Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kamfanoni, gidajen abinci, bankuna za su ci gaba da aiki a Legas

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Mun zo karshe

    Muna godiya da kasancewa da kuka yi da mu tun daga safiya, yayin da muka zo karshen rahotannin a wannan shafi.

    Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya kuma mu hadu gobe.

  2. Kamfanoni, gidajen abinci, bankuna za su ci gaba da aiki a Legas

    Kamfanoni masu zaman kansu a Jihar Legas na da damar ci gaba da ayyukansu cikin kashi 60% na abin da suka saba yi, kamar yadda Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ba su dama.

    Gwamnan ya ce suna da damar yin hakan daga karfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana. Ya bayyana haka ne a wurin taron manema labarai ranar Lahadi a birnin Legas.

    Su ma masu gidajen sayar da abinci an ba su irin wannan damar, inda za su rika budewa daga karfe 9:00 na safe zuwa 7:00 saboda Azumin Ramadana.

    "Masu gidajen abinci, idan har sun amince za su rika samar wa ma'aikatansu ababen sufuri, sannnan kuma a saya a tafi da shi, to za su iya budewa domin mutane su samu su sha ruwa a wannan lokaci na azumi," in ji Sanwo-Olu.

    Kasuwanni za su rika budewa a ranakun Talata da Alhamis da Asabar - kasuwanni da shagunan sayar da kayan abinci ne kadai ke da wannan damar. Kasuwannin da ba na abinci ba kuma, za su bude a ranakun Litinin da Laraba da Juma'a daga karfe 9:00 zuwa 3:00.

    Kazalika gwamnan ya karfafa wa bankuna gwiwar ci gaba da ayyuka, inda su ma za su bude daga karfe 9:00 zuwa 3:00.

    Jihar Legas na da mutum 1,084 da suka harbu da cutar korona zuwa yanzu, a cewar ma'aikatar lafiyar jihar, 28 sun mutu daga cikinsu sannan an sallami 247.

  3. United za ta tuhumi Rojo da karya dokar hana fita

    Manchester United za ta tuhumi Marcos Rojo, bayan ya karya dokar da Argentina ta kafa ta hana zirga-zirga don gudun yada cutar korona.

    An saka hotunan Rojo a kafar sada zumunta tare da abokansa suna zukar taba da wasan kwallon teburi.

    Dan uwan Rojo mai suna Franco ne ya saka hotunan a shafinsa na sada zumunta kuma daga baya ya goge.

    Yanzu Rojo yana buga wasannin aro ne a kungiyar Estudiantes.

    Argentina ta kafa dokar hana fita da za ta kare ranar 10 ga watan Mayu.

  4. Coronavirus: Wani maganin gargajiya ya karbu a wurin wasu shugabannin Afirka

    Shugaban Tanzania ya ce zai tura jirgin sama zuwa kasar Madagascar domin jigilar wani maganin gargajiya da aka hakikance cewa yana maganin cutar korona.

    Shugaban kasar Congo-Brazzaville ma ya yi alkawarin safarar maganin.

    An samar da maganin ne daga ganyen artemisia, wanda da shi ake hada maganin zazzabin malaria.

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce babu wata hujja da ke tabbatar da wani maganin korona sannan ta gargadi mutane da su guji yin maganin cutar da kansu.

    An kaddamar da maganin a matsayin Covid-Organics sannan an fara kasuwancinsa bayan an gwada shi a kan mutum 20 a tsawon mako uku, a cewar shugaban ma'aikatan fadar shugaban Tanzania.

  5. Korona ta kashe ministan Nijar Ben Omar

    Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa ministan kwadagon kasar Malam Ben Omar ya rasu a ranar Lahadi sakamakon cutar korona.

    Omar shi ne minista na farko a kasar da korona ta yi ajalinsa.

    Kafin rasuwarsa, shi ne shugaban jam'iyyar PSD Basira wadda ke cikin kawancen masu mulki.

    Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan ministan da jam'iyyarsa da kum a 'yan kasa baki daya.

    Ya zuwa yanzu, mutum 29 ne suka rasu a Nijar sakamakon cutar korona, yayn da 696 suka har bu da ita, sai kuma 350 da suka warke.

  6. Spaniya ta samu adadi mafi karanci na wadanda suka mutu a rana guda

    An samu adadi mafi karanci na wadanda suka rasa rayukansu a rana guda a Spaniya tun bayan saka dokar hana fita a tsakiyar watan Maris, inda mutum 164 suka mutu a cikin awa 24 da suka gabata.

    An samu raguwar sabbin wadanda suka harbu da cutar ma a karon farko duk da yawan gwajin da aka kara.

    A wurin wani taron manema labarai a birnin Madrid, shugaban sashen gaggawa na hukumar lafiya, Fernando Simon ya ce adadin mai kyau ne amma ya yi gargadin cewa da ma akan samu karancin adadi a karshen mako.

    Mutum 25,100 ne suka mutu jumilla, a cewar alkaluman Jami'ar Johns Hopkins.

  7. Adadin wadanda ke rasuwa a Italiya na ci gaba da raguwa

    Italiya ta sanar da karin mutuwar mutum 174 sakamakon annobar korona, adadi mafi karanci cikin wata biyu da suka gabata.

    Hakan na zuwa ne yayin da kasar ke shirin sassauta dokar kulle. Shi ma adadin wadanda ke jinyar cutar da wadanda ke sashen kulawar gaggawa na ci gaba da raguwa.

    Dagaa ranar Litinin, 'yan Italiya za su samu damar fita motsa jiki, matukar dai za su kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

    Za kuma su samu damar ziyarar 'yan uwa - ban da abokai - a cikin yankinsu. Gwamnati ta yi hakan ne domin ta wayar da kai game da irin ziyarce-ziyarcen da aka bai wa mutane damar yi.

  8. Wadanda suka halarci jana'izar Abba Kyari sun tsallake rijiya da baya

    Sashin lafiya na hukumar babban birnin Najeriya – Abuja ya sanar da cewa wadanda suka halarci jana’izar Malam Abba Kyari, tsohon shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa duk basu kamu da cutar korona ba.

    Sanarwar da mukadashin sakataren lafiyar na Abuja, Dr M B Kawu ya sanya wa hannu ta ce an yi wa mutanen gwaji kuma dukkaninsu babu wanda ya harbu da cutar Covid 19.

    Sanarwar ta ce mutanen duk suk kammala kwana 14 da doka ta yarda na su kebe kansu a don haka a yanzu sun koma wajen iyalansu.

  9. Wasu mutum 315 sun mutu a Birtaniya

    Jumillar mutum 28,446 ne suka rasa rayukansu a fadin Birtaniya sakamakon annobar cutar korona, bayan an samu karin 315 a alkaluman ranar Asabar.

    Adadin ya hada da wadanda suka mutu a asibiti da gidajen kulawa da gajiyayyu.

  10. An killace iyalan marigayi Sarkin Kauran Namoda

    Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta ce ta killace iyalan marigayi Mai martaba Sarkin Kauran Namoda da Allah ya yi wa rasuwa da safiyar Lahadi.

    Alhaji Muhammad Ahmad Asha ya nuna alamun cutar korona kafin cikar wa’adinsa.

    Kwamishinan lafiya na Zamfara Yahaya Muhammad Kanoma ya ce sarkijn ya rasu ne a dakin da aka killace shi da masu jinyarsa a asibiti yayin da ake jiran sakamakon gwajin da aka yi masa, wanda aka tura Abuja.

  11. Za a ci gaba da Bundesliga a watan Mayu

    Ranar Lahadi ministan harkokin cikin gida na Jamus, Horst Seehofer ya goyi bayan a ci gaba da gasar Bundesliga ta kakar 2019-20 ba tare da 'yan kallo ba.

    A makon da za mu shiga, gwamnatin Jamus za ta yi taro tare da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki kan zakulo hanyoyin da ya kamata a bi domin karkare gasar shekarar nan.

    Kodayake tuni wasu kungiyoyin Jamus suka koma atisaye na daidaiku da na rukuni-rukuni saboda bin dokar da gwamnati ta saka ta bayar da tazara.

  12. Dangote ya gina katafariyar cibiyar gwajin Korona a Kano

    Wata gidauniya karkashin jagorancin attajiri Alhaji Aliko Dangote mai suna Aliko Dangote Foundation (ADF), za ta kaddamar da wata katafariyar cibiyar gwajin cutar korona a Jihar Kano ranar Lahadi.

    Cibiyar wadda za ta fara da gwajin samfuri 400, ana sa ran za ta koma gwada samfuri 1,000 nan da ranar 10 ga watan Mayu a kowacce rana.

    Tuni kamfanin 54Gene ya kafa irin wannan cibiya a jihohin Legas da Ogun, kuma shi ne zai kafa ta Kano.

  13. Sabon salon kiran sallah da annobar korona ta kawo

    Sakamakon hana sallar jam'i da hukumomi a kasashen duniya daban-daban suka yi don kiyaye lafiyar jama'a daga cutar korona, yanzu masu kiran salla wato ladanai, na amfani da salon kiran salla na lokacin annoba.

    Maimakon yadda aka saba inda ladan kan yi kira ga jama'a su hallara domin a yi sallar jam'i, yanzu ladanai kan yi amfani da wasu kalamai na daban - na bukatar jama'a su yi salla a gidajensu.

    Wannan wani salon kiran salla ne da mutane da dama ba su taba ji ba sai a wannan lokaci na annobar Korona.

    "Yanzu idan mun kira sallah sai mu ce ala sallu fi rihalikum ko kuma fi biyutikum wato ku yi sallah a gidajenku," in ji Zakariyya Muhammad, babban ladanin masallaci na kasa da ke Abujar Najeriya.

  14. Cutar korona ta kashe dan majalisa a Nasarawa

    Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce cutar korona ta yi ajalin wani dan majalisar jiha Hon Sule Adamu.

    Gwamnan jihar Abdullahi Sule ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar ga manema labarai yayin da yake bayani kan halin da ake ciki kan annobar korona.

    Mai taimakawa gwamman kan harakokin watsa labarai ya shaida wa BBC cewa dan majalisa ya nuna alamun cutar korona kuma ya rasu ne kafin fitar da sakamakon gwajin da aka yi masa na cutar.

    Gwajin kuma ya tabbatar da yana dauke da cutar.

    Yanzu gwamnatin ta rufe zauren majalisar jihar tare da killace dukkanin 'yan majalisar don dakile bazuwar cutar a jihar.

  15. An tilasta wa motar fasinja komawa Katsina daga Abuja

    Jami'an tsaro a Abuja babban birnin Tarayya sun kama wata mota bas ta daukar fasinja da ta fito daga Katsina duk da dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya ta kafa.

    A cikin wani bidiyon da aka wallafa a shafin Twitter na hukumomin birnin Tarayya, shugaban rundunar hadin guiwa ta jami'an tsaro a Abuja Ikharo Attah ya ce sun tilastawa direban motar da fasinjan da ke ciki komawa inda suka fito.

    Ya kuma ce ba za su lamunce wa keta dokar kulle ba da aka kafa da nufin dakile bazuwar cutar korona.

  16. Gwamnatin Nasarawa ta mayar da Almajirai jihohinsu na asali

    Gwamnatin Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya ta fara mayar da almajirai zuwa jihohinsu na asali.

    Gwamnatin ta wallafa a Twitter hotunan almajiran yayin da suke shiga motocin da za su mayar da su jihohinsu.

    Amma a sanarwar, gwamnatin Nasarawa ba ta bayyana jihohin da almajiran suka fito da za a mayar da su ba.

    Rahotanni sun ce almajiran sun kai kusan 800 da gwamnatin ta tara za ta mayar da su garuruwansu. Kuma jihohin da rahotanni suka ce za a mayar da almajiran sun hada da Kaduna da Jigawa da Gombe da Filato da kuma jihar Taraba.

    A karshen watan Afrilu ne Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 suka sanar da rufe dukkanin makarantun tsangaya da zummar shawo kan annobar korona a yankin.

    Gwamnatin Kaduna ta ce almajiran da aka dawo da su daga Kano ne ya kara yawan adadin masu cutar korona a jihar.

  17. Mutum 10,000 sun kamu da korona a rana ɗaya a Rasha

    A ƙasar Rasha mutum 10,000 sun kamu da cutar korona a rana ɗaya, wanda shi ne adadi mafi girma tun ɓullar cutar a kasar.

    Waɗanda suka kamu sun fi yawa a Moscow inda asibitoci ke aiki a ko da yaushe.

    Sai dai ba a samu ƙaruwar adadin waɗanda suka mutu ba daga 1,280 da cutar ta kashe a Rasha.

    Cutar ta kama Firaminista da kuma wasu manistoci.

    Zuwa yanzu mutum 134,687 suka kamu da cutar korona, kamar yadda alƙalumman jami'ar Johns Hopkins suka nuna.

    Rasha ta ruɓanya yawan adadin gwaji a rana inda a yanzu aka yi wa sama da mutum 40,000 gwaji a Moscow kawai a rana ɗaya

  18. Mai dauke da cutar korona ta tsere bayan killace ta a Taraba

    Rahotanni daga Taraba sun ce daya daga cikin majinyatan cutar korona ta tsere daga cibiyar da aka killace su.

    Kafar talabijin ta Channels ta ce kwamishinan lafiya Innocent Vakkai kuma jagoran yaki da cutar korona a jihar ne ya sanar da haka yayin ganawa da manema labarai.

    Ya ce wata mata ce ta tsere, kuma suna kan kokarin gano ta.

    Zuwa yanzu mutum takwas aka tabbatar da sun kamu da cutar korona a jihar Taraba

  19. Yawan masu mutuwa a Spain na ci gaba da raguwa

    A karon farko an samu karancin adadin mutanen da cutar korona ke kashewa a rana daya, tun kafa dokar hana fita a tsakiyar watan Maris.

    An samu karin mutum 164 da suka mutu, kuma an samu raguwar wadanda ke kamu da cutar duk da fada gwaji da aka yi.

    Sai dai masana na ganin yawanci a karshen mako adadin na raguwa.

    Spain dai ta sassauta kulle a kasar daga ranar litinin, yayin da aka tilasta saka abin rufe fuska da kuma haramta jigilar motocin safa.

  20. Jami'an lafiya 16 sun kamu da korona a Borno

    Gwamnatin Borno ta ce jami'an lafiya 16 sun kamu da cutar korona

    Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Salisu Kwayabura yayin da yake bayani kan halin da ake ciki kan cutar korona a jihar ya ce cikin sa'a 48 jami'an lafiya 16 ne suka kamu da korona a Borno.

    Ya ce sun kara daukar matakai domin kare jami'an lafiyar a jihar.

    Gwamnatin kuma ta ce za ta samar da sabuwar cibiyar killace masu cutar korona a jihar bayan wadanda ake da su a Ngarannam da kuma asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri sun cika da kusan kashi 50.

    Gwamnatin Borno kuma ta bayyana damuwa kan yadda har yanzu wasu al'ummar jihar ba su yadda da akwai cutar korona ba.

    Mataimakin gwamnan jihar Umar Usman Kadafur ya ce mutane na bayyana shakku kan cutar korona kamar yadda suka lokacin da aka fara samun rikicin Boko Haram.

    "Cutar korona wani rikicin Boko Haram ne ke tafe, amma duk da haka mutane ba su yarda ba," in ji shi.