An samu karuwar mutanen da suka kamu da coronavirus ta kasashen Gabashin Afirka.
Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa mutum 10 sun kamu da ita a Rwanda ya zuwa Lahadi, inda jumulla ake da mutum 70 - mafi yawa a yankin.
A cikinsu, mutum shida sun shiga kasar ne daga Dubai, biyu daga Afirka ta Kudu, daya daga Najeriya yayin da dayan kuma ya je daga yankin Gabashin Afirka, a cewar da sanarwar da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar.
Shugaba Paul Kagame ya yi gargadin cewa za a ci gaba da samun mutanen da za su kamu da cutar a yayin da hukumomi suka ci gaba da gano mutanen da suka yi mu'amala da masu dauke da cutar.
A halin da ake ciki kasar na cikin mako na biyu na dokar hana fita ta kwana 14 da aka kakaba mata.
Eritrea ta tabbatar da cewa mutum shida sun kamu da cutar ranar Lahadi, inda jumulla suke da mutum 12 masu dauke da ita. Shida daga cikinsu sun je kasar ne gabanin soma amfani da dkar hana jiragen saman kasashen wajen shiga kasar, a cewar ministan lafiyar kasar.
Biyar daga cikin masu fama da cutar mata ne masu shekaru tsakanin 32 zuwa 60. Ana bai wa dukkansu kulawa, in ji ma'aikatar lafiyar kasar.
Kasar ta rufe dukkan makarantu sannan ta haramta shiga motocin haya. Kazalika an haramta taruwar fiye da mutum goma a wuri daya.
Ranar Lahadi Ethiopia ta sanar da samun sabbin mutum biyar da suka kamu da coronavirus inda jumulla suka kai mutum 21. A jihar Tigray da ke arewacin kasar inda aka sanar da dokar hana fita makon jiya domin dakile cutar, 'yan sanda sun harbe wani mutum har lahira a kokarinsu na tilasta bin dokar hana bude mashaya.
A kasar Kenya, mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar sun tashi daga 38 zuwa 42 ranar Lahadi. Sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun hada da wani dan kasar ta Kenya da Ba'amurke da dan kasar Kamaru da kuma dan kasar Burkina Faso.
Uganda tana da masu dauke da cutar 33 yayin da a Tanzania ake da mutum 14, ko da yake ba a samu wadanda suka kamu da coronavirus a Burundi da Sudan ta Kudu ba.