Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnati ta gargadi 'yan Najeriya kan cutar Coronavirus

Wannan shafi yana kawo maku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana da sauran kasashen Afirka da ma fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

  1. Ana tuhumar 'yan sanda da laifin cin zarafin wani direba a Ghana

    Ana tuhumar wasu 'yan sanda guda biyar da laifin cin zarafin wani deriba har suka raunata shi, a Bimbilla da ke yankin arewacin Ghana.

    A baya nan dai ana ci gaba da samun yadda ake dakatar da jami'an 'yan sanda tare da tuhumar su a kan lafukan da suka aikata musamman na cin rafin al'umma da rashin iya aiki.

  2. Ukraine ta bukaci Iran ta mika na'urar daukar bayanan jirgin da ya yi hatsari

    Ministan harkokin wajen Ukraine ya ce ya kamata Iran ta mika na'urarar daukar bayanan jirgin saman nan da ya yi hatsari a Tehran a farkon watan nan.

    Vadym Prystaiko zai gana da ministan gwamnatin Iran, wanda ya tafi Kyiv domin tattaunawa.

    Da yake jawabi a wani taron manema labarai, Mista Prystaiko ya ce na'urar nadar bayanan jirgin mallakar Ukraine ce, saboda haka ya kamata a mika musu shi.

    Iran ta tabbatar da cewa ita ce ta harbo jirgin amma a bisa kuskure.

    A yau ne za a gudanar da jana'izar mutanen da al'amarin ya rutsa da su a Ukraine.

    Daga cikin mutum 176 da suka mutu a hatsarin jirgin, mutum 11 daya daga cikinsu 'yan Ukraine din ne.

  3. Har yanzu ana jiran alkalai

    Har yanzu ana dakon shigowar alkalai minti 20 bayan cikar lokacin da suka sa domin komawa zaman

  4. Kotu na shirin dawowa daga takaitaccen hutu

    Kotun Koli na dab da dawowa daga takaitaccen hutun da ta tafi inda ake sa ran idan ta dawo ta dora daga inda ta tsaya na shari'o'in Bauchi da Filato.

    Gwamna Simon Lalong na Filato shi ma ya zo kotun .

  5. Zaki na neman janyo zanga-zanga a Sudan

    Ana ta samun kiraye-kiraye a shafukan intanet na a ceto wani zaki da ke fama da yunwa wanda aka killace a wani wurin shakatawa da ke birnin Khartoum na kasar Sudan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

    A ranar Lahadi ne dai dandazon jama'a ya nufi wurin shakatawar bayan da hotunan zakin suka mamaye kafafen sada zumunta.

    Akwai dai zakuna guda biyar da ke daure a cikin keji a wurin na shakatawa wandanda ke fama da matsalar yunwa da magani na tsawon 'yan makonni.

    Jami'an da ke kula da wurin shakatawar na cewa wasu daga cikin zakunan sun rasa kaso biyu bisa uku na nauyinsu a 'yan kwanakin da suka gabata.

  6. 'Yan Tanzania da dama za su iya rasa wayoyinsu

    Nan gaba a yau ne miliyoyin ‘yan Tanzania za su iya rasa wayoyinsu na salula idan aka toshe layukan wayoyin nasu.

    Hakan wani bangare ne na yunkurin gwamnati na ganin an yi wa kowane layin waya rajista kafin cikar wa’adin karfe 10 na daren yau Litinin.

    Tanzania ce kasar yankin Afirka ta baya-bayan nan da ita ma ta rungumi tsarin zamanantar da rajistar wayoyin salula.

    An shafe makwanni ana samun dogon layin jama’a a wajen ofishin hukumar bayar da katin shaidar zama dan kasa yayin da ‘yan Tanzania suke kokarin yin rajista saboda kauce wa rasa damar yin amfani da wayoyinsu na salula.

    Sai dai yayin da wa’adin da aka sanya kan shirin rajistar ke karatowa, sama da mutane miliyan 20 ne basu samu yin rajistar layukan wayarsu ba.

  7. Ganduje ya bukaci 'yan hamayya su hada hannu da gwamnati

    Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga abokan hamayyarsa da su zo su hada hannu domin ci gaban Kano.

    Ya bayyana haka ne wata sanarwa jim kadan bayan hukuncin Kotun Koli a ranar Litinin.

    A sanarwar da Abba Anwar ya fitar wanda shi ne sakataren watsa labaran gwaman ya yi godiya ga jama'ar Kano da suka dage da addu'o'i domin ganin sun samu nasara.

    Ya kuma yaba wa alkalan kotun wadanda suka gudanar da shari'ar inda ya bayyana cewa hakan na nuna jajircewar bangaren shari'ar wajen kawo ci gaba ga dimokradiyya.

  8. Ranar Laraba kotu za ta yanke hukunci kan belin Shehu Sani

    Kotu ta saka ranar Laraba 22 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan batun neman beli da lauyoyin Shehu Sani suka yi.

    Kotun kuma ta saka ranar Litnin 27 ga watan Janairu a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan bukatar EFCC na neman ci gaba da tsare Shehu Sani.

  9. Mutane sun yi cirko-cirko a titunan Legas

    Daruruwan mutane sun yi cirko-cirko a safiyar Litinin a gefen titunan birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya sakamakon daukewar masu baburan haya da aka fi sani da okada a birnin.

    Hakan ya biyo bayan gargadin ba-zata da gwamnatin jihar ta bayar na dakatar da ayyukan 'yan okada.

  10. Shari'ar Shehu Sani

    Lauyoyin EFCC karkashin jagorancin Barista G.K Latonu sun nemi karin kwanaki 14 domin ci gaba da tsare sanatan domin ba su damar tatsar bayanai daga gareshi kan zarge-zargen da suke yi masa.

    Barrista Abdul Ibrahim shi ne lauyan da ke jagorantar lauyoyin da ke kare Shehu Sani.

    A halin yanzu dai lauyoyin Shehu Sani sun nemi a bayar da belinsa.

    Sanatan dai bai hallarci zaman kotun ba.

  11. Kotu ta tafi hutu

    Lauyoyin M.A sun nemi kotu ta soke zaben Bala ta kuma ayyana M.A a matsayin gwamnan Bauchi.

    Lauyoyin Bala da INEC sun nemi a yi watsi da karar saboda ba su da hujja.

    A halin yanzu dai kotu ta yanke cewa za a saurari daukaka karar da M.A ya yi

    Kotun ta tafi hutu, za ta dawo karfe uku na yamma domin ci gaba da zamanta.

    Kotun ta tashi ne bayan sauraron Lauyoyin masu kara da masu kare kai a shari'ar Filato da Bauchi

  12. Fashewar bututun mai ta hallaka mutum uku a Lagos

    Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutum uku sakamakon gobarar da ta tashi a wani waje a birnin Legas da ke kudancin kasar.

    Gobarar ta tashi lokacin da wani bututun mai na babban kamfanin man fetur na kasar, NNPC, ya kama da wuta ranar Lahadi da daddare.

    Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce ta ciro gawar mutumu uku-- manyan mutane biyu da kuma wani yaro daya--wadanda suka kone sakamakon tashin gobarar.

    Kazalika wasu gidaje da motoci da ke kusa da bututun man sun kone.

    Hotuna sun nuna yadda wuta ta rika yin rimi a yankin na Abule-Egba. Galibi dai ana samun tashin irin wannan gobara ne sakamakon aikin masu satar mai da ke fasa bututan man.

  13. An fara shari'ar Bauchi

    A halin yanzu dai an kira shari'ar Bauchi inda Mohammed Abdullahi Abubakar na jam'iyyar APC wanda shi ne tsohon gwamnan jihar yake kalubalantar nasarar da Bala Muhammad na jam'iyyar PDP ya yi a zaben gwamnan jihar.

  14. Za a fara shari'a tsakanin Shehu Sani da EFCC da ASD

    A wani bangaren kuma, a ranar Litinin ne ake fara sauraren shari'a a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja tsakanin Sanata Shehu Sani da Hukumar EFCC da kuma Alhaji Sani Dauda (ASD).

    Tun a kwanakin baya ne dai hukumar EFCC ta tsare Shehu Sani inda take zarginsa da karbar ''kudade da sunan mukaddashin hukumar EFCC Ibrahim Magu''.

    Tuni Shehu Sani ya musanta zargin da ake yi masa.

  15. Yadda magoya bayan Ganduje ke murna a Kano

    Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon.

  16. Alkalai 7 sun dawo zaman kotun bayan hutu

    Alkalai bakwai sun dawo zaman kotu bayan hutun da suka tafi na dan wani lokaci.

    Tun da farko dai alkalai biyar ne suka yanke hukunci kan zaben Kano da Sokoto a safiyar yau.

    A yanzu haka dai an kira shari'ar jihar Filato tsakanin Jeremiah Useni na jam'iyyar PDP da kuma Simon Bako Lalong na jam'iyyar APC.

  17. Magoya bayan Ganduje da Tambuwal bayan hukuncin kotu

  18. PDP na zanga-zanga kan hukuncin zaben gwamnan Imo

    A yau ne jam'iyyar PDP ke jagorantar wata zanga-zanga don nuna adawa da hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar Imo a Najeriya.

    A makon da ya gabata ne kotun ta kwace nasarar Emeka Ihedioha na PDP wanda har ya kusa shafe shekara a kan mulkin, ta bai wa dan takarar APC Hope Uzodimma.

    Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar musamman daga bangaren da ke hamayya

  19. Kotu ta tafi hutu

    A halin yanzu dai kotun tafi hutu kuma ana sa ran cewa za ta dawo nan ba da jimawa ba domin yanke hukunci kan zaben Bauchi da Benue da kuma Filato.

  20. Labarai da dumi-dumi, Kotu ta tabbatar wa Tambuwal da kujerarsa

    Kotun Koli ta kori karar Ahmed Aliyu na APC ta tabbatar wa Aminu Waziri Tambuwal na PDP da kujerarsa ta gwamnan Sokoto.