Kaduna ta sake gano masu korona 14 cikin almajiran Kano

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana karon farko

    Kim Jong-un

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana karon farko a cikin kusan mako Uku, hakan ya kawo karshen rashin ganinsa da ya soma daukan hankali tsakanin kasashen da ke jita-jita kan lafiyarsa.

    Kamfanin dilancin labaran kasar ya ce ya kaddamar da masana'antar taki a kusa da birnin Pyongyang.

    An fitar da hotunan da ke nuna shi lokacin da yake bude masana'antar cikin yanayi na fara'a tare da wasu jami'an gwamnati.

    Babu dai wani bayani kuma ba a ambato inda Mista Kim ya shiga kwana biyu ba, ko dalilan rashin ganinsa har a taron kasar mai muhimmanci da aka gudanar a tsakiyar watan Afrilu.

  2. Amurka za ta gaggauta amfani da Remdesivir a matsayin maganin cutar korona

    Remdesivir

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomi a Amurka su bada umarni a gaggauta fara amfani da kwayar Remdesivir a matsayin maganin cutar korona.

    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka FDA ta dau wannan matakin ne bayan gwaji ya nuna cewa maganin na rage yawan alamun cutar.

    Maganin wanda tun farko an samar da shi ne domin magance cutar Ebola.

    Kamfanin Gilead, wanda ya ke yinsa, ya bayyana yunkurin a matsayin mai matukar amfani kuma irinsa na farko, sannan zai bayar da kyautar kwalbar allurar miliyan daya.

    Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence ya ce za a fara raba maganin zuwa asibitoci a ranar Litinin.

  3. Indiya ta tilasta amfani da waya mai nuna masu cutar korona

    Corona India

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Indiya ta tilastawa ma'aikata a ƙasar yin amfani da wata manhaja a wayar salula da aka samar da za ta gano mutanen da suka kamu da cutar korona.

    Wannan matakin na zuwa a yayin da gwamnatin ta fara sassauta dokar kulle a yankunan da babu cutar sosai.

    Manhajar mai suna Arokya Setu, a watan da ya gabata ne aka ƙaddamar da ita. Tana sanar da masu amfani da ita idan sun yi cudanya da mutanen da gwaji ya tabbatar da suna dauke da cutar korona.

    Masu gwagwarmaya dai na bayyana damuwa kan bayanan da ake samu za su iya keta sirrin mutane.

  4. Cutar korona ta fantsama cikin al’umma a Kano – Dr Sani Gwarzo

    Bayanan sautiCutar korona ta fantsama cikin al’umma a Kano – Dr Sani Gwarzo

    Tawagar ƙwararrun likitoci da suka je Kano domin kai wa jihar ɗauki, sun ce abin da ake tsoron ya faru ya riga ya faru a Kano.

    Dakta Nasiru Sani Gworzo, ɗaya daga cikin tawagar ƙwararrun likitocin ya shaidawa shirin Ra’ayi Riga na BBC cewar cutar korona daga mataki na ɗaiɗaikun al’umma yanzu ta fantsama cikin al’umma.

    "Zance mafi inganci yanzu, korona ita ta ke yin awon gaba da yawancin mutanen da suke mutuwa,” in ji shi.

    Ya ce kafin cutar korona ana zuwa asibiti, wasu na zuwa ƙasashen waje neman lafiya amma yanzu ba wurin zuwa. Irin haka ya sa mutanen da ba ma korona ba ce suke mutuwa.

    "Amma akwai korona ita kanta, domin adadin da muke gani a gwaje gwaje a baya, idan aka kai samfur 100 ana samun biyar zuwa 10 masu korona amma yanzu idan aka kai 100 za a dawo da 80 duk korona ce.

    Dakta Gwarzo ya ce abubuwan da suka gano suna da yawan gaske.

    Ya ce bayan an dawo da yin gwaji a Kano, kuma za a bude sabon ɗakin gwaji wanda za a iya linka adadin yawan waɗanda ake yi wa gwaji a rana.

  5. Zan yi tsawon rai - Ghali Naabba

    Tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya Ghali Umar Naabba ya ce yana fatan zai yi tsawon rai kamar yadda a al'adance ake faɗa idan an yi wa mutum ƙaryar mutuwa.

    Naabba wanda ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa ya rasu, ya shaida wa BBC cewa ƙaryar mutuwa ba sabon abu ne a Najeriya.

    Ya ce ƙaryar cewa ya rasu, zai iya sa Allah ya kara masa tsawon rai a duniya, kamar yadda ya shaida wa Yusuf Yakasai a tattaunawarsu.

    Bayanan sautiZan yi tsawon rai - Ghali Naabba
  6. Kano ce yanzu ta biyu a yawan masu korona a Najeriya

    Gwamna Ganduje

    Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

    Yawan masu kamuwa da korona a jihar Kano sun lunlluka a kwanakin baya-baya nan bayan gwamnati ta dauki matakai sakamakon mace-macen da aka samu.

    Alkalumman Hukumar da ke dakile cutuka masu a yaduwa a Najeriya sun nuna an samu karuwar yawan masu cutar korona zuwa 311 daga 77 da aka ruwaito a farkon karshen makon da ya gabata.

    Yanzu Kano ita ce jiha ta biyu a jerin jihohin Najeriya da cutar ta bazu bayan jihar Legas.

    Mutum 8 ne aka tabbatar da cutar korona ta kashe a Kano. Ana ganin dai an samu karuwar yawan masu kamuwa da cutar ne bayan hankali gwamnati ya karkata zuwa jihar bayan mace-macen da aka samu kwanakin baya.

    A ranar Litinin Shugaba Buhari ya kafa dokar kulle a Kano ta tsawon mako biyu domin dakile bazuwar cutar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Manufar dokar hana fita

    A birnin Wuhan na China aka fara samun barkewar cutar korona, kuma an yi nasarar dakile cutar ta hanyar kafa dokar hana fita.

    Bayanan bidiyo, Dokar hana fita ita ce babbar hanyar dakile coronavirus
  8. Shugaban AIT da iyalansa 7 sun kamu da cutar korona

    Shugaban kamfanin sadarwa na DAAR Communication, Raymond Dokpesi da iyalansa bakwai da suka kunshi har da surukinsa gwaji ya tabbatar da suna dauke da cutar korona.

    Tun da farko ɗansa Raymond Dokpesi Jnr ya fara kamuwa da cutar kwanaki uku da suka gabata.

    Kafar AITLive ta ce gwajin da hukumar dakile cutuka masu yaduwa NCDC ta gudanar kan iyalan Dokpesi sun tabbatar da mutum takwas na dauke da cutar.

    Kafar ta ce Dokpesi da iyalansa da ke dauke da cutar yanzu haka an killace su a asibitin koyarwa ta Jami'ar Abuja da ke Gwagwalada inda ake kula da masu cutar korona.

    shugaban kamfanin AIT

    Asalin hoton, AIT

  9. Barka

    Jama'a barkanmu da wannan rana ta Asabar, da fatan kun wayi gari lafiya lafiya.

    Awwal Janyau ke muku barka a wannan shafinmu da muke kawo labarai da rahotannikai-tsaye daga sassan duniya musamman game da annobar cutar korona.

    Ga kadan daga cikin abubuwan da suka faru da dare zuwa wayewar gari a takaice:

    Amurka ta amince a fara amfani da maganin Ebola Remdesivir a matsayin maganin cutar korona. Kamfanin da ya samar da maganin ya ce ya bayar miliyan daya da rabi na maganin domin warkar da masu korona.

    Gwamnatin Kaduna ta Mallam Nasir El-Rufai ta haramta shiga da ratsa jihar da dare

    Karin mutum 92 sun harbu da cutar korona cikin sa'a 24 a jihar Kano, inda yanzu adadin wadanda suka kamu suka kai 311.

    An samu mutum 238 da suka kamu da cutar korona a Najeriya a rana daya, adadi mafi girma tun bullar cutar a kasar.

    Kusan mutum 10 aka kara samu da suka mutu a Najeriya, inda adadin wadanda suka mutu suka kai mutum 68

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tanadi ma'aikata 3,000 a Jihar Kano da za su yi aikin dakile yaduwar cutar korona a jihar.