Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau
Rufewa
A nan za mu dakatar da kawo ma ku labarai da rahotanni kai-tsaye daga sassan duniya.
Da fatan za ku kasance da mu gobe inda za mu ci gaba da kawo maku labarai da rahotanni kai-tsaye musamman kan annobar cutar coronavirus daga sassan duniya.
Sai da safe.
Coronavirus: An kara samun mutum daya a Katsina
An sake samun mutum 5 da suka kamu da coronavirus a Najeriya kamar yadda hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar ta sanar a Twitter.
Alkalumman hukumar sun ce an kara samun mutum daya da ya kamu da cutar a jihar Katsina bayan mutum na farko da ya rasu a Daura. Yanzu mutum 5 alkalumman hukumar suka ce suna dauke da cutar a Katsina.
A Legas inda cutar ta fi kamari, an kara samun mutum biyu, da jihar Kwara mutum daya.
Yanzu jimillar mutum 323 suka kamu da cutar a Najeriya, yayin da 85 suka warke daga cikinsu. Adadin mutum 10 ne kuma cutar ta kashe.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Kwara na yaki da Covid 19 da kudaden da EFCC ta kwato
Hukumar EFCC da
ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce gwamnatin jihar Kwara ta yi
amfani da kudaden da ta kwato domin samar da cibiyoyin killace wadanda
suka kamu da cutar coronavirus.
Sanarwar da
kakakin EFCC Tony Orilade ya aikawa BBC, ta ce gwamnan jihar AbdulRaman AbdulRazaq ya bayyana cewa kudaden da hukumar ne ta
kwato da aka sace aka yi amfani aka samar da cibiyoyin.
EFCC ta ce ta mika wa gwamnatin Kwara N263,327,800
a watan Maris daga kudaden da ta kwato da aka sace a hukumar tara kudaden
shigar jihar.
Sanarwar ta ce, kudaden sun taimaka wa jihar
samar da kayayyakin da suka dace domin yaki da coronavirus da kuma farfado da cibiyoyin
lafiya.
Kwara na cikin jihohin da cutar coronavirus ta bulla, inda zuwa yanzu aka tabbatar da mutum biyu sun kamu.
Covid 19: Karin mutum biyar sun warke a Legas
Gwamnatin Legas ta ce an sallami karin
mutum biyar da suka warke daga cutar coronavirus
Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu
ya fadi a Twitter cewa mata hudu ne da namiji daya aka sallama.
Ya ce yanzu jimillar mutum 55 suka warke daga cutar a
jihar Legas daga cikin 177 da suka kamu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
An tilasta rufe hanci da baki a Nijar
Hukumomi a Nijar sun tilasta wa al’ummar kasar amfani da abin rufe baki
da hanci a fuska a matsayin kariya ga cutar coronavirus.
Tuni Majalisar dokokin Nijar ta amince da sanya dokar ta-baci
tsawon wata uku a fadin kasar.
Wakiliyar BBC a Yamai ta ce dokar rufe baki da hanci da ta shafi mutanen birnin Yamai inda cutar ta fi bazuwa, tun a ranar Asabar ta
fara aiki, yayin da kuma dokar ta-baci da majalisa ta amince za ta fara aiki
daga ranar Lahadi har zuwa 11 ga watan Yuli.
Kuma matakin rufe baki da hancin ya shafi direbobi ne a birnin, amma kuma an shawarci mutane su dinga saka wa a matsayin kariya.
Zuwa yanzu hukumomi sun ce akwai mutum 430 a Nijar da ke fama da cutar
coronavirus, a cikinsu hamsin sun warke, yayin da 11 kuma suka rasu.
Asalin hoton, Getty Images
An tsawaita dokar hana taruka a Ghana
Asalin hoton, @NAkufoAddo
Bayanan hoto, Mutum 408 ne aka tabbatar sun kamu da Covid-19 a Ghana
Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya tsawaita dokar hana taruka da aka saka ta wata daya a fadin kasar da karin mako biyu.
A wata sanarwa da babban jami'in hulda da jam'a a fadar shugaban kasa ya wallafa a shafinsa na Facbook, Eugene Arhin ya ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin 13 ga watan Afrilu.
"Shugaba Akufo-Addo ya bayar da umarnin tsawaita dokar hana taruka na tsawon mako biyu da za ta fara aiki daga ranar Litinin 13 ga watan Afrilu," in ji Eugene.
Ya kara da cewa ita ma dokar hana fita da aka saka a biranen Accra da Tema da Kumasi da Kasoa, an kara ta na tsawon mako daya kuma za ta fara aiki daga ranar Litinin.
Ya zuwa yanzu mutum 408 ne aka tabbatar sun kamu da Covid-19 a Ghana, takwas sun mutu sannan hudu sun warke daga cutar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a Instagram, 2
Covid 19: Ana iya daurin aure ta hanyar bidiyo a UAE
Hadaddiyar
Daular Larabawa ta bayar da damar daurin aure ba tare da an yi taro ba, a yayin
da kasar ke kokarin karfafa wa mutanen kasar nisantar juna a yakin da take yi da cutar
coronavirus.
An kaddamar
da wani tsari wanda zai ba malami damar daura wa ma’aurata aure ta hanyar
bidiyo ba tare da an yi taron daurin aure ba.
Kamfanin
dillacin labaran kasar ya ce an bullo da matakin ne domin taimakawa hukumomin
kasar sa ido ga harakokin aure.
'Mutum 5,000 aka yi wa gwajin coronavirus a Najeriya'
Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da Najeriya ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da coronavirus, har ya zuwa jiya Asabar mutum 5,000 aka yi wa gwajin cutar a kasar, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Tun a ranar 27 ga watan Fabrairu ne Najeriya ta tabbatar da bullar cutar a jikin wani dan kasar Italiya bayan ya isa Jihar Legas sannan kuma ya je Jihar Ogun.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton mutum 318 sun kamu da ita - 10 sun mutu 70 sun warke.
Kasar Afirka ta Kudu mai adadin mutum miliyan 57, ta yi wa mutum 73,000 gwajin cutar ta Covid-19.
Ministan lafiyar Afirka ta Kudu ya ce: "Wannan ya yi matukar kadan in aka kwatanta da hadarin cutar a Afirka ta Kudu." Ya ce suna fatan su rika gwada mutum 30,000 a kullum.
Najeriya wadda ta fi girman tattalin arziki a Afirka kuma mai yawan al'umma miliyan 190, mutum 5,000 ne kawai suka samu yin gwajin ya zuwa ranar Asabar.
"Gwajin nan jidali ne," in ji wani likita da ke aiki a wani asibiti mai zaman kansa a Jihar Legas da ya bukaci kada a ambaci sunansa. Ya kara da cewa: "Ba mu sani ba ma ko adadin daidai-wadaidaita yake."
Rashin kayan aikin gwajin kan sa wasu kasashe su yi hasashen adadin mutanen da ke kamuwa da cutar. Kasar Kenya ga misali, ta yi hasashen cewa nan da karshen watan Afrilu masu cutar za su kai 10,000 a kasarta.
Sai dai kwana 10 da shiga Afrilu, mutanen da suka kamu da cutar ba su wuce 200. Babban darakta a ma'aikatar lafiyar kasar ya fada a farkon watan nan cewa hakan ya faru ne saboda ba su yi wa mutanen gari gwajin ba.
Shugaban hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Africa Centres for Disease Control and Prevention ya fada wa AFP cewa sakamakon gwaje-gwajen cutar a Afirka "ba cikakke ba ne, ba mu da kayan aiki".
Yadda gwamman Legas ya yi bikin Easter a gida
Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya wallafa hotunan yadda ya
yi addu’oin Easter tare da iyalinsa a gida a Twitter.
Gwamman ya ce ya yi wa iyalinsa da Legas da Najeriya addu’a,
musamman a wannan yanayi mafi kalubale da ake ciki.
Mutum 177 suka kamu da cutar coronavirus a Legas, yayin da 50 suka warke, mutum 5 kuma suka mutu sanadiyar cutar a jihar da aka fara samun bullar coronavirus a Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Coronavirus ta kashe jumullar mutum 9,594 a Ingila
Ingila ta bayar da rahoton mutuwar 657 a rana guda, inda adadin ya kai 9,594 jumulla.
A yankin Scotland kuma, mutum 24 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon cutar ta Covid-19 a cikin awa 24 da suka gabata, wanda ya kawo jumullar adadin zuwa 566.
A yankin Wales ma hukumar lafiya ta ce marasa lafiya 18 sun mutu - jumullarsu 369.
A Northern Ireland, adadin ya karu zuwa 118, bayan samun rahoton mutuwar wasu 11 a ranar Lahadi.
Za a fara raba tallafin kayan abinci a Abuja
Asalin hoton, FCTA
A jiya Asabar, Karamar Ministar Abuja - babban birnin Najeriya - Hajiya Dr Ramatu Tijjani ta kai ziyara wurin ajiyar kayan tallafin da za a raba wa marasa karfi saboda rage radadin dokar hana fita da annobar coronavirus ta haifar.
A sakon da hukumar kula da birnin ta FCTA ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce daga kowanne lokaci za ta iya fara raba wa mutane kayan a sassan Abuja.
Zuwa yanzu birnin Abuja yana da wadanda suka kamu da cutar Covid-19 guda 56, inda aka sallami 11 sannan biyu suka mutu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, An sallami Firai Ministan Birtaniya daga asibiti
An sallami Firai Ministan Birtaniya daga asibiti bayan ya yi jinyar Covid-19 a dakin kulawar gaggawa a wani asibitin birnin Landan, a cewar fadar Downing Street.
An kwantar da Mista Johnson ne a asibitin St Thoma a ranar Lahadi da ta gabata.
Sai dai fira ministan ba zai koma ofis kai tsaye ba, zai ci gaba da murmurewa a gidansa na Chequers da ke Buckinghamshire, in ji Downing Street.
"Bisa shawarar da likitocinsa suka bayar, firai minista ba zai koma aiki nan kusa ba," wani mai magana da yawun fadar ya bayyana a wata sanarwa.
Sanarawar ta ce Mista Johnson ya gode wa ma'aikatan asibitin St Thomas "saboda kyakkyawar kulawar da suka ba shi", ya kuma kara da cewa sauran wadanda suka kamu da cutar ne suka tsaya masa a rai.
Wasu mutum 11 sun kamu da coronavirus a jihar Legas
Gwamnatin Jihar Legas ta tabbatar da samun wasu mutum 11 da suka harbu da cutar Covid-19 a ranar Asabar 11 ga watan Afrilu, abin da ya kawo jumullar adadin zuwa 177 a jihar.
Kwamishinan Lafiya Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana hakan a yau Lahadi, inda ya ce wasu mutum hudu kuma sun warke har ma an sallame su daga cibiyar killacewa - jumullar adadin ya kama 50.
Abayomi ya ce an sake samun wani mutum da ya mutu sakamakon cutar kuma yawan wadanda suka mutu a jihar sun zama shida kenan.
Hukumar NCDC ta ce ya zuwa karfe 9:30 na daren Asabar, mutum 318 ne suka harbu da coronavirus a Najeriya, 70 sun warke sannan 10 sun mutu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Karin mutum 1,000 sun mutu a Spaniya
Kasar Spaniya ta ce adadin wadanda suka mutu daga cutar coronavirus ya karu da fiye da mutum 1,000 a ranar Lahadi bayan kusan sati uku a jere adadin na kowacce rana yana yin kasa.
Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce 619 ne suka rasu ranar Lahadi, ba kamar Asabar ba, inda 510 suka mutu - kwana ukun da aka yi a jere na raguwar adadin ya zo karshe.
Baki dayan wadanda suka mutu a kasar sun karu zuwa 16,972 daga 16,353, a cewar ma'aikatar lafiyar.
Jumullar wadanda suka kamu kuma ya karu zuwa 166,019 daga 161,852.
Sakon Ista daga Shugaba Buhari zuwa ga Kiristocin Najeriya
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Bayanan hoto, Buhari ya nemi Kiristoci da su jaddada imaninsu kan Yesu, su dage da addu'a
"Ina jan hankalin Kiristoci da su jaddada imaninsu a kan Yesu, wanda ya kubuta daga zalunci, ya nuna juriya da jajircewa da kuma takawa," sakon Ista kenan daga Shugaba Buhari na Najeriya zuwa ga Kiristocin kasarsa.
Buhari ya taya Kiristocin murnar bikin Ista ne 'yan sa'o'i bayan ya tsawaita dokar hana zirga-zirga da aka saka a wasu jihohi ciki har da Abuja, sannan ya jaddada muhimmancin ba da tazara da wanke hannu a-kai-a-kai.
Kazalika shugabn ya ce yana sane sarai da halin da matakan hana yaduwar coronavirus suka jefa al'umma.
Sai dai ya ce: "Ganin cewa abu ne na ko a mutu ko a yi rai, zai yi kyau kowanne dan kasa ya yi wata sadaukarwa domin kare kasarmu daga bala'i...kuma na yi imani idan jama'a suka dage da addu'a da kuma aiki kasar nan za ta yi nasara."
Al'ummar Kirista a fadin duniya na bikin Ista a yau Lahadi, wanda ya zo a wani yanayi maras dadi, yayin da coronavirus ke ci gaba da daukar rayukan dubban mutane a kullum.
Bisa koyarwar addinin Kirista, ana yin bikin ne domin tunawa da tasowar Yesu Almasihu daga cikin matattu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Coronavirus 'matsala ce ta siyasa, ba ta lafiya ba'
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yuval Noah Harari ne marubicin littafin Sapiens: wanda ya yi magana kan takaitaccen tarihin dan Adam
"Zabin da muka yi na yaki da cutar Covid-19 zai sauya duniya nan da shekaru masu zuwa," in ji wani masanin tarihi dan kasar Isra'ila Yuval Noah Harari, marubucin littafin Sapiens: da ya yi magana kan takaitaccen tarihin dan Adam.
Wacce irin al'umma za mu zama lokacin wannan annoba? Ya kamata kasashe su zama tsintsiya madaurinki daya? Ko kuma kowa ya yi ta kansa? Tsare mutane da sanya ido kansu ne matakan da ya kamata a dauka kan 'yan kasa ko kuma kama-karya?
"Wannan rikicin ya sanya mu daukar tsauraran matakai kuma cikin gaggawa. Amma duk da haka muna da zabi," a cewar Harari.
Bayanan hoto, Coronavirus ta kashe mutum 52 a Saudiyya
Sarki Salman na Saudiyya ya bayar da umarnin tsawaita dokar hana fita a wasu sassan kasar har sai baba-ta-gani sakamakon ci gaba da samun masu dauke da cutar Covid-19 da ake yi a kasar.
Kamfanin dillancin labara na SPA ya ambato wani jami'in ma'aikatar harkokin cikin gida yana wannan batu a yau Lahadi, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Tun farko an kafa dokar ranar 23 ga watan Maris ta tswon kwana 21 a matsayin daya daga cikin matakan kariya daga yaduwar coronavirus.
Jami'in ya ce: "Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida na kira ga al'umma da su bi umarnin masarauta domin kare lafiyarsu, tare da jaddada duk wata dokar kariya da aka saka a wasu birane da unguwanni, inda aka hana zirga-zirga a wasu yankuna 13 a Saudiyya."
Ya zuwa yanzu, Saudiyya ta bayar da rahoton mutum 4,033 da aka tabbatar sun kamu da Covid-19, inda 52 suka mutu sannan 720 suka warke.
Coronavirus: An yanke wa dan sanda hannu a Indiya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, An sha kai wa 'yan sanda hari a sassan kasar a yunkurinsu na tilasta wa mutane bin dokar hana zirga-zirga
An yanke hannun wani dan sanda yayin da yake kokarin tabbatar da dokar hana fita a Jihar Punjab da ke arewacin Indiya.
Kazalika an raunata wasu abokan aikinsa biyu a harin.
Lamarin ya faru ne a unguwar Patiala a lokacin da wata mota ta afka kan wani wurin binciken ababen hawa. Matuka motar ne kuma suka fito suka fara kai wa 'yan sandan hari.
An kama akalla uku daga cikin maharan da aka ce 'yan wata kungiyar addini ne.
Shugaban 'yan sandan Punjab ya fada wa NDTV cewa bayan artabu na tsawon sa'a biyu miyagun sun "mika wuya dauke da wukake da takubba".
An sha kai wa 'yan sanda hari a wasu sassan kasar a yunkurinsu na tilasta wa mutane bin dokar hana zirga-zirga da aka saka domin dakile yaduwar annobar cutar Covid-19.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Bikin Ista ya tarar da bakon yanayi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Fasto Mark de Leon ya fara bikin Easter a kasar Philippines
Bikin Ista na bana ya ci karo da bakon yanayi, saboda haka shi ma bikin sai ya zama bako ga mabiya addinin Kirista.
Annobar coronavirus ta haramta wa Kiristoci haduwa da junansu domin yin bikin na tasowar Yesu Almasihu daga matattu, kamar yadda koyarwar addinin ta nuna.
Nan gaba a yau ne Fafaroma Francis zai yi jawabin ranar Ista daga dakin karatunsa maimakon gaban dandalin St Mark’s.
Tuni Fafaroman ya bukaci jama'a da kada su "mika kai ga tsoro" kan cutar coronavirus, inda ya bukaci su kasance "mazaunin rayuwa a lokacin mutuwa".
Jagoran na Cocin Roman Katolika na jawabi ne yayin gudanar da addu'o'in kwanan zaune na daren Ista a zauren Cocin St Peter's da kasance wayam.
Mabiya darikar katolika a fadin duniya - kimanin biliyan daya da miliyan 300 - na iya kallon jawabinsa na ranar Ista da za a nuna kai-tsaye ta intanet.