Rufewa
Masu bibiyarmu duka-duka a nan muka kawo karshen wannan shiri da ke kawo muku bayanai kai tsaye dangane da cutar coronavirus. Sai da safe.
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.
Nasidi Adamu Yahaya, Umar Mikail, Usman Minjibir and Awwal Ahmad Janyau
Masu bibiyarmu duka-duka a nan muka kawo karshen wannan shiri da ke kawo muku bayanai kai tsaye dangane da cutar coronavirus. Sai da safe.
Kamfanin Google ya wallafa rahotonsa da ya kunshi bayanan biliyoyin mutanen da ke amfani da wayoyin salula a yayin da gwamnatoci ke daukar matakan takaita wa mutane fita domin dakile bazuwar coronavirus.
Google ya bibiyi mutanen da suka bayar da dama a gano inda suke kuma Google ya gano wadanda suka je kamar tashar jirgin kasa da kantina a kasashe sama da 130 tsawon mako biyar har zuwa karshen Maris.
Google ya ce ya fitar da rahoton ne domin taimakawa jami’an lafiya tabbatar da ko mutane na kiyaye dokar hana fita.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya yi gargadi ga kasashen da ke fama da coronavirus kan gaggawar dage dokar hana fita da suka kafa.
Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa taron manema labarai a Geneva cewa, duk da matakan suna illa ga tattalin arziki, amma sassauta su zai fi yin illa.
Ya ce dole kasashe su ci gaba da daukar matakai, musamman wadanda suka shafi ganowa da gwaji da killacewa da kuma kula da lafiyar wadanda suka kamu tare da gano wadanda suka yi mu’amula da su.
WHO ta ce sama da mutum miliyan daya ke dauke da coronavirus a duniya, inda sama da 50,000 suka mutu
Ya ce dole ne kasashe su ci gaba da bin matakan tsuke bakin aljihu, wadanda suka danganci gano, gwaji, ware da kuma magance kowace kara

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, @Chikwe_I
Gwamnatin Najeriya ta ce babban kalubale da take fuskanta a yaki da coronavirus shi ne, matsalar kwararru, kamar yadda shugaban hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya Chikwe Ihekweazu ya bayyana.
Chikwe Ihekweazu wanda mamba ne a kwamitin shugaban kasa na musamman kan yaki da coronavirus a Najeriya, ya bayyana haka ne a ranar Juma'a a wani taron manema labarai.
Ya ce: "Babban kalubalenmu ba kudi ba ne kawai da kuma kayan aiki; rashin kwararru ne babbar matsalarmu, ma'aikata wadanda suke da kwarewa wurin gano cutuka. Babu yadda za a yi ka horar da mutane a lokaci guda."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Ya kara da cewa wajibi ne "a rika yin gwajin cutar cikin sauri ba tare an kauce wa ka'idojin aikin ba," sannan ya ce "kamar yadda saurin yake da amfani haka ma ingancinsa yake da muhimmanci".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Chikwe Ihekweazu ya ce yanzu haka sun bude sabon dakin gwajin cutar na uku a Jihar Legas sannan kuma suna shirin bude wani a Abuja, sai kuma Jihar Kano.
A nasa bangaren, Boss Mustapha wanda shi ne sakataren gwamnati kuma shugaban kwamitin, ya ce lallai ne kwamitin ya yi kira ga jami'an tsaro da su yi kaffa-kaffa wurin tabbatar da an bi dokar hana fita da gwamnati ta saka.
Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su zama masu da'a ta hanyar bin dokokin da aka sanya saboda a cewarsa, "babu wani dan Najeriya da ya kamata ya shiga damuwa ko matsi a wannan lokaci".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Dan jarida mai sa ido kan coronavirus, Abdulbaki Jari ya yi duba kan wannan tambaya.

Asalin hoton, Getty Images
Ana zargin wasu likitoci guda biyu 'yan kasar Faransa da nuna wariyar launin fata bayan sun nemi da a yi gwajin rigakafin cutar coronavirus a kan 'yan Afirka.
Jean-Paul Mira da Camille Locht dukkanninsu sun fadi hakan ne a gidan talbijin na Faransa cewa akwai wanda aka yi gwajin a kansa - da ake amfani wajen rigakafin cutar tarin fuka a Afirka.
Wasu fitattun mutane 'yan Afirka kamar dan wasna kwallon kafa, Didier Drogba sun ce bai kamata a mayar da 'yan Afirka zakarun gwajin dafi ba.
To sai dai cibiyar da Dr Locht ke aiki, ta ce ba a fahimci likitocin ba ne kasancewar za a gudanar da irin wannan gwajin rigakafin a wasu kasashen Turai.

Asalin hoton, Getty Images
Kasar Saudiyya na da wadanda suka kamu da coronavirus 1,885, wadanda suka mutu 21 da kuma wadanda suka warke 328.
Ga matakan da take dauka domin dakile cutar:
Hukumomi a Tunisia sun sanya wani dan sanda na mutumin-mutumi ya rika kewayawa cikin Tunis, babban birnin kasar domin ganin yadda jama'a ke bin umarnin zama a gidajensu don hana kamuwa da coronavirus.
Idan dan sandan ya ga mutum yana tafiya a waje, zai je inda yake ya tambaye shi abin da ya sa ya fito waje bayan kuma ya san an hana fitowa.
Dole ne mutum ya nuna wa dan sandan mutum-mutumin katin shaida, wato ID card da sauran takardu, sannan 'yan sandan da ke kula da shi za su dauki bayanansa.
Wannan ne mako na biyu tun da aka rufe kasar da zummar hana yaduwar coronavirus, wacce ta yi ajalin mutum 14 a Tunisia.

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, PA Media
Sarauniya 'Yazzabil ta Ingila za ta yi wa 'yan kasar jawabi ranar Lahadi dangane dabatun annobar coronavirus, a karo na hudu na irin wannan jawabi kan annoba a tsawon shekarunta 68 tana jagorantar masarautar kasar.
Fadar Buckingham ta ce za a watsa bayanin sarauniyar ne wanda aka nada a gidan sarautar Winsor Castle ta gidajen talbijin na kasar.
Sarauniya dai kan yi jawabin da ake nada a lokutan bukukuwan kirsimeti.
Ma'iakatar lafiyar Birtaniya ta ce ya zuwa karfe 5:00 na yammacin Alhamis, jumullar mutum 3,605 ne suka mutu sakamakon cornavirus, daga mutum 38,168 da suka kamu da cutar.
A yankin Scotland kuwa mutum 46 ne suka mutu, inda a Wales mutum 24 suka rasu sannan yankin Northern Ireland na da mutum 12.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce sun sallami mutum 4 bayan sake yi musu gwajin da ya nuna sun warke daga cutar coronavirus.
A shafinsa na Twitter, Sanwo-Olu ya ce uku daga cikin wadanda aka sallamar mata ne inda guda daya namiji ne.
Gwamnan ya ce hakan ya kara ba su kyakkyawan fatan cewa za a kawo karshen annobar coronavirus.
Duk da cewa hukumar NCDC mai kula da hana yaduwar cututtuka ba ta sanar ba, jumullar wadanda suka warke daga annobar cornavirus a Najeriya sun zama 24.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sabuwar asibitin Birtaniya mafi girma da aka gina cikin kwana tara domin majinyatan coronavirus ta fara aiki.
An sauya ExCeL exhibition centre katafaren wurin da ake taruka da bukukuwa ne a gabashin London zuwa asibitin coronavirus.
Asibitin na da girman da ke kunshe da gadajen majinyata 4,000.
Cikin kwana tara aka sauya katafaren babban dakin taron mai girman kafa 87,328 zuwa asibiti da ke da bangarori sama da 80, kowanne dauke da gado 42.
Akwai kuma gadaje kusan 500 na zamani da ke dauke da na'urorin taimakawa majinyaci shakar iska da ake kira ventilators. Akwai kuma wani bangare da ke da wasu gadajen 3,500.
Idan har aka kammala, za ta kasance daya daga cikin manyan asibitoci a duniya.

Rundunar sojin Rwanda ta ce ta kama jami'anta biyar bayan wasu mazauna yankunan marasa galihu da ke babban birnin kasar Kigali sun zarge su da yi wa mata fyade a yayin da suke tilasta wa mutane bin dokar hana fita domin hana yaduwar Covid-19.
Mazauna Nyarutarama sun shaida wa masu shigar da kara na rundunar sojin cewa sojojin sun kuma yi wa maza duka sannan suka sace musu kayayyaki, a cewar wakilin BBC da ke Kigali.
Daya daga cikin matan ta shaida wa 'yan jarida cewa ranar 26 ga watan Maris wani soja ya kutsa kai cikin dakinta inda ya lakada wa mijinta duka, sannan ya yi mata fyade lokacin da ta yi yunkurin hana shi dukan mijin nata.
Gwamantin kasar ta sanya dokar hana fita domin dakile yaduwar Covid-19, amma mazauna birnin sun yi korafin cewa jami'a tsaro suna gallaza musu.
A makon jiya, an harbe mutum biyu har lahira bayan an kama su a wajen gidajensu.
'Yan sanda sun ce mutanen biyu sun yi yunkurin kai wa jami'an tsaro hari.
Rwanda ta tabbatar da cewa mutum 84 sun kamu da cutar Covid-19.

Asalin hoton, Dr. Ramatu Tijjani
Hukumomi a birnin Abuja na Najeriya na ci gaba da ayyukan tsaftace birnin saboda coronavirus.
A jiya Alhamis ne Karamar Ministar Abuja, Dr Ramatu Tijjani Aliyu ta jagoranci aikin feshi a kan gadar Major Flyover da ke kan titin Kubwa da kuma Kasuwar Kubwa.
Abuja ce ta biyu a yawan masu Covid-19 da mutum 38.
Jihar Legas ce ta fi kowacce jiha yawan masu cutar, inda mutum 98 suka kamu.
Zuwa yanzu mutum 190 ne suka kamu a Najeriya, biyu sun mutu, 20 sun warke.
Jihohi masu coronavirus:
Legas - 98
Abuja - 38
Osun - 20
Oyo - 8
Akwa Ibom - 5
Ogun - 4
Edo - 4
Kaduna - 4
Bauchi - 3
Enugu - 2
Ekiti - 2
Rivers -1
Benue - 1
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Taurarin kwallon kafar Afirka, Didier Drodga da Samuel Eto'o sun yi Allah-wadai da maganar wasu daktocin Faransa biyu cewa ya kamata a fara yin gwajin cutar Covid-19 a Nahiyar Afirka.
An dai ga likitocin ne guda biyu ta wata kafar talabijin suna tattaunawa a wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a 'yan kwanakin nan.
Didier Drodga ya ce ra'ayin nasu ya mayar da 'yan Afirka kamar "wasu ababen yin gwaji".
A wani sakon Twitter, Drogba ya kara da cewa: "Afirka ba dakin gwaji ba ce."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Tsohon dan kwallon Kamaru, Samuel Eto'o ya kira likitocin da "miyagu", a shafinsa na Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Kazalika 'yan kungiyoyin yaki da wariyar launin fata sun soki kalaman likitocin da kuma sauran mutane da suka yi sharhi kan bidiyon.
An yada bidiyon sosai a intanet daga gidan talabijin na LCI a Faransa, wanda ya nuna Dakta Jean-Paul Mira da kuma Dakta Camille Locht suna magana kan riga-kafin annobar coronavirus.
A cikin bidiyon, Dakta Mira daga asiubitin Cochin na birnin Paris ya nuna cewa ya kamata a yi gwajin riga-kafin Covid-19 a Afirka kamar yadda aka yi na cutar kanjamau ta HIV Aids.
Dakta Camille Locht na cibiyar French National Institute of Health and Medical Research (Inserm), ya amince da ra'ayin Mira, yana cewa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3

Asalin hoton, g
An tilasta wa Democrats jinkirta ayyana mutumin da zai fafata da Donald Trump a zaben shugaban Amurka da za a yi a watan Nuwamba a yayin da ake tsaka da fama da annobar Covid-19.
Kwamitin fitar da 'yan takara na jam'iyyar, Democratic National Convention (DNC), ya bayyana cewa "ana fama da kalubale kan harkokin lafiya", don haka sai watan Agusta za a sanar da mutumin da zai yi wa jam'iyyar takara.
A halin da ake ciki, tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Biden ne ke kan gaba a masu son yi wa jam'iyyar takara a zaben da ke tafe, kuma ya yi wa mutumin da ke bi masa Bernie Sanders, fintinkau.
Kwanakin baya Mista Biden da wasu jami'an Democrats sun yi kira a jinkirta sanar da wanda zai yi wa jam'iyyar takara, wanda aka so ayyanawa ranar 13 ga watan Yuli.
Masu shirya taron fitar da dan takarar sun ce za su bi shawarwarin jami'an lafiya kafin su dauki mataki na gaba.
Mutum sama da 5,600 ne suka mutu sanadiyar Covid-19 a Amurka, yayin da mutum fiye da 236,000 suka kamu da cutar.`

Asalin hoton, Getty Images
Kasar Ghana ta bayar da rahoton mutum 214 da suka kamu da coronavirus da kuma mutuwar mutum biyar.
Mutum sama da 50 ne kuma aka sallama bayan sun warke daga cutar, inda yanzu ake sa ido a kansu daga gida.
Wasu sassa a kasar na cikin dokar zaman gida, ciki har da birnin Accra, da birni na biyu ma fi girma wato Kumasi, da garin kasuwanci na Tema, domin dakile yaduwar annobar.
An hana shige da fice in ban da abubuwan da suka zama dole. Hukumomi sun tsaurara bin sawun wadanda ake zargin sun yi mu'amala da masu cutar a garuruwan da ake da su, inda suka dauki jinin mutum kusan 6,000 domin yin gwaji.
Har wa yau, jami'an tsaro na neman wani mai coronavirus ruwa a jallo da ya tsere daga cibiyar killacewa a garin Tamale.
Iyakokin kasar na ci gaba da kasancewa a rufe tare da haramta taruwar jama'a.

Asalin hoton, EPA
Kamfanin Grupo Modelo na kasar Mexico da ke samar da barasa mai suna Corona ya ce ya dakatar da ayyukansa saboda annobar coronavirus da ke ci gaba da addabar duniya.
An mayar da kamfanin wani abin yi wa ba'a da tsokana tun bayan barkewar cutar saboda rashin sa'ar kamanceceniya da sunansa ya yi da annobar.
Wata jita-jita ma cewa ta yi kasuwar barasar a Amurka ta yi mummunar faduwa, amma kamfanin ya musanta hakan.
Hasali ma, matakin tsayar da aikin ba shi da alaka da sunan kamfanin.
Gwamnatin Mexico ta sanya Grupo Modelo a matsayin kamfanin da ba ya cikin abubuwa masu matukar amfani a yayin dokar zaman gida, hakan ya sa dole kamfanin zai tsayar da aiki har zuwa 30 ga Afrilu.
Kamfanin zai dakatar da samar da barasar Corona, wadda ake kai wa kasashe 180, daga ranar Lahadi.
Mexico na da fiye da mutum 1,500 da suka kamu da coronavirus sannan 50 suka mutu sakamakon cutar.
Jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta kara samun mutum shida da ke dauke da cutar Coronavirus.
Zuwa safiyar ranar Juma’a (3 ga watan Afrilu), akwai mutum 20 kenan dauke da Covid 19 a jihar ta Osun, a cewar hukumar yaki da cutuka ta Najeriya.
Hakan na nufin Legas da Abuja ne kawai suka fi jihar Osun yawan masu dauke da cutar Coronavirus.
A jumlace a fadin Najeriya hukumomi sun tabbatar da mutum 190 ne ke dauke da cutar a daukacin kasar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Adadin wadanda suka mutu a kasar Spain sakamakon annobar coronavirus ya karu da mutum 932 da suka mutu a cikin sa'a 24 da suka wuce, a cewar hukumomi.
Jumullar adadin yanzu ya kai mutum 10,935, adadi na biyu mafi girma kenan a duniya bayan na kasar Italiya.

Asalin hoton, Nigerian Army
Rundunar sojojin Najeriya na rokon 'yan kasar su taimaka mata da bayanai idan suka ga sojoji na cin zararfin wani yayin dokar zaman gida da aka saka saboda dakile coronavirus a kasar.
Rundunar ta kuma samar da lambobin waya da mutane za su iya kira domin bayar da rahoto, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Alhamis.
Lambobin su ne: 07017222225 - 0906005290 - 08099900131 - 08077444303.
Tun kafin a saka dokar hana fitar a wasu jihohi aka fara rade-radin cewa sojoji ne za su sa ido wurin tabbatar da ita, abin da rundunar ta sha musantawa.
Dokar hana fita a Najeriya ta fara aiki ne a daren ranar Litinin a jihohin Abuja da Legas da Ogun, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar a jawabinsa na ranar Lahadi ga 'yan kasa.
Mutum 184 ne suka kamu da cutar a kasar zuwa yanzu, inda mutum 20 suka warke sannan biyu suka mutu.