraron kasar zuwa watan Satumba.