Bayanai kan coronavirus a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail, Usman Minjibir and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rahoton abin da ke faruwa a Turai

    • A Faransa, gwamnati na kokarin sanya wasu tsauraran matakan hana mutane yin tafiye-tafiyen bikin Easter ta hanyar duba kayayyaki a tashoshi da filin jirgi da kan tituna. Marasa lafiya sama da 400 ne aka sauya wa wurin jinya ta hanyar amfani da jirgin kasa mai dan karen sauri tun da ga ranar 18 ga watan Maris.
    • Adadin wadanda suka mutu a Jamus ya karu zuwa fiye da 1,000. Yanzu kasar tana da wadanda suka kamu da cutar sama da na China, a cewar wasu alkaluma daga Jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka.
    • A ranar Alhamis ne kasar Spain ta samu mutane ma fi yawa a karon farko da suka mutu a rana daya, inda 950 suka mutu. Mamata a Spain sun fi na ko'ina yawa ban da Italiya.
    • Shugabar Kungiyar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce za a fara tattaunawa kan ko za a bude iyakokin kasashen kungiyar zuwa nan da bikin Easter
    • A Girka, an ayyana wani sansanin 'yan ci-rani da kuma wani jirgin ruwa da ya tashi daga tashar Piraeus a matsayin inda aka fara samun bullar cutar coronavirus. Daga cikin 380 da ke cikin jirgin, 119 sun kamu da cutar, yayin da aka gano wasu 24 na dauke da cugtar a sansanin Ritsona da ke kusa da Athens, a cewar hukumomi
    • Shin man kade yana maganin COVID-19?

      Wasu na cewa shafa man kade a hannu da fuska ka iya kare mutum daga cutar coronavirus, wannan ba gaskiya ba ne.

      Mu ci gaba da yawaita wanke hannuwanmu. Idan mun je sayen kayan abinci, mu yi amfani da safar hannu wajen duba kayan, ka da mu taba da hannuwanmu.

      Bayanan bidiyo, Shin da gaske man Kade na maganin COVID-19?
    • Coronavirus ta bulla a Malawi

      Malawi ta tabbatar da samun mutum uku da suka kamu da coronavirus.

      Kasar da ke kudancin Afirka na cikin kasashe kalilan a nahiyar wadanda a baya ba su da mutane da ke dauke da cutar. Sauran kasashe su ne Lesotho, Comoros, Sudan ta Kudu da São Tomé and Príncipe.

      Shugaba Peter Mutharika ne ya bayyana bullar cutar a jawabin da ya yi wa 'yan kasar ta talbijin ranar Alhamis inda daga bisani gwamnatin kasar ta wallafa shi a shafinta na Twitter:

      An bayyana bullar cutar ne a yayin da kasar ke shirin gudanar da zabe a watan Yuli

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, An bayyana bullar cutar ne a yayin da kasar ke shirin gudanar da zabe a watan Yuli
      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Coronavirus: Halin da dan Atiku Abubakar yake ciki

      Mohammed Atiku, dan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce yana samun sauki tun bayan da aka killace shi sakamakon kamuwa da coronavirus.

      A wani sakon bidiyo da mahaifinsa ya wallafa a Twitter, ya ce ko da yake lokacin da aka kai shi cibiyar killace masu dauke da cutar da ke Gwagwalada a Abuja, babban birnin kasar ya fada cikin fargaba da tashin hankali, amma babu abin da ya fi bata masa rai fiye da labaran karya da ake yadawa kan irin su da ke dauke da coronavirus.

      A cewarsa, an fi watsa irin wadannan labarai kan irin sa da suka fito daga gidajen 'yan siyasa.

      Ya ce yana sa ran kammala wa'adinsa na zaman wurin killace masu dauke da cutar, yana mai cewa "yau ina kwana na 11 zuwa 12, ina fatan barin wurin nan ba da dadewa ba, watakila idan sakamakon gwaje-gwajen da za a yi min suka kasance masu armashi."

      Ya jinjina wa ma'aikatan lafiya da ke kula da masu cutar, amma ya bukaci jama'a su ci gaba da daukar matakan kare kansu daga kamuwa da cutar.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Covid-19: Mutum 561 sun warke a kasashen Tarayyar Afirka

      Ya zuwa safiyar Juma'a, 4 ga watan Afrilu, mutum 561 ne suka warke daga coronavirus a kasashe 50 na kungiyar tarayyar Afirka, a cewar hukumar yaki da cutuka ta nahiyar, wato Africa CDC.

      A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Juma'a, Africa CDC, ta kara da cewa mutum 7,028 ne suka kamu da cutar a kasashen, yayin da mutum 284 suka riga mu gidan-gaskiya.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Coronavirus ta kashe sama da mutum 53,000

      Alkaluma kan yaduwar coornavirus a duniya sun nuna cewa ya zuwa Juma’a da safe, cutar ta hallaka sama da mutum 53,000 a fadin duniya.

      Bayanai daga Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, wacce ke bin diddigin yaduwar cutar, sun nuna cewa fiye da mutum miliyan daya ne suka kamu da coronavirus, yayin da sama da mutum 211,000 suka warke ya zuwa safiyar ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, 2020.

      Kasashe goman da suka fi fama da annobar su ne:

      Amurka – 245,573

      Italiya – 115,242

      Spaniya – 112,065

      Jamus - 84,794

      China - 82,464

      Faransa - 59,929

      Iran - 50,468

      Birtaniya - 34,173

      Switzerland – 18,827

      Turkiyya - 18,135

    • Barkanmu da wannan lokaci

        • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
        • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

      Daga nan Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da wannan safiya. Da fatan za ku ksance tare da mu domin sanin halin da duniya ke ciki dangane da coronavirus, cutar da ta addabi kasashen duniya.

      Za kuma mu kawo muku sauran labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman daga kasashen Najeriya da Nijar da ma sassan duniya.

      Kuna iya tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.