Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kamfanoni, gidajen abinci, bankuna za su ci gaba da aiki a Legas

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Labarai da dumi-dumi, Jarman Kano Farfesa Isa Hashim ya rasu

    Allah Ya yi wa Jarman Kano Farfesa Isa Hasim rasuwa

    Ya rasu ne a ranar Lahadi yana da shekara 86 kamar yadda wani surukinsa ya tabbatar wa BBC.

    Babu dai wani cikakken bayani kan dalilin rasuwarsa.

    Amma rasuwarsa na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 da rasuwar Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila wanda Allah Ya karbi ransa a ranar Asabar.

  2. Cutar korona za ta jefa miliyoyin yara cikin hatsari

    Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef ya yi gargadin cewa annobar cutar korona za ta jefa miliyoyin yara a Gabas ta tsakiya da arewacin Afirka cikin hatsarin rashin samun rigakafin cutuka.

    Hukumar Unicef ta ce an dakatar da ayyukan da suka shafi rigakafi ga yankunan yayin da hankalin ma'aikatan lafiya ya karkata ga yaki da cutar korona.

    Hukumar ta ce wannan zai sa duk yaro ɗaya cikin biyar ƴan kasa da shekara biyar za su rasa samun rigakafin cutar foliyo.

    Sannan hukumar ta ce kusan yara rabin miliyan ƴan kasa da shekara 15 za su rasa rigakafin kyanda.

  3. Za a dawo yin Sallar jama'i a Iran

    Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce za a bude masallatai ranar Litinin a a biranen da cutar korona ba ta bazu sosai ba.

    Shugaban ya ce za a dawo da yin sallar Juma'a amma sai idan masallatan sun kiyaye matakan kariya.

    Ya kara da cewa za a ci gaba da bude harakokin kasuwanci, yayin da tuni aka ba masu aski da cibiyoyin wasanni damar budewa.

    Cutar korona ta fi yi wa Iran illa a yankin Gabas ta tsakiya, inda alkalumma suka nuna sama da mutum dubu shida suka mutu, ko da yake ana ganin alkalumman sun fi haka.

  4. Budewa

    Jama'a barkanmu da wannan rana ta Lahadi, da fatan kun wayi gari lafiya lafiya.

    Awwal Janyau ke muku barka a wannan shafinmu da muke kawo labarai da rahotannikai-tsaye daga sassan duniya musamman game da annobar cutar korona.

    Ga kadan daga cikin abubuwan da suka faru da dare zuwa wayewar gari a takaice:

    ·Sama da mutum miliyan 3.3 suka kamu da cutar korona a duniya, yayin da cutar ta kashe fiye da mutum 240,000

    ·Yawan masu cutar korona a Najeriya ya kai 2,388 bayan samun karin mutum 220 a ranar Asabar.

    ·Karin mutum 17 sun mutu a Najeriya a rana daya inda adadin wadanda suka mutu a kasar suka kai 85.

    ·Al'ummar garin Rano da ke Jihar Kano arewacin Najeriya sun wayi gari cikin yanayi na jimami bayan rasuwar mai Martaba sarkin Rano, Tafida Abubakar Ila a yammacin Asabar.

    ·Yawan wadanda cutar korona ta kashe a Amurka sun kai 65,000, kamar yadda jami’ar Johns Hopkins ta bayyana

    ·Za a bude mujami'u a Jamus karon farko tun bayan sanya dokar hana fita a watan Maris.

    ·Iran za ta bude masallatai a ranar Lahadi a biranen kasar.