Koriya Ta Kudu
Korea Koriya ta Kudu za ta aike da jirgin soji tekun Hormuz don taimaka bai wa safarar jiragen ruwa na dakon kaya damar wucewa.
Wannan mataki dai Amurka ce ta bukaci Koriya ta Kudun ta taimaka don gadin jiragen dakon mai, a daidai lokacin da dangantaka tsakaninta da Iran ke kara lalacewa.
Ma'aikatar tsaron Koriyan ta tabbatar da cewa tawagar ta za su aiki na daban, ba irin wanda kawancen Amurka ke jaoranta ba.
Tun a shekarar 2009 ne Koriya ta Kudu ta girke jirgin soji da ke yaki da masu fashin teku a tekun Aden da ke arewacin Yemen, ta dayan bangaren kuma a gabashin Afirka.
Kwamandojinta sun yi fice wajen yaki da 'yan fashin teku, musamman fafatawarsu da 'yan fashin Somaliya a shekarar 2011 a lokacin da suka kubutar da tankokin kasarsu.























