Gwamnatin Najeriya ta fara raba tallafin kudi naira dubu ashirin ga marasa karfi musamman a yankunan karkara daga cikin shirye-shiryenta na tallafi da ake kira Cash Transfer.
Gwamnatin ta ce tana bada kudin ne domin rage radadin rashi da wasu 'yan kasar ke fama da shi, a wani mataki na yaki da talauci a fadin kasar baki daya musamman wannan lokaci na coronavirus.
Ministar Ma'aikatar Agaji da Ci Gaban Al'umma, Sadiya Umar Farouk ta shaida wa BBC cewa suna bayar da kudin ne ga masu karamin karfi da suka da hada marayu da masu bukata ta musamman da mata marasa karfi da kuma wadanda mazajensu suka mutu.
Ta ce dubu biyar ya kamata a bai wa mutanen amma yanzu gwamnati na raba dubu ashirin ne domin rage masu radadi.
"Tun 2016 gwamnati ta fara raba tallafin ga masu karamin karfi, amma saboda coronavirus, shugaban kasa ya bukaci a ninka wa mutane kudaden zuwa N20,000 maimakon dubu biyar, saboda mutane su samu saukin radadin halin da aka shiga," inji Ministar.
Ta kuma ce gidaje sama da dubu biyar ne za a bi ana rabawa mutane kudaden a yankin karamar hukumar Kwali a Abuja.
Ministar ta bayyana cewa sun yi amfani ne da rajistar sunayen mutanen da suka amfana da shirin farko na rage talauci a tsakanin al'umma.
Sannan kuma an ninka tallafin ne domin sake rage musu radadin wahalhalun tattalin arziki da za su shiga sakamakon dokar hana fita domin yaki da coroinavirus.