Coronavirus: 'Za mu killace duk wanda ya shigo Kaduna'

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail, Awwal Ahmad Janyau and Usman Minjibir

  1. Kungiyar Tarayyar Turai na tsaka mai wuya kan coronavirus

    Turai

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da samun rabuwar kai tsakanin kasashen Turai mambobin kungiyar Tarayyar Turai wato EU da kuma cibiyoyi a kan yadda ya kamata su bullowa annobar Covid-19, yayin da cutar ke ci gaba addabar duniya baki daya:

    • Bayan tattaunawar awa 16, ministocin kudin kasashen kungiyar sun fada a yau Laraba cewa har yanzu ba su cimma matsaya ba kan matakin za su dauka game da tattalin arzikinsu. Kasashen Jamus da Netherlands suna fargabar cewa za su bige da daukar nauyin bashin wasu kasashen, yayin da kasashen Italiya da Spain suka ce har yanzu akwai jan aiki
    • Babban jami'in lafiya na kungiyar ta EU ya ce ba shi da wani kwarin gwiwa a kan kungiyar game da matakan da take dauka kan annobar coronavirus
    • Wasu kotuna a kasar Jamus sun yi watsi da bukatar wasu 'yan darikar Katolika ta zuwa bikin Easter yayin da ake tsaka da dokar hana fita a kasar
    • Shi kuwa Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha caccaka ne bayan ya kai ziyara wani gari da cutar ta yi wa kamari, inda mutanen garin suka fito domin gaishe shi. Rahotanni sun bayyana cewa Macron ya yi ta rokon su da su bai wa juna tazara amma ko a jikinsu
  2. Mutum bakwai sun warke daga coronavirus a Abuja

    Ministan Abuja Muahhamed Bello

    Asalin hoton, FCTA

    Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Muhammaed Bello ya ce suna gab da sallamar mutum bakwai da suka yi jinyar Covid-19 a Abuja bayan gwaji ya nuna sun warke daga cutar.

    Ministan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai ranar Talata. Ya kara da gode wa mazauna birnin game da "hadin kan da suka bayar" wajen bin dokar hana fita da aka saka.

    A gefe guda kuma, Minista Muhammad Bello ya kai ziyarar gani da ido wata cibiyar killace masu coronavirus mai cin gado 500, wadda bankin Polaris Bank Plc ya sadaukar ga hukumar birnin.

    Cibiyar killace masu coronavirus a Abuja

    Asalin hoton, FCTA

    Ita ma FATE Philanthropy Coalition for Covid-19 - kungiya mai yaki da Covid-19 - ta bayar da tallafin irin wannan cibiya mai gado 50. Kazalika akwai asibitoci biyu da aka tanada domin kulawa da masu cutar da suke a Asokoro da kuma Karu.

    Har wa yau, sanarwar ta zayyana wasu lambobi da ta ce na kiran gaggawa ne domin bayar da rahoton wanda ake zargin ya kamu da cutar - 08099936312, 08099936313.

    Tun asali dai wadanda suka kamu da coronavirus a Abuja ana killace su ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Abuja da ke Gwagwalada.

    Zuwa yanzu, akwai mutum 50 da aka tabbatar sun kamu da Covid-19 a birnin na Abuja - adadi na biyu kenan mafi yawa bayan Jihar Legas.

    Jumullar wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun kai 254, a cewar hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka. Mutum 44 daga ciki sun warke, yayin da shida suka mutu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Covid-19 ta kashe fitaccen mawakin Somalia

    Ahmed Ismail Hussein Hudeydi, daya daga cikin mutanen da suka kafa masana'antar wakar zamani a Somalia, ya rasu a London yana da shekara 92 bayan ya yi fama da Covid-19.

    An fi saninsa da suna "Sarkin Oud" - wato wani abin kida da yake amfani da shi - Hudeydi ya shahara a "lokacin fafutukar kyamar mulkin mallakar tuwa" a Somalia, a cewar Hanna Ali,darakta a wata kungiar 'yan Somalia mazauna London.

    A wata sanarwa da ta fitar ta kara da cewa: "A takaice, wakokinsa tamkar wata hanya ce ta fafutukar yaki da mulkin mallaka da neman 'yancin kai."

    An hafe shi a garin Berbera da ke da tashoshin jiragen ruwa a 1928 amma ya girma a kasar Yemen ko da yake ya koma kasarsa yana matashi, a cewa Ms Ali.

    Ya koma zama a London a shekarun 1990 lokacin yakin basasar Somalia.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Matar shugaban kasa ta rera 'wakar coronavirus'

    Mai dakin shugaban kasar Ethiopia Zinash Tayachew ta fitar da sabuwar wakar coci inda ta nemi "jinkai daga Allah" a yadin da duniya ke fama da annobar coronavirus.

    Wakar bata yi bayani kai tsaye game da kwayar cutar ba, sai dai ta rera wasu baituka irin su "kada ka yi watsi da mu a wannan hali da munanan labarai suka addabi duniya".

    Ranar Talata aka fitar da wakar mai take Maren - wacce a harshen Amharic ke nufin "ka jikanmu".

    Tuni aka wallafa bidiyon wakar a YouTube inda 'yan kasar Ethiopia suke ta rarrabawa a shafukan sada zumunta. Bidiyon ya nuna mai dakin shugaban kasar a tsugune tana addu'ar neman "Allah kada ka juya wa mutanena baya".

    Ranar 12 ga watan Maris Ethiopia ta sanar da bullar coronavirus karon farko a kasar kuma tun daga waccan ranar zuwa yanzu an tabbatar da mutum 52 da suka kamu da ita, yayin da mutum biyu suka mutu.

    Ku latsa bidiyon da ke kasa don sauraren wakar mai dakin shugabam kasar:

    Kauce wa YouTube
    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba. Ana yi samun tallace-tallace YouTube

    Karshen labarin da aka sa a YouTube

  5. Mutum kusan miliyan daya da rabi sun kamu da coronavirus

    Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka da ke bin diddigin yaduwar annobar coronavirus, ta ce mutum 1, 431,900 ne suka kamu da cutar a fadin duniya zuwa safiyar ranar Laraba 8 ga watan Afrilu, 2020.

    Jami’ar ta kara da cewa cutar ta kashe mutum fiye da 82,000.

    Iran – 62,589

  6. Budewa

      • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake yi muku barka da wannan safiya. Da fatan za ku kasance tare da mu domin sanin halin da duniya ke ciki dangane da coronavirus, cutar da ta addabi kasashen duniya.

    Baya ga batun wanna cuta, za kuma mu kawo muku sauran labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman daga kasashen Najeriya da Nijar da ma sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.