Korona: Najeriya za ta gwada magungunan gargajiya 3

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Mustapha Musa Kaita and Halima Umar Saleh

  1. Trump ya zargi Twitter da hana shi 'yancinsa

    Shugaba Trump ya soki Twitter da hana shi 'yancin fadin albarkacin baki bayan a karon farko shafin ya bayyana wani sako da shugaban ya wallafa a matsayin na yaudara.

    Wannan yaki da Twitter ya soma ne lokacin da Mista Trump mai mabiya sama da miliyan 80 ya yi ikirarin cewa amfani da wasiku wajen kada kuri'a a zaben kasar da ke tafe zai haddasa mummunan magudin zabe.

    Kamfanin Twitter ya mayarda martani ta hanyar tura wa mutane wani shafi da ke dauke da makala ta musamman da cikakkun bayanai da ke karyata ikirarin shugaban.

    A farkon wannan watan Twitter ta fito da sabon tsarin dakile bayanan karya, wanda ke taimakawa wajen ganon sahihancin labarai musamman a kan cutar korona.

    Trump

    Asalin hoton, EPA

  2. Ban taba mika ikona ga Abba Kyari ba - Buhari

    Fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Buhari bai taba mka ikonsa na gudaar da mulki ga tsohon shugaban ma'aikanta Malam Abba Kyari ba.

    Wa sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar, ya wallafa a shafnsa na Twitter ranar Talata, ta musanta cewa Shugaba Buhari ya soke nade-naden da marigari Abba Kyari ya sanya wa hannu.

    "An ja hankalin fadar shugaban kasa kan wasu rahotanni da ke zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhariya soke wasu ayyuka da nade-nade da tsohon shugaban ma'aikata ya sanya wa hannu.

    Bamu yi mamaki ba, saboda rahotannin ba su ambato sahihanci majiyoyi ba. Babu kanshin gaskiya a wadannan rahotanni kuma ya kamata yan Najeriya su yi watsi da su," a cewar Garba Shehu.

    Ya kara da cewa 'yan Najeriya ne suka "sake zaben Shugaba Buhari a watan Fabrairun 2019. Bai sarayar da ikon da 'yan Najeirya suka dora a kansa ba kuma ba zai taba sarayar da shi ga kowa ba."

    A baya dai, jami'an gwamnati da dama cikin har da mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, sun zargi tsohon shugaban ma`aikata a fadar, Abba Kyari da yin shisshigi a cikin al`amuran da basu shafe su ba.

    Abba Kyari ya rasu a watan jiya bayan ya yi fama da cutar korona.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Abba Kyari da Buhari

    Asalin hoton, BUHARI SALLAU

  3. An kori 'yan sanda huɗu daga aiki saboda kashe baƙar-fata a Amurka

    Magajin birnin Minneapolis da ke Amurka ya kore 'yan sanda hudu daga aiki wadanda ake zargi da sanadin mutuwar wani mutum bakar- fata bayan sun kama shi.

    A hotunan bidiyon da ganau suka nada a ranar Litinin, an ji mutumin, wanda yake da kimanin shekara 40, yana ihu yana gaya wa daya daga cikin 'yan sanda wanda ya danne shi da gwiwar kafarsa cewa "ba na iya numfashi."

    Magajin birnin, Jacob Frey ya yi Allah-wadai da abin da ya faru wanda ya bayyana a matsayin babban kuskure, sannan ya ce kasancewar mutum bakar-fata a Amurka ba laifin kisa ba ne.

    Wannan lamari ya tuna wa mutane abin da ya faru da wani bakar-fata mai suna Eric Garner, wanda ya mutu lokacin da aka tsare shi a shekarar 2014.

    An shake wuyan Garner da wani karfe inda ya rika cewa "Ba zan iya yin numfashi ba" kusan sau goma sha biyu.

    Wannan kalami nasa ya zama wani furuci da masu fafutuka suka rika yi a wajen zanga-zangar kyamar cin zarafin da 'yan sanda suke yi wa bakaken-fata a Amurka.

    Dan sanda

    Asalin hoton, DARNELLA FRAZIER

  4. Najeriya za ta gwada hydroxychloroquine don maganin cutar korona

    Magani

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriya za ta ci gaba da shirinta na gwada maganin cutar maleriya hydroxychloroquine a kan masu fama da cutar korona duk da matakin da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta dauka na dakatar da irin wannan gwaji saboda fargabar illar da zai haifar..

    Shugabar Hukumar Abinci da Magunguna ta kasar (Nafdac), Mojisola Adeyeye, ta shaidawa gidan talbijin na TVC cewa ko da yake ba ta jayayya da matakin na WHO amma tana so a gwada maganin a kasar domin su ga tasirinsa.

    “Ban san abin da suke son cimma ba, ko sun yi nazari ne a kan al'ummar Caucasia ko kuma 'yan Afirka. Idan suna son cimma wani buri ne kuma suka gwada maganin a kan al'ummar Caucasia, babu laifi. Amma ba na tsammani sun samu sakamako na tasirin maganin a kan al'ummar Afirka, saboda kwayoyin halittarmu daban suke da na wadancan," a cewarta.

    Farfesa Adeyeye ta kara da cewa za a kammala gwajin tsakanin wata uku zuwa hudu.

    Wani bincike da aka wallafa a mijallar kimiyya ta The Lancet a kwanakin baya ya nuna cewa maganin zai iya haddasa mutuwa ga maru dauke da cutar korona.

    Kauce wa YouTube
    Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba. Ana yi samun tallace-tallace YouTube

    Karshen labarin da aka sa a YouTube

  5. Buɗewa

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Nasidi AdamuYahaya ne yake yi muku barka da warhaka.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanar da ku halin da duniya take ciki.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.