Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cikin watan Mayu ake sa ran ci gaba da wasannin Bundesliga kakar 2019-20
Ranar Lahadi ministan cikin gida na Jamus, Horst Seehofer ya goyi da bayan a ci gaba da gasar Bundesliga ta kakar 2019-20 ba tare da 'yan kallo ba.
A makon da zamu shiga gwamnatin Jamus za ta yi taro tare da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki kan zakulo hanyoyin da ya kamata abi a karkare gasar shekarar nan.
Koda yake tuni wasu kungiyoyin Jamus suka koma atisaye na daidaiku da na rukuni-rukuni saboda bin dokar da gwamnati ta saka ta bayar da tazara.
A cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasanni a Jamus don gudun yada cutar korona, yanzu ana sa ran gwamnatin Jamus za ta yadda a karkare gasar Bundesliga ta shekarar nan.
Mahukuntan da ke gudanar da gasar lik a Jamus sun mika wa gwamnati tsare-tsare da suka yi na ganin an koma wasanni ba tare da 'yan kallo ba.
Cikin tsarin da aka gabatar har da gwajin 'yan wasa, amma babu batun killace 'yan kwallo koda an samu kungiya dauke da mai cutar.
Kawo yanzu Bayern Munich ce ke jan ragamar teburin Bundesliga da maki 55, sai Borrusia Dortmund ta biyu da maki 51, sai ta uku RB Leipzig mai maki 50, bayan kammala wasannin mako 25.
Robert Lewandowski na Bayern Munich ke kan gaba da kwallo 25 a raga, sai Timo Werner na Rb Leipzig da 21, yayin da Jadon Sancho na Borrussia Dortmund keda 14 a raga.
Sama da mutum 6,600 cutar korona ta hallaka a Jamus, kuma fiye da 162,000 suka kamu da annobar.