Gwamnati ta gargadi 'yan Najeriya kan cutar Coronavirus

Wannan shafi yana kawo maku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana da sauran kasashen Afirka da ma fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

  1. NCDC mai kula da yaduwar cututtuka a Najeriya ta yi gargadi kan Coronivirus

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Hukumar da ke sa ido kan yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta ja hankalin 'yan kasar da su lura da cutar Coronivirus da ke yaduwa yanzu haka a duniya.

    Hukumar ta ja hankalin 'yan kasar da su sanya ido musamman a kafofin shiga Najeriyar kamar filayen jirgin sama da sauran su.

    A wani sakon jan hankali da ta wallafa a shafinta na Twitter hukumar ta ce ya kamata 'yan kasar su yi hattara.

  2. Ghana ta yi kira da 'yan kasar su lura da cutar Coronavirus

    Cutar Coronivirus

    Hukumomi a Ghana sun bayar da sanarwar jawo hankalin al`umma dangane da fargabar bullar kwayar cutar Coronavirus.

    A cikin wata sanarwar da ma`aikatar kiwon lafiya da rattaba hannu, ministan lafiyar Mr Kwaku Agyeman Manu ya ce cutar na kama da mura da zazzabi da karancin numfashi.

    Ya kuma kara da cewa tuni aka tabbatar da cutar ta yi ajalin mutum hudu a kasar China.

    Hakazalika an samu labarin bullar kwayar cutar a kasashe kamar Koriya ta Arewa da Japan da hadaddiyar daular larabawa, don haka hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin kariya daga yaduwar kwayar cutar .

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Cutar Coronavirus ta kashe mutum hudu a China
  3. Labarai da dumi-dumi, Gwamnatin Kano ta tabbatar da bullar annobar zazzabin Lassa

    Abdullahi Umar Ganduje

    Asalin hoton, Ganduje Twitter

    Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa an samu bullar cutar zazzabin Lassa a jihar.

    Kwamishinan lafiyar jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai da ya yi a birnin Kano ranar Laraba da safe.

    A cewar kwamishinan, akalla akwai mutum 292 da ake tsammani sun kamu da wannan cuta kuma ana kula da su kamar dai yadda ka'idojin kula da cutar suka bukata.

    Ya kara da cewa gwaji kan mutum biyun da ake zargi na dauke da cutar daga cikin uku ya gano cewa sun kamu da cutar kuma sun mutu.

    Yanzu haka dai akwai wasu karin mutum biyu da ke wani asibitin garin ‘Yar Gaya da ke karamar hukumar Dawakin Kudu inda suke karbar magani.

    Kazalika, gwamnatin jihar ta Kano ta samar da kudade domin shawo kan cutar tare da wayar da kan al'ummar jahar dangane da alamomin cutar da matakan da ya kamata a dauka domin gujewa kamuwa da ita.

    Gwamnatin ta kuma bayar da lambobin waya da za a kira da zarar an ga alamun cutar

    An dai fara samun bullar cutar ne a jihar ta Kano a ranar 21 ga watan Janairu, bayan da jami'in da ke kula da cututtuka a karamar hukumar Tarauni ya bayar da rahoton wasu mutane uku da ke dauke da cutar ta Lassa.

  4. Shugaban PDP na Kano ya sauya sheka zuwa APC

    Rabiu Sulaiman Bichi

    Asalin hoton, Rabiu Bichi Facebook

    Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano, Rabi'u Sulaiman Bichi, ya ce ya sauya sheka daga jam'iyyarsa ta PDP zuwa APC.

    Rabi'u Sulaiman Bichi, wanda ya shaida wa jaridar Premium Times hakan ranar Laraba, ya ce nan ba da jimawa ba zai fito fili ya bayyana aniyar tasa ta sauya shekar da ya yi.

    Sauya shekar shugaban na jam'iyyar PDP na zuwa ne kwana biyu bayan da kotun kolin Najeriya ta tabbatar wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje nasararsa.

    Rahotanni na cewa shugaban jam'iyyar ta PDP ya sauya shekara ne tare da Hajiya Binta Sipikin wadda ita ce mai magana da yawun tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso.

    Rabi'u Sulaiman Bichi dai na daya daga cikin mukasantan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

    Rabiu Sulaiman Bichi tare da Kwankwaso

    Asalin hoton, Rabiu Sulaiman's Facebook

  5. Akwai yiwuwar za a hana 'yan Najeriya shiga Amurka

    Donald Trump

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Amurka, Donald Trump, na yin wani yunkurin kara fadada yawan kasashen da Amurka za ta hana ‘yan kasar shiga Amurka, kamar yadda rahotanni ke fadi.

    Kasashen dai wadanda su hudu ne dukkansu daga yankin Afirka suke sun hada da Najeriya da Tanzania da Sudan da Eritrea.

    Shugaba Trump, wanda ya fadi hakan yayin wata hira da mujallar Wall Streer Journal a lokacin taron koli kan tattalin arziki na duniya a Davos, Switzerland, ya tabbatar da cewa yana kokarin fadada jerin sunayen kasashen da za a hana shiga Amurka amma bai fadi sunayen su ba.

    A makon gobe ne ake sa ran za a fitar da jerin sunayen kasashen da hana su bizar Amurka zai shafa.

    A watan Satumbar 2017 ne dai shugaba Trump ya sanya takunkumin hana bizar shiga Amurka ga kasashen Iran da Libya da Somalia da Syria da kuma Yemen.

    A 2018 ne kuma kotun kolin kasar ta amince da hukuncin.

  6. Soyayyar dan Najeriya da 'yar Amurka

    Masu soyayya

    Kafin mu fara ga matashiya kan labarin matashin nan dan Najeriya da ke zaune a birnin Kano wanda ya hadu da wata 'yar Amurka a shafin Instagram inda suka yi ta shan soyayya, kafin daga bisnai ta yi takanas ta Kano ta je gidansu a birnin Kano.

    A takaice labari dai yanzu haka ana ta haramar shan shagalin biki a watan Maris. Sai ku latsa nan domin karanta cikakken labarin. . 'Matan Najeriya ba su iya soyayya kamar Turawa ba'

  7. Farawa

    Masu bibiyarmu barkanku da warhaka. Barka da sake saduwa a shafinmu na BBCHausa.com da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijer da Kamaru da Chadi da Ghana da ma sauran sassan Afirka da duniya. Da fatan yau ma za ku kasance da mu domin ci gaba da inda muka tsaya a ranar Talata.

  8. Ban kwana

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin duka-duka a nan muka kawo karshen kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kaimu za mu dawo dauke da wasu rahotannin kai tsaye. A madadin Halima Umar Saleh da Umar Mika'il da Nabeela Mukhtar da Imam Saleh muke cewa sai gobe.

  9. Labarai da dumi-dumi, Kotu ta tabbatar da zaben Fintiri da Ortom

    x

    Asalin hoton, @AhmaduFintiri

    Bayanan hoto, Ahmadu Fintiri

    Kotun Kolin Najeriya a ranar Talata ta yanke hukunci kan zaben Benue da kuma Adamawa.

    Kotun dai ta tabbatar da zaben Samuel Ortom na PDP daga Benue wanda Emanuel Jime na jam'iyyar APC ya kalubalanta.

    Hakazalika kotun ta tabbatar da zaben gwamnan Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri inda ta yi watsi da karar da Muhammad Jibirila Bindow ya shigar gabanta.

    A jiya ne dai kotun ta yanke hukunci kan zaben Kano da Sokoto da Bauchi da kuma Filato.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Samuel Ortom
  10. Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya Abubakar Bashir Wali ya rasu

    jana'izar Bashir Wali

    Asalin hoton, Abubakar Aminu Ibrahim

    jana'izar Bashir Wali

    Asalin hoton, Abubakar Aminu Ibrahim

    An yi jana’izar tsohon alkalin alkalan Najeriya Mai Shari'a Abubakar Bashir Wali a gidansa da ke Kano.

    Wasu hotuna da wani mataimaki ga gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya wallafa a Facebook sun nuna gwamnan a lokacin da ya halarci sallar jana’izar mamacin.

    Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne ya jagoranci jana'izar a ranar Talata.

    Rahotanni sun ce ya rasu ne bayan rashin lafiyar da ya yi fama da ita.

  11. Hukumar NiMet na taro domin fitar da rahoto kan hasashen ruwan sama a 2020

    .

    A yau hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Najeriya NiMet ke taro domin fitar da rahoto kan hasashenta na ruwan sama a shekarar 2020 mai taken ''Rawar da bayanai kan sauyin yanayi ke takawa wajen yanke shawara a lokacin da yanayi ke sauyawa.''

    Rahoton dai zai taimaka wa mutane musamman manoma da kuma hukumomi wajen dakile annoba wajen sanin yaushe za a fara ruwa da yaushe zai tsaya.

    Wannan na nufin manomi zai san takamaimai lokacin da ya kamata ya fara shuka lokacin damina a jihar da yake.

    Rahoton zai taimaka wa hatta masu kula da filayen tashin jirgin sama lokacin damina kan yaushe ya kamata jirgi ya tashi da kuma akasin haka.

  12. Norway ta gargadi 'yan gudun hijira masu tafiya Turai

    b

    Yayin da yake bayani a wani sansanin 'yan gudun hijira a Rwanda, Joran Kallmyr ya bayyana cewa ''Yana da kyau mu gargade su kan cewa ka da su shiga ta Libiya idan suna so a karbe su a Birtaniya''.

    Ya bayyana cewa 'yan gudun hijirar su bi ta Rwanda saboda idan suka bi ta Libiya ba za a karbe su a Turai ba.

    Mista Kallmyr ya kai ziyarar ne a ranar Litinin inda ya yi alkawarin cewa kasarsa na da niyyar daukar 'yan gudun hijira 600.

    Ya kuma bayyana cewa kasar Norway za ta bi a hankali wajen tantance 'yan gudun hijirar domin ba za ta dauki bara gurbi ba.

  13. Ra'ayoyi daga shafin Twitter

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  14. EFCC ta gurfanar da 'Mama Boko Haram' da wasu a gaban kotu

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, EFCC ta gurfanar da Aisha Wakil wadda aka fi sani da 'Mama Boko Haram' da wasu mutum biyu kan zargin almundahanar miliyan 111 a gaban kotu.

    Hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta gurfanar da Aisha Wakil tare da Tahir Sa'idu da kuma Prince Lawal Shoyode a gaban mai shari'a Aisha Kumalia da ke Babbar Kotun jihar Borno kan zarge-zarge biyar.

  15. Labarai da dumi-dumi, Ana fargabar bullar zazzabin Lassa a Kano

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Kano na cewa ana fargabar barkewar annobar zazzabin Lassa a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

    An fara zargin cewa annobar ta barke ne a asibitin bayan likitocin da suka duba wani mara lafiya sun mutu, sannan wasu mutum uku da suka yi mu’amala da shi yanzu haka na kwance cikin halin jinya.

    Mara lafiyar dai ya je asibitin ne daga jihar Bauchi.

    Kawo yanzu dai ba a tabbatar da cewa ko zazzabin na Lassa ne ya barke ba, sai dai wani likita a asibitin ya shaida wa BBC cewa alamu na nuna annobar Lasa ce ta barke a asibitin.

    Wata majiyar kuma ta shaida wa BBC cewa an dauki jinin mutanen da suka yi mu’amala da mara lafiyar da kuma likitocin da suka mutu, kuma yanzu haka ana tantance jinin a dakin bincike.

    Zuwa karfe uku na yammacin Talatar nan ne ake sa ran hukumomin asibitin za su fitar da sanarwa a kan batun.

  16. Birtaniya da Najeriya sun hada hannu don bunkasa noman gyada

    Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar Haruna Tangaza da Tajuddeen Aminu Dantata

    Burtaniyar ta shirya taron koli kan saka jari tsakaninta da kasashenna Afirka a kokarin da take yi na neman sabbin abokan hulda gabanin ficewarta daga tarayyar EU karshen wannan watan.

    Daya daga cikin muhimman abubuwan da kasashen za su fi bai wa karfi har da noman gyada da Najeriya ta yi kaurin suna a kansa.

    Alhaji Tajuddeen Aminu Dantata shi ne shugaban kamfanin Dantata Foods and Allied Products da ke Najeriya, kuma na daya daga cikin shugabannin kamfanonin da suka halarci taron daga Najeriya, ya shaida wa BBC cewa taron zai taimaka wajen samun masu siyan gyadar daga sassan duniya da kuma ita birtaniya wadde dama ita ce ke siyan yawancin gyadar da Najeriya ke samarwa.

    Ya ce kamar a Najeriya an sanya kudurin noma akalla kadada dubu dari a kashin farko na shekarar 2020.

  17. 'Boko Haram ta kashe' shugaban CAN a Adamawa

    CAN chairman Michika

    Asalin hoton, Family

    Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe shugaban kungiyar CAN na karamar hukumar Michika a jihar Adamawa.

    A ranar Talata ne Mista Nicholas wanda da ne ga wanda aka kashe ya tabbatar wa BBC da mutuwar mahaifinsa, amma ya ce ba zai iya wani karin bayani ba don suna cikin alhini da makoki.

    An dai yi garkuwa da shugaban kungiyar ne a farkon watan Janairun wannan shekara a wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a kauyensu.

    Kwanaki kadan bayan da aka yi garkuwa da shi, an ga marigayin a wani bidiyo da 'yan kungiyar Boko Haram din suka saki, inda aka ga malamin addinin yana rokon gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ceto shi.

  18. Ana neman a taimaka wa zakuna biyar da ke fama da yunwa a Sudan

    zaki a sudan

    Asalin hoton, AFP

    Rahotanni daga babban birnin Khartoum a Sudan na cewa ana ci gaba da kiraye-kirayen kai wa wasu zakuna biyar da ke fama da yunwa da rashin lafiya dauki.

    A ranar Lahadi ne jama’a suka yi tururuwa zuwa inda ake ajiyar zakunan bayan da hotunansu ya karade shafukan sada zumunta.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wanda ya tsara gangamin kubutar da zakunan, Osman Salih na cewa "Na kadu da naga hotunan zakunan, kasusuwansu duk sun bayyana saboda rama."

    Ana ajiye da zakunan biyar a keji da ke wani wurin shakatawa na Al-Qureshi da ke Khartoum amma kuma suna fama da rashin abinci da magunguna na tsawon shekaru, kamar yadda AFP ta bayyana.

    Jami’an da ke kula da wurin shakatawar da kuma ma’aikatan lafiya sun ce zakunan sun rame sosai cikin ‘yan makwanni.

    "Babu abinci, a mafi yawan lokuta muna sayen abincin da kudinmu domin ciyar da su," in ji Essamelddine Hajjar mai kula da wurin shakatawar.

    Karamar hukumar Khartoum ce ke kula da wajen baya ga tallafi daga masu bayar da gudummawa sai dai Sudan ta samu kanta cikin matsalar tattalin arziki sakamakon hauhawar farashin kayan masarufi da kuma karancin kudaden canji, kamar yadda AFP ya rawaito.

  19. Taron wayar da kan nakasassu a Nijar

    Bayanan sautiRahoton Tchimma kan nakasassu

    Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron rahoton

    A Jamhuriyar Nijar, nakasasun yankin Goure ta jahar Damagaram sun samar da wata kungiya da za ta ba su damar tunkarar matsalolin da suke yi wa rayuwarsu tarnaki.

    Gwamnatin Nijar din a nata bangaren ta shirya wasu tarurruka don taimaka wa nakasasun wajen sanin hakkokinsu da kuma yadda za su yi kokowa don kwato su.

  20. Myanmar kan batun Musulman Rohingya

    Kotun da gwamnatin Myanmar ta kafa ta karkare cewa ta yiwu wasu daga cikin sojin kasar sun aikata laifukan yaki akan tsirarun Musulmin kabilar Rohingya, amma ba a samu sojojin da aikata kisan kare dangi ba.

    Masu binciken sun duba abin da ya faru a shekarar 2017 a jihar Rakhine da ya janyo rasa matsugunin sama da Musulmin Rohingya 700,000.

    Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi sojojin da aikata kisan kare dangi ga 'yan Rohingya, wannan rahoto na zuwa ne kwanaki gabannin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague ta yanke nata hukuncin.