Tasirin
coronavirus ga hada-hadar kudi zai jefa kusan mutum miliyan 24 a talauci, a
kasashen gabashin Asiya da na Pacific, a cewar Bankin Duniya.
Bankin
ya bayyana cewa ''za a samu matsin tattalin arziki a duka kasashen duniya''.
Bankin
Duniyar ya yi gargadi kan jama'ar da suka dogara kan masana'antu da cewa suna
cikin babban hatsari sakamakon tasirin da cutar za ta yi.
Cutar
za ta yi tasiri ga yawan bude ido a Thailand da Tsibirin Pacific, da kuma wasu
kamfanoni da ke a Vietnam da Cambodia.
Bankin
ya bukaci yankunan da su kara inganta bangaren kiwon lafiya da kuma kayayyakin
aiki, tare da bayar da tallafi ga marasa lafiya.
A
wani hasashe da ya yi, bankin ya ce idan abubuwa ba su tabarbare sosai ba kusan
mutum miliyan 24 za su tsallake fadawa talauci a yankin a 2020, sakamakon
tasirin da annobar za ta yi ga tattalin arziki.
Idan kuma abubuwa sun tabarbare matuka kamar
yadda bankin ya yi hasashe, kusan mutum miliyan 35
za su kasance cikin talauci, ciki har da mutum miliyan 25 a China.