Kaduna ta sake gano masu korona 14 cikin almajiran Kano

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai tsaye dangane da annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Sai da safenku

    Karshen rahotannin kenan a wannan shafi.

    Umar Mikail na fatan za ku ci gaba da karanta labarai a kasan shafin da kuma can farkonsa.

    Mu zama lafiya.

  2. Mutum 22 sun warke daga cutar korona a Legas

    Yayin da adadin mutanen da ke kamuwa da cutar korona ke karuwa, wasu na warkewa a Jihar Legas, inda gwamnati ta ce ta sallami mutum 22.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafnita na Twitter, takwas daga cikin 22 din mata ne, 14 kuma maza.

    An sallame su ne daga cibiyoyin killace masu jinyar cutar da ke Yaba da Luth da Lekki.

    Ya zuwa yammacin Asabar, Jihar Leags ta tabbatar da samun mutum 1,022 da suka harbu da cutar korona, an sallami 225 daga cikinsu sannan 25 sun rasa rayukansu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Idan yanzu kuka shigo shafin namu, ga abubuwan da suka faru zuwa yanzu

    Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    • Saudiyya ta bayar da rahoton karin mutum 1,362 da suka harbu da cutar korona cikin sa'a 24 da suka gabata, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar kasar. JaridarSaudi Gazetteta ruwaito ma'aikatar lafiyar na cewa an samu karin mutum bakwai da suka mutu da kuma 210 da suka warke.
    • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya sassauta dokar hana fita da Shugaba Muhammadu Buhari ya saka ta tsawon kwana 14. Yanzu mazauna birnin Kano za su iya fita a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.
    • Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce wasu mutum 14 daga cikin almajiran da aka mayar jihar daga Kano sun harbu da cutar korona, abin da ya kawo jumillar mutun 41 da suka kamu a jihar. An samu karin mutum daya da ya rasu, a cewar wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mai bai wa Gwamna Nasir Elrufa'i shawara kan harkokin yada labarai, ya fitar ranar Asabar
    • Mutum na biyu da ya kamu da cutar korona a jihar Kebbi ya rasu a gidansa bayan ya gudu daga cibiyar killace masu cutar. Kwamishinan lafiya na jihar, Alhaji Jaafaru Muhammed ne ya bayyana haka inda ya ce mutumin mai shekaru 60, yana fama da ciwon sukari da hawan jini
    • Amurka na da mafi yawa sosai na wadanda suka rasu sakamakon cutar korona a duniya, duk da cewa ta fi wasu da yawa yawan jama'a idan aka kwatanta da na Turai da suka samu dubban alkaluman masu mutuwa. Jumillar adadin yanzu ya zarta 65,000 da kuma fiye da mutum miliyan 1.1 da aka tabbatar sun harbu da cutar
    • Duk da sassauta dokokin kulle da Shugaba Buhari na Najeriya ya yi daga ranar Litinin mai zuwa, hukumar babban birnin kasar, Abuja (FCTA) ta umarci ma'aikatan da ke zaune a wajen birnin da kada su koma. Ministan Abuja Mallam Muhammad Bello ya ce za a aiwatar da matakin sassauta dokar ne sannu-sannu
    • Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya ce ma'aikatan da ke zaune a jiharsa amma suke aiki a jihar Legas, basu da izinin fita daga cikin jihar domin zuwa Legas. Ya bayyana cewa duk da za a sassauta dokar kulle ga ma'aikata a mako mai zuwa, gwamnatinsa ba za ta bar ma'aikata su dinga shige da fice ba zuwa wasu jihohin.
    • Firai Ministan Spaniya Pedro Sanchez ya ce daga ranar Litinin mai zuwa dole ne duk wanda zai hau motocin sufuri na al'umma ya saka takunkumin rufe fuska. Wannan na zuwa yayin da aka fara sassauta dokar kulle a kasar. Wakilin BBC ya ce ''kafin yanzu gwamnati shawara take bayarwa da a rika rufe fuska, to amma daga ranar Litinin ya zama umurni.''
    • Faransa na shirin tsawaita dokar ta-baci kan lafiya da ta fara aiki a watan Maris saboda cutar Korona. Za a tsawaita dokar ne na tsawon watanni biyu . Amma duk da haka gwamnatin Shugaba Emmanuel Macron na shirin fara sassauta dokar kulle daga ranar 11 ga watan Mayu. Faransa na daya daga cikin kasashen da cutar Korona ta yi barna sosai, inda mutun 25,000 suka mutu.
    • Gwamnan jahar Ta'iz da ke Yemen ya bayyana rufe iyakokin yankin na tsawon sati biyu yayin da ake ci gaba da samun rahotannin bullar cutar Korona a kasar. Ta'iz ce jaha ta uku mafi girma a Yemen din da yaki ya daidaita kuma a yanzu gwamnatin jahar ta sanar da rufe masallatai da kasuwanni. Wakilin BBC yace ''idan aka kwatanta irin yadda annobar Korona ke barna a sauran kasashen duniya, za a iya cewa Yemen na da dan sauki kawo yanzu.
    • Fursunoni a gidan yarin Manaus da ke Brazil sun yi garkuwa da jami'ai biyar da ke tsare da su a gidan yarin. Al'amarin na zuwa a daidai lokacin da wasu fursunonin suka gudu daga gidan yarin da safiyar yau. A yanzu jami'an tsaro na ci gaba da tattunawar sulhu da su, amma 'yan gidan yarin na bukatar a shigo da masu rajin kare hakkin dan Adam da kuma 'yan jarida a tattaunawar.
  4. Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Rano

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnatin JIhar Kano da Masarautar Rano da Majalisar Sarakunan Kano bisa rasuwar Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Il.

    Mai magana da yawun Masarautar Rano, Wali Ado ya ce Sarkin ya yi jinyar kwana biyar ne, inda aka kai shi asibiti ranar Juma'a.

    Sanarwar da Garba Shehu mai magana da yawun Shugaba Buhari ya fitar ta ce "abin takaici ne yadda mai martaba ya rasu a lokacin da gwamnati ke dogara kan sarakunan gargajiya domin wayar da kan al'umma game da yadda za su tsira da rayuwarsu".

    Buhari ya yi addu'ar Allah Ya ji kansa, Ya yafe masa kura-kuransa, sannan ya shawarci iyalansa da masarauta da su rika tunawa da shi da ayyukansa na gari da ya aiwatar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Kaduna ta sake gano masu korona 14 cikin almajiran Kano

    Nasir Elrufai

    Asalin hoton, KDSG

    Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce wasu mutum 14 daga cikin almajiran da aka mayar jihar daga Kano sun harbu da cutar korona, abin da ya kawo jumillar mutun 41 da suka kamu a jihar.

    Kazalika an samu karin mutum daya da ya rasu, a cewar wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mai bai wa Gwamna Nasir Elrufa'i shawara kan harkokin yada labarai, ya fitar ranar Asabar.

    Har wa yau, kwamishin lafiya ta Kaduna ta ce akwai yiwuwar adadin ya zarta haka domin kuwa suna jiran karin sakamako na wasu mutanen da aka yi wa gwajin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. NCDC na wayar da kan jama'ar Kano kan matakan kare kai

    Kano

    Asalin hoton, NCDC

    Tawagar kai dauki ta hukumar NCDC mai dakile yaduwar cutuka a Najeriya ta fara shiga lungu da sakon Jihar Kano domin wayar da kan mazauna jihar kan matakan da ya kamata su dauka na kare kansu daga cutar korona.

    "Muna ziyartar unguwanni ne domin tabbatar da cewa mutane sun san yadda za su kare kansu sannan kuma mu zakulo wadanda suka kamu da cutar da ba lallai a san suna da ita ba," a cewar daya daga cikin ma'aikatan mai suna Arhyel Malgwi.

    Dazun nan Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya sassauta dokar hana fitar da Shugaba Buhari ya kakaba wa Kano ta mako biyu, wadda ta fara aiki ranar Talata da zummar rage yaduwar cutar korona a jihar.

    Yanzu mazauna Kano za su iya fita harkokinsu a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma domin sayayyar kayan abinci, a cewar gwamnantin jihar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Mai cutar Korona a Kebbi ya rasu bayan ya tsere daga cibiyar killance mutane

    Kebbi State

    Asalin hoton, KBSG Twitter

    Mutum na biyu da ya kamu da cutar korona a jihar Kebbi ya rasu a gidansa bayan ya gudu daga cibiyar killace masu cutar.

    Kwamishinan lafiya na jihar, Alhaji Jaafaru Muhammed ne ya bayyana haka inda ya ce mutumin mai shekaru 60, yana fama da ciwon sukari da hawan jini.

    Jami’in gwamnatin ya ce a ranar 26 ga watan Afrilu margayin ya fice daga cibiyar kula da masu cutar korona.

    Kwamishinan ya ce an gano mutum 12 da margayin yayi hudda da su kuma za a yi musu gwajin cutar ta covid 19.

    A cewarsa suna tukuru domin ganin cutar ta korona bata yadu ba a jihar ta Kebbi.

  8. Ganduje ya sassauta dokar hana fita a Kano

    Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya sassauta dokar hana fita da Shugaba Muhammadu Buhari ya saka ta tsawon kwana 14.

    Yanzu mazauna birnin Kano za su iya fita a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.

  9. Wadanda suka mutu a Amurka sun haura 65,000

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka na da mafi yawa sosai na wadanda suka rasu sakamakon cutar korona a duniya, duk da cewa ta fi wasu da yawa yawan jama'a idan aka kwatanta da na Turai da suka samu dubban alkaluman masu mutuwa.

    Jumillar adadin yanzu ya zarta 65,000 da kuma fiye da mutum miliyan 1.1 da aka tabbatar sun harbu da cutar.

  10. Ma'aikatan Abuja da ke jihohi kada su dawo aiki – FCTA

    Ministocin Abuja

    Asalin hoton, FCTA

    Duk da sassauta dokokin kulle da Shugaba Buhari na Najeriya ya yi daga ranar Litinin mai zuwa, hukumar babban birnin kasar, Abuja (FCTA) ta umarci ma'aikatan da ke zaune a wajen birnin da kada su koma.

    Wannan umarni yana kunshe ne a wata sanarwa da Ministan Abuja Mallam Muhammad Bello ya fitar ranar Asabar, inda ya ce za a aiwatar da matakin sassauta dokar ne sannu-sannu.

    "Kazalika, ma'aikatan da ke zaune a wajen birnin Abuja su ci gaba da zama a garuruwan da suke har sai an dage dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi," in ji wani bangare na sanarwar.

    Sanarwar ta kara da cewa dukkanin taruka haramun ne a birnin da suka hada da na biki da addini.

    Har wa yau, wuraren taruwar jama'a kamar gidajen kallo da sinima da wasanni da shakatawa da na shan barasa, baki daya za su ci gaba da kasancewa a rufe.

    Game da sufuri kuwa, an haramta yin acaba ko okada a fadin Abuja, sannan 'yan tasi mutum uku kacal za su dauka bayan direba, yayin da 'yan adaidaita sahu za su dauki mutum biyu ban da direba. Su ma motocin bas za su dauki kashi 50% ne kawai na abin da ya kamata motar ta dauka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Masu aiki a Legas mazauna jihar Ogun sun shiga tasku

    Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya ce ma'aikatan da ke zaune a jiharsa amma suke aiki a jihar Legas, basu da izinin fita daga cikin jihar domin zuwa Legas.

    Ya bayyana cewa duk da za a sassauta dokar kulle ga ma'aikata a mako mai zuwa, gwamnatinsa ba za ta bar ma'aikata su dinga shige da fice ba zuwa wasu jihohin.

    Gwamnan ya bada wannan sanarwarce a wani jawabi da aka watsa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar.

    Shugaba Buhari ya sanar da sassauci kan dokar kulle a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja daga ranar Litinin.

    Ana sa ran ranar 4 ga watan Mayu manyan ma'aikata za su koma aiki bisa tsarin da shugaba Buhari ya fitar.

  12. Korona ta halaka ƙarin mutum bakwai a Saudiyya

    Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Saudiyya ta bayar da rahoton karin mutum 1,362 da suka harbu da cutar krona cikin sa'a 24 da suka gabata, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar kasar.

    Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito ma'aikatar lafiyar na cewa an samu karin mutum bakwai da suka mutu da kuma 210 da suka warke.

    Birnin Madina ne kan gaba a yawan sabbin wadanda suka kamun na ranar Asabar, inda aka samu 249, sai Jaddah da ke biye masa da mutum 244 da kuma Riyadh mai 161.

    Jumillar wadanda suka harbu da cutar korona a Saudiyya sun kai 25,459, sai kuma wadanda suka mutu 176. Kazalika 3,765 sun warke.

  13. Faransa za ta tsawaita dokar ta-baci

    Eiffel Tower

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Faransa ta sanar da cewa za ta tsawaita dokar ta-baci har zuwa 24 ga watan Yuli.

    Ministan Lafiya Olivier Véran ya ce za a gabatar wa da majalisa kudirin ranar Litinin.

    Ya ce dage dokar ta-bacin, wadda ta fara ranar 24 ga watan Maris, ya yi wuri kuma za a iya shiga hadarin samun karin mutanen da ke harbuwa.

    Faransa na da wadanda suka kamu da cutar krona 167,000 da kuma 24,628 da suka mutu.

  14. Korona ta fi kashe mutane a Najeriya a yammacin Afirka

    Issoufou Mahamadou

    Asalin hoton, @PresidenceNiger

    Da alama Najeriya ba a tattalin arziki kawai take jagoranci ba a tsakanin mambobin kungiyar tattalin arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS), ita ce jagora a yawan wadanda suka mutu da wadanda suka harbu da cutar korona cikin kasashe 15 ya zuwa ranar Juma'a.

    A cewar wasu alkaluma daga Hukumar Lafiya ta kungiyar mai suna WAHO, mutum 2170 ne suka harbu da cutar a kasar, yayin da 68 suka mutu, sai kuma 351 da suka warke.

    Sai kuma Burkina Faso da ke bi mata, inda mutum 44 suka mutu, da kasar Nijar mai 33, da Mali mai 26.

    Sai dai, alkaluman sun nuna cewa adadin mutanen da suka warke daga cutar a kasar Ivory Coast sun fi na sauran takwarorinta yawa a yankin.

    Jumillar mutum 597 ne suka warke daga cikin 1333 da suka harbu da cutar ya zuwa ranar Juma'a 1 ga watan Mayu, a cewar hukumar .

    Kazalika mutum 15 ne suka mutu daga cikin wadanda suka kamun, abin da ya kawo wadanda ke dauke da cutar yanzu haka zuwa 721.

    Sai kuma kasar Nijar da take bi mata, inda mutum 478 suka warke, 33 suka mutu, sai kuma 217 da ke dauke da cutar a yanzu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Labarai da dumi-dumi, Boris Johnson ya raɗa wa ɗansa sunayen likitocin da suka duba shi

    Boris Johnson da budurwarsa Carrie Symonds sun raɗa wa jaririnsu sunan Wilfred Lawrie Nicholas Johnson.

    Sunayen na girmamawa ne ga kakaninsu da kuma likitoci biyu da suka kula da Mista Johnson lokacin da yana jinyar cutar korona a asibiti, kamar yadda Mis Symonds ta wallafa a shafin Instagram.

    Ta gode wa ma'aikatan asibitin jami'ar kwalejin Landon da suka kula da ita.

    Boris Johnson da budurwarsa Carrie Symonds

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Philippines ta saki fursunoni kusan 10,000

    Gidan yari a Philippines

    Asalin hoton, Getty Images

    Kusan fursunoni 10,000 aka saki a Philippines yayin da ƙasar ke yakin daƙile bazuwar cutar a cunkosun gidajen yari.

    Kotun ƙoli ce ta bayar da umurnin sakin fursunoni 9,731 musamman waɗanda ke jiran shari'a, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya ruwaito.

    Cutar korona ta yadu a cikin gidajen yarin Philippines musamman waɗanda suka fi cunkoso.

    An saki fursunonin ne saboda yadda kiyaye matakin nesa nesa da juna ya gagara a gidajen yarin da suka cika maƙil.

    Gidajen yarin da cutar ta yaɗu sun hada da na tsibirin Cebu inda mutum 348 suka kamu zuwa Juma'a. Da kuma gidan yarin Quezon City da ke Manila babban birnin ƙasar.

    Zuwa yanzu mutum kusan 9,000 suka kamu da cutar korona a Philippines, yayin da 603 suka mutu.

    Gidan yari a Philippines

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Fiye da mutum 40,000 suka kamu da korona a Afirka

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Tarayyar Afirka ta ce zuwa yanzu mutum 40.746 suka kamu da cutar korona a mambobin kungiyar 53.

    Cutar ta kuma kashe mutum 1,689, yayin da kuma mutum 13.383 suka warke daga cikin wadanda suka kamu.

    Alkalumman hukumar sun nuna cewa cutar ta fi yaɗuwa da kuma yin kisa a arewacin Afirka inda ta kama mutum 15,135, ta kuma kashe 1,057.

    Yankin yammacin Afirka ne na biyu inda cutar ta fi yaɗuwa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Jihar Oyo ta ce likitanta ya kamu da korona bayan ya dawo daga Kano

    Gwamnatin Oyo ta ce ta fara samun sakamakon gwaje-gwajen cutar korona da aka gudanar.

    Gwamnan jihar Seyi Makinde ya sanar a shafinsa na Twitter cewa mutum ɗaya daga cikin sakamako biyu da aka dawo da su, wani likita ne da ya dawo daga Kano yayin da ɗayan kuma ma'aikaci ne a hukumar tsaron farin kaya.

    Gwamnan ya ce har yanzu tna jiran sakamakon gwaji 300, daga cikin samfur 775 da aka ɗauka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Cutar korona ta ƙara kama wani ministan Rasha

    Cutar korona ta kama ministan ayyuka na Rasha Vladimir Yakushev, kwana guda bayan cutar ta kama Firaminista.

    Cutar ta kuma kama mataimakin ministan, kamar yadda kafofin yada labaran Rasha suka ruwaito.

    A ranar Alhamis ne Firaminista Mikhail Mishustin ya shaida wa shugaba Vladimir Putin cewa yana ɗauke da cutar.

    Yanzu shugaba Putin na tattaunawa kan tafiyar da harakokin gwamnati ta hanyar bidiyo.

    cikin sa'a 24, mutum 9,623 aka tabbatar da sun kamu da korona a Rasha, kuma fiye da rabinsu a Moscow.

    Cutar na kara yaɗuwa kusan a kullum, yayin da ta kashe mutum 1,222 a Rasha.

    Shugaba Putin sanye da kayan kariya lokacin da ya ziyarci asibiti

    Asalin hoton, AFP

  20. Mutum 43 sun kamu da Korona a gidan yarin Kinshasa

    Gidan Yari a birnin Kinshasa na Congo

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu mutum 43 da aka tabbatar da sun kamu da cutar korona a gidan yarin soji na N'dolo da ke birnin Kinshasa kasar Jamhuruiyyar Dimokudariyar Congo.

    Jami'an lafiya da hukumomin gidan yarin na kokarin daukar matakan dakile yaduwar cutar tsakanin sauran fursunonin da ke gidan yarin.

    Hukumomin sun ce suna tunanin kafa tanti a gidan yarin domin killace wadanda suka kamu tare da kuma rage cunkoso a gidan yarin.

    Tun 10 ga watan Maris, mutum 604 aka tabbatar da sun kamu da cutar a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo, kuma kashi 96 na yawan wadanda suka kamu suna birnin Kinshasa. cutar ta kashe mutum 32 a kasar, yayin da 75 suka warke.