Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnati ta gargadi 'yan Najeriya kan cutar Coronavirus

Wannan shafi yana kawo maku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana da sauran kasashen Afirka da ma fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

  1. Sau uku kotuna na korar karar Abba Kabir Yusuf

    Abba Kabir Yusuf ya fara kai kara ne kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Kano a watan Afrilun 2019, inda bayan sauraron korafe-korafensa, kotun ta kori karar.

    Daga baya ya mayar da karar gaban kotun daukaka kara wadda ita ma ta sake watsi da karar a watan Nuwamban 2019.

    Sai kuma a yau Litinin 20 ga watan Janairun 2020, Kotun Koli ta yanke hukunci karshe wanda Abba ba zai sake samun wata dama ta kai kara ba.

  2. Alkalan da suka yanke hukuncin Kano

    Wannan hukunci na yau Kotun Koli na nufin Abba Gida-Gida kamar yadda aka fi saninsa, ba zai iya kara daukaka kara ba.

    Mai shari'a Sylvester Ngwuta ne ya jogaranci yanke hukuncin tare da sauran alkalan da suka hada da Mai shari'a Kudirat Kekekere-Ekun da Mai shari'a Olukayode Ariwoola da Mai shari'a Amina Augie da kuma Mai shari'a Uwani Abba-Aji.

  3. An zo kan Sokoto

    A yanzu kuma alkalan sun fara karanto shari'ar jihar Sokoto tsakanin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na PDP da Ahmad Aliyu na APC.

  4. Kanawa mabiya Ganduje da Abba sun fara barin cikin kotun

    Yanke wannan hukunci ke da wuya sai mabiyan Ganduje da Abba suka fara barin cikin Kotun Kolin, in ji abokin aikinmu da ke a kotun.

  5. Labarai da dumi-dumi, Kotu ta kori karar Abba Kabir Yusuf

    Kotun Kolin Najeriya ta kori karar Abba Kabir Yusuf inda ta tabbatar wa Abdullahi Umar Ganduje da kujerarsa.

  6. Shari'ar Kano na daukar hankali

    Wannan shari'a ta Kano ga dukkan alamu ita ce ta fi daukar hankalin al'umma, watakila saboda irin sarkakiyar da ke cikinta da kuma girman jihar a matsayinta nta cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya.

  7. An kira shari'ar farko

    Shari'ar farko da aka fara kira ita ce tsakanin Abba Kabir Yusuf da wadanda yake kara bangarori biyu, Ganduje da hukumar INEC.

    An kuma fara karanta hukunci.

  8. Alkalai biyar sun shigo kotu

    A halin yanzu dai alkalai biyar cikin bakwai sun iso cikin Kotun Kolin kuma ana sa ran da zarar saura biyun sun iso za a fara zaman shari'a.

    Kotun ta yi tsit in ji abokin aikinmu da ke a cikin kotun

  9. Tsohon gwamnan Bauchi M.A ya iso kotu

    Tsohon gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar na jam'iyyar APC ya hallara a cikin Kotun Koli inda tuni ya zauna domin jiran hukuncin kotun kan karar da ya kai a gabanta.

  10. Gwamnan Bauchi Bala Kaura ya hallara a kotu

    Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad na jam'iyyar PDP ya hallara a Kotun Koli, Mohammed Abdullahi Abubakar na jam'iyyar APC wanda shi ne tsohon gwamnan jihar ke kalubalantar nasarar da Balan ya samu a bara.

    A makon da ya gabata dai ana ta rade-radin cewa an kwantar da Bala Muhammad din a wani asibiti da ke Landan sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita.

  11. An tsaurara tsaro a Kotun Kolin Najeriya

    An dai jigbe jami'an tsaro gabanin fara zaman Kotun Koli kan shari'o'in zaben jihohin da ke gabanta.

    Lauyoyi da 'yan jarida da 'yan siyasa, mafi yawansu daga Kano da Sokoto su ne suka cika kotun, kamar yadda abokin aikinmu da ke can Yusuf Ibrahim Yakasai ya shaida mana.

    Akwai kuma 'yan sanda da dama a cikin kotun wadanda suke kula da kofofin shiga.

    Wakilin ya ruwaito mana cewa a wasu lokutan 'yan sandan suna amfani da karfi wajen hana mutane shiga zauren kotun musamman idan an samu turmutsutsu.

    Akwai matakan tsaro hudu da aka sanya a kan hanya kafin kai wa harabar ginin kotun.

  12. Shimfida

    A ranar Litinin ne aka sa ran Kotun Koli a Najeriya za ta yanke hukunci kan kararrakin zabukan gwamna na jihohin Kano da Sokoto da Bauchi da Benue da Filato.

    A Kano dan takarar gwamna na PDP ne dai Abba Kabir Yusuf ke kalubalantar nasarar da Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben bayan da kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar Kano da kuma kotun daukaka kara a Kaduna suka yi watsi da kararrakin da ya kai.

    Yayin da shi kuma Ahmad Aliyu Na APC yake kalubalantar nasarar da Aminu Waziri Tambuwal na PDP ya samu shi ma a zaben inda daga baya kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar, da kuma kotun daukauka kara a Kaduna suka yi watsi da kararrakin da ya kai gabansu.

    A jihohin Kano da Sokoto dai sai da aka je zagaye na biyu a zaben gwamnan jihohin da aka gudanar a bara.

    Akwai kuma shari'a tsakanin Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad na jam'iyyar PDP da kuma Mohammed Abdullahi Abubakar na jam'iyyar APC.

    Sai kuma akwai shari'a tsakanin Samuel Ortom na jam'iyyar PDP da kuma Emmanuel Jime na jam'iyyar APC daga Benue, sai kuma na jihar Filato tsakanin Jeremiah Useni na jam'iyyar PDP da kuma Simon Bako Lalong na jam'iyyar APC.

    A makon da ya gabata ne dai kotun ta yanke hukunci kan zaben Imo inda ta kori Emeka Ihedioha daga gwamnan jihar ta bai wa Hope Uzodimma na jam'iyyar APC.

  13. Barka da warhaka

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu barkanku da warhaka. Da fatan kun wayi gari lafiya. A ranar Litinin za mu ci gaba da kawo muku wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana da sauran sassan Afirka da ma duniya.

    Kuma a yau za mu kawo muku rahotanni kai-tsaye kan yadda Kotun Koli a Najeriya za ta yanke hukunci kan shari'ar zabe na wasu jihohi da suka hada da Kano da Sokoto da Bauchi da Filato da Benue. Sai ku ci gaba da kasancewa da mu.