Coronavirus: An kara samun mutum daya a Katsina

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Coronavirus: Amurka ta fi kowacce kasa yawan wadanda suka mutu

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka a yanzu ta zarta Italiya a yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon annobar coronavirus a duniya baki daya.

    Sabbin alkaluma daga Jami'ar Jons Hopkins sun nuna cewa sama da mutum 20,000 ne suka mutu a Amurkar.

    Wannan adadi maras dadin ji ya samu ne jim kadan bayan kasar ta bayyana samun fiye da mutum 2,000 da suka mutu a rana daya kacal - adadi mafi yawa kenan tun bayan barkewar cutar.

    Gwamnan Jihar New York, Andrew Cuomo ya fada a ranar Asabar cewa adadin ya daina karuwa daga yadda aka saba.

    New York ce jihar da cutar ta fi yin kamari a Amurka, inda fiye da mutum 180,000 suka kamu da ita daga cikin kusan 530,000 a kasar.

    Zuwa ranar Asabar, kowacce jiha a Amurka ta ayyana matakan yaki da annoba domin dakile yaduwar cutar.

  2. Mutum 404,878 sun warke daga coronavirus

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Alkaluman Jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka ta ce ya zuwa yanzu mutum 404,878 ne suka samu warkewa daga annobar coronavirus, wadda ke haddasa cutar Covid-19 a duniya baki daya.

    Kasar China ce kan gaba a yawan wadanda suka warke din, inda take da mutum 77,929.

    Ga jerin kasashe shida da ke kan gaba:

    China - 77,929

    Spain -59,109

    Jamus - 57,400

    Iran - 41,947

    Italiya - 32,534

    Amurka - 32,110

  3. Assalamu Alaikum

      • Marubuci, Umar Mikail

    Masu bibiyarmu barkanku da wannan safiya ta Lahadi daga Sashen Hausa na BBC.

    Wannan shafi zai rika kawo muku abin da ke wakana a Najeriya da makobtanta da ma sassan duniya musamman game da annobar cutar coronavirus, wadda ke haddasa Covid-19.

    Umar Mikail ne ke cewa ku biyo mu.