Coronavirus: 'Za mu killace duk wanda ya shigo Kaduna'

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail, Awwal Ahmad Janyau and Usman Minjibir

  1. Rufewa

    To masu bibiyarmu nan muka kawo karshen wannan kawo muku bayanai kai tsaye a yau Laraba. Da fatan za ku kasance da mu a gobe Alhamis domin karin wasu bayanan kai tsaye daga Najeriya da sauran sassan duniya. Mun gode.

  2. Coronavirus: Boris Johnson na warwarewa

    Boris Johnson

    Asalin hoton, Getty Images

    Firai Ministan Birtaniya, Boris Johnson yana samun lafiya bayan shafe dare biyu a wurin kulawar gaggawa a asibiti, in ji Chancellor Rishi Sunak.

    Mista Sunak ya ce Boris Johnson na zaune a kan gado yana tattaunawa da malaman asibitin St Thomas Hospital da ke London.

    Mista Sunak ya kara da cewa za a yi wani taro gobe Alhamis inda za a tattauna kan matakin hana fita da kasar ke ciki.

    Wannan dai na zuwa a dai-dai lokacin da a kullum ake samun mutum 938 su mutu a asibitoci.

  3. Coronavirus: Ana tantama kan alkaluma daga China

    A ranar Talata ne dai kasar China ta yi ikrarin cewa ba ta samu mace-mace ba sanadiyyar cutar coronavirus a karon farko tun watan Janairu.

    To sai dai ba kowane ya gamsu da ikrarin Chinar ba saboda irin yadda China ta yi kaurin suna wajen fitar da alkaluma da suka hada da na tattalin arzikinta.

    Har wa yau, batun tantamar da ake yi na samun mutanen da aka tabbatar suna da cutar ta coronavirus.

    Daga watan Janairu har zuwa Maris, hukumar lafiya ta China ba ta ma'ana daban-daban har bakwai kan cutar coronavirus.

  4. Coronavirus: 'Za a killace duk wanda ya shigo Kaduna'

    Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Elrufa'i ya ce daga ranar Alhamis 9 ga watan Maris 2020, duk wanda aka kama ya ratsa ta jihar to za a dauki matakin ladambatarwa a kansa.

    Gwamnan wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya ce kasancewar sun yi dokar hana zirga-zirga a jihar, ya sa duk matafiyin da aka kama yana ratsa jihar to za a umarce shi ya koma inda ya fito ko kuma a killace shi har zuwa mako biyu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Hana fita ya sa mutane fita motsa jiki a Abuja

    Duk da mutane sun kiyaye dokar hana fita da gwamnatin Najeriya ta kafa a Abuja babban brinin Tarayya, amma wasu na fitowa domin motsa jiki.

    Sai dai kuma ba su kiyaye shawarar bayar da tazara ta akalla mita biyu ba tsakaninsu a yayin da suke motsa jiki.

    Shugaba muhammadu Buhari ne ya kafa dokar hana fita ta tsawon mako biyu a inda cutar ta fi yaduwa, Legas da Abuja da kuma Ogun mai makwabtaka da Legas.

    Yadda hana fita ya sa mutane motsa jiki a Abuja

    Asalin hoton, Getty Images

    Yadda hana fita ya sa mutane motsa jiki a Abuja

    Asalin hoton, Getty Images

    Yadda hana fita ya sa mutane motsa jiki a Abuja

    Asalin hoton, Getty Images

    Yadda hana fita ya sa mutane motsa jiki a Abuja

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Masu coronavirus a Ghana sun kai 313

    Kasar Ghana ta samu karin mutum 26 da suka kamu da cutar coronavirus, inda alkaluman masu cutar a kasar suka kai 313, inda mutum shida suka mutum.

    Dama dai gwamnatin Ghana ta sanar da cewa za a fuskanci karin alkaluman masu dauke da cutar sakamakon gwaji da ake ta yi wa jama'a.

    Shugaba Akufo-Addo ya ce a wannan makon za a tantance ko za a tsawaita dokar kulle bayan sakin jerin sunayen mutanen da aka yi wa gwaji fiye da 15,000.

  7. Coronavirus: Kungiyar Kwadago ta Duniya ta ce za a rasa miliyoyin ayyukan yi

    ILO

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Kwadago ta Duniya ta ce fiye da ma'aikata bilyan daya ka iya rasa ayyukansu ko kuma fuskantar rage albashi sakamakon dokar kulle da ta shafi tattalin arzikin duniya.

    Nan da watanni shida na shekarar 2020 ana tsammanin cewa yawan awowin da ake yi a wurin aiki za su ragu da kaso 6.7 wanda idan aka kimanta ya kai yawan aikin da mutum milyan 195 daga cikin masu aiki bilyan 3.3, ke yi.

    Kungiyar ta ILO ta kwatantan annobar coronavirus da "bala'in da yafi kowanne tun bayan yakin duniya na biyu."

    Gwamnatocin kasashen duniya sun bayar da umarnin rufe duk wasu sana'o'i da yin su ba dole ba ne tare da tsayar da wasu ayyukan da kuma umartar jama'a su zauna a gida.

    Annobar dai ta shafi ayyukan mutane kaso 38 na ma'aikata a suniya, in ji ILO.

  8. An tilasta amfani da abin rufe fuska a Delhi

    Hukumomi a Delhi babban birnin Indiya sun tilastawa mazauna birnin amfani da abin toshe baki da hanci a wuraren da ya kasance na taron jama’a saboda coronavirus.

    Tuni hukumomi a Mumbai suka dauki irin matakin, inda aka tilastawa kowa yin amfani da abin rufe fuska domin dakile bazuwar coronavirus.

    Sai dai Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce masu lafiya ba su bukatar sanya wani abun toshe baki da hanci.

    Yawan masu kamuwa da cutar a India sai karuwa suke a ‘yan kwanakin nan, inda aka tabbatar da mutum sama da dubu biyar sun kamu da cutar, yayin da kuma mutum dari da hamsin suka mutu.

  9. Putin ya kara wa likitocin Rasha albashi

    Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya sanar da karin albashi ga ma’aikatan lafiya tare da kara ware kudade ga aibitocin kasar.

    Putin wanda ya sanar da matakin a wata ganawa da jami’an gwamnatinsa ta bidiyo da aka watsa a kafar talabijin ya ce makwanni biyu ko uku masu zuwa za su kasance masu muhimmanci na yaki da cutar.

    Ya kuma bukaci jami’ansa su dauki matakai na taimakawa 'yan kasuwa. Shugaban ya bukaci ‘yan Rasha su kara hakuri kan matakan da aka dauka na hana fita, domin lokacin zai zo ya wuce.

    Shugaban Rasha Vladimir Putin

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Tawagar likitoci 15 ta sauka Abuja daga China

    Wata tawagar likitoci 15 daga China ta sauka a filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

    Jaridar ta ce wani jirgin kamfanin Air Peace ne ya sauka da tawagar likitocin.

    Jaridar ta kara da cewa tawagar wadda ta sauka da misalin karfe 5:15 agogon Najeriya ta samu tarbar ambasadan China a Najeriya, Dr Zhou Pingiian da baban darektan kamfanin gine-gine na kasar China na China Civil Engineering Construction Company, CCCECC da kuma wasu manyan jami'an ma'aikatun kasashen waje da na lafiya na Najeriya.

    Dama dai Najeriya ta ce za ta gayyaci likitocin daga China domin taimaka wa kasar wajen yaki da annobar coronavirus.

    Hakan ne ya sa kungiyar likitocin kasar ta nuna rashin amincewarta, inda ta fitar da sanarwa mai dauke da kakkausan martani ga gwamnatin kasar.

    Wata sanarwa da kungiyar likitocin Najeriyar ta fitar na cewa cin fuska ne, ba tare da tuntubarsu ba gwamnati ta gayyato takwarorinsu na kasar China.

    Suka ce gayyatar "wani abin damuwa ne da matukar ban takaici".

    Sanarwar wadda ta wallafa a shafinta na intanet ta ce abin kunya ne ga likitocin Najeriya da sauran ma'aikatan lafiya wadanda suke aiki tukuru wajen bayar da gudunmawa a yakin da kasar ke yi da annobar coronavirus, duk da mummunan yanayin aiki da tsarin kula da lafiya maras inganci amma gwamnati ta zagaye ba tare da tuntubar su ba.

  11. Shugabannin Afirka ba su yarda da batun Trump ba, sun goyi bayan WHO

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugabannin Afirka sun goyi bayan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da shugabanta Dr Tedros Adhanom bayan caccakar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi masa.

    Mista Trump ya fada a Twitter ranar Talata cewa WHO "yar korar China ce" duk da cewa "mafi yawan" kudin da take samu daga Amurka ne.

    Sannan ya yi gargadi cewa zai dakatar da tallafin da yake bai wa kungiyar.

    Gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar goyon bayan hukumar lafiyar, inda ta ce "tana yaba wa WHO da kuma shugabanta Dr Tedros Adhanom", dan kasar Habasha wato Ethiopia.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Tun farko Shugabar Kungiyar Hadin Kan Afirka ta AU, Moussa Faki Mahamat ta kare shugaban WHO, sannan kuma Shugaban Rwanda, Paul Kagame ya mara mata baya.

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  12. Labarai da dumi-dumi, An samu adadin mutuwa na rana guda mafi yawa a Birtaniya

    Mutanen da suka mutu sakamakon coronavirus a Birtaniya sun karu zuwa 7,097 bayan mutum 938 sun mutu a rana guda - adadin da ba a taba samun kamarsa ba.

    Sai dai kwararru sun yi gargadi da a rage bayar da rahoton wadanda suka mutu na rana guda saboda hakan ka iya bayyana tsagwaron wahalar da ke cikin aikin ne kawai sama da hakikanin sauyin da ake samu na adadin.

  13. Kano na ci gaba da shirin ko-ta-kwana kan coronavirus

    Wurin killace masu coronavirus a Kano

    Ana ci gaba da ginin cibiyar killace masu cutar coronavirus ta Alhaji Aliko Dangote tare da hadin gwiwar gwamntin Jihar Kano a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a kwaryar birnin Kano.

    Zuwa yanzu dai hukumomi ba su bayar da sanarwar bullar cutar ba a Jihar Kano amma ta bulla makobciyarta wato Kaduna, inda mutum biyar suka kamu.

    Wurin killace masu coronavirus a Kano

    Zuwa lokacin hada wannan rahoto mutum 254 ne suka harbu da cutar a Najeriya, a cewar hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa.

    Daga cikin wannan adadi, mutum 44 sun warke sannan shida sun rasa rayukansu.

  14. Mutane da dama sun mutu a Ingila cikin kwana daya

    Karin mutum 828 da suka harbu da cutar coronavirus sun mutu a Ingila a cikin awa 24 da suka wuce, kuma hakan ya sa jumullar adadin suka kai 6,483.

    A yankin Wales ma, mutum 33 ne suka mutu, inda jumullarsu suka kai 245.

    Dr Robin Howe na hukumar lafiyar Wales ya ce an samu karin mutum 284 da suka harbu da cutar, wanda baki dayan adadin ya zama 4,073 a yankin.

    Shi ma yankin Northern Ireland ya bayara da rahoton mutuwar mutum biyar - jumullarsu 78 ner a yankin.

  15. Coronavirus: Za a tuhumi masu karya doka da laifin kisa a Tunisia

    Yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da lakume rayuka a fadin duniya, kasar Tunusiya ta yi barazanar tsauraran hukunci kan duk wanda ya ki bin dokar da gwamnati ta saka.

    A ranar Talata ne ministan harkokin cikin gida ya yi gargadin cewa mutanen da suke yada cutar da "ganganci" za su fuskanci tuhumar hukuncin kisa ba da gangan ba.

    Wasu gwamnatoci ma sun sanar da daukar tsauraran matakan domin dakile annobar.

    A watan da ya gabata Rasha ta ce za a dinga yanke hukuncin shekara bakwai ga duk wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar wani sakamakon karya dokar hana fita.

    A kasar Singapore, duk mai dauke da cutar da aka kama da saba doka za a ci tararsa dala 10,000 - sama da naira miliyan uku - da kuma daurin wata shida, wadanda suka maimaita laifin kuma za su fuskanci hukuncin da ya fi haka.

  16. Gobara ta tashi a ofishin Babban Akanta na Najeriya

    Babban Akawu na Najeriya

    Asalin hoton, Federal Fire Service

    Gobara ta tashi a ofishin Babban Akanta na Najeriya wato Accountant General da ke Abuja da safiyar yau Laraba.

    Hukumar kashe Gobara ta kasa ta bayyana a shafinta na Twitter cewa ta kashe gobarar amma bata bayyana abin da ya haddasa faruwar hakan ba.

    Kazalika babu rahoton rasa rai ko kuma dukiya ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.

    Accountant General a Najeriya, shi ne mai kula da baitul malin kasar, wanda shugaban kasa ke nadawa bisa tanadin kundin tsarin mulki.

    Ahmed Idris shi ne mai rike da mukamin a yanzu, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a shekarar 2015.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    'Yan Najeriya da dama sun bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta - mafi yawansu na ganin ba gobarar Allah da Annabi ba ce.

    Wani ya ce ya bibiyi martanin abin da ya biyo bayan gobarar kuma abin da zai ce kawai shi ne; "yan Najeriya sun daina aminta da shugabanninsu".

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Wani ma ya ce "wannan shiri ne kawai domin kuwa gobe gwamnati za ta bayyana cewa wasu takardun bayanan kudi sun kone a gobarar".

    Kauce wa X, 3
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 3

  17. Abin da ya faru a fadin duniya zuwa yanzu

    Mutane

    Asalin hoton, Getty Images

    • Fiye da mutum biliyan daya ne a fadin duniya ke fuskantar barazanar rasa aikin yi ko kuma raguwar albashi sakamakon dokar hana fita, a cewar wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya. Ta ce kusan kashi 81 cikin 100 na ma'aikatan duniya ne dokar ta shafa
    • Mutane a birnin Wuhan na China - inda annobar coronavirus ta samo asali - sun fara fita daga cikin dokar zaman gida ta tsawon wata biyu. Masu lafiya a birnin za su iya ficewa daga garin yanzu
    • Fira Minsitan Indiya Narendra Modi da kuma manyan jami'an gwamnatinsa za su yafe kashi 30 cikin 100 na albashinsu saboda lahanin da coronavirus ta yi wa tattalin arzikin kasar. A gefe guda kuma, wasu jihohi suna kiran da a kara tsawon dokar zaman gida, wadda za ta kare a mako mai zuwa
    • To wannan fa abin kunya ne! Domin kuwa magajin gari ne a Jihar Illinois ta Amurka ya bayyana kunyar da ya sha. Ya tura 'yan sanda domin su tarwatsa wani taron jama'a da suka karya dokar bayar da tazara, kwatsam kuma sai ya tarar da matarsa a wata mashaya cikin jama'a

    Daga karshe, yayin da kwayoyin cutar coronavirus kan rayu na tsawon lokaci a wasu wurare kamar dandariyar kasa, kar ku manta da wanke inda hannu kan taba akai-akai a gidajenku - kamar makunnar lantarki da ta ruwa.

  18. Bayanai daga Nahiyar Latin Amurka kan coronavirus

    • Shugaban Venezuela, Nicolás Maduro ya yi umarni da a killace duk wadanda aka gano suna dauke da cutar coronavirus a asibiti. A wani jawabi da ya yi a daren Talata, Maduro ya ce kasarsa na da isassun gadaje sannan kuma ta dakile annobar. Venezuela ta dade tana fuskantar karancin abinci da magunguna
    • A Venezuela din dai, ma'aikatan lafiya sun fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun shafe sa'o'i a kan layin sayen man fetur, kuma hakan ya shafi kokarinsu na zuwa wurin aiki a kan lokaci.
    • An kori wani jami'n lafiya a kasar Mexico bayan an zarge shi da tofa wa wani ma'aikacin lafiya yawu tare da neman a ba shi kulawa ta musamman a wani asibiti da ke Jihar Oaxaca. Ana tuhumar Daniel López Regalado, wanda ya kamu da coronavirus, da laifin "saka rayuwar wasu cikin hadari".
  19. Covid-19: An dakatar da ministar da ta karya dokar hana zirga-zirga

    An dakatar da ministar sadarwa ta Afirka ta Kudu tsawon wata biyu – ba tare da biyanta albashi ba– saboda an kama ta da laifin karya dokar hana zirga-zirga ta hanyar fita cin abincin rana da abokinsa.

    Mutane suna ta magana a kan Stella Ndabeni-Abrahams bayan an ga wani hotonta tana cin abinci a waje tare da Mduduzi Manana, tsohon minista a wannan makon.

    Hoton ya nuna mutanen biyu suna zaune a tebir wanda mutum hudu ka iya zama suna cin abincin rana.

    Wanna ne mako na biyu tun da aka tilasta wa 'yan kasar ta Afirka ta Kudu zaman gida domin dakile yaduwar coronavirus, inda ake bari su fita kawai idan za su sayi kayan bukatar gaggawa, kamar abinci da magani.

    Shugaba Cyril Ramaphosa, wanda ya tattauna da ministar kan hoton, ya fitar da sanarwa inda ya ce bai "gamsu da dalilan da ta bayar na zuwa wurin cin abincin ba".

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Coronavirus ta kashe wani dan Birtaniya a Legas

    Wani dattijo mai shekara 66 dan kasar Birtaniya ya mutu sakamakon annobar coronavirus a Jihar Legas da ke kudancin Najeriya.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya ce mutumin ya je India ne sannan ya karasa Legas daga birnin Dubai a ranar 17 ga watan Maris.

    Kazalika kwamishinan ya ce an samu karin mutum 10 da suka kamu da cutar a jihar - jumulla 130 kenan - sannan kuma wani guda daya ya warke, wanda ya kawo jumullarsu 32.

    Zuwa yanzu hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya ta ce mutum 254 ne suka kamu da cutar sannan 44 sun warke, shida kuma sun mutu.