Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa an samu bullar cutar zazzabin Lassa a jihar.
Kwamishinan lafiyar jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai da ya yi a birnin Kano ranar Laraba da safe.
A cewar kwamishinan, akalla akwai mutum 292 da ake tsammani sun kamu da wannan cuta kuma ana kula da su kamar dai yadda ka'idojin kula da cutar suka bukata.
Ya kara da cewa gwaji kan mutum biyun da ake zargi na dauke da cutar daga
cikin uku ya gano cewa sun kamu da cutar kuma sun mutu.
Yanzu haka dai akwai wasu karin mutum biyu da ke wani
asibitin garin ‘Yar Gaya da ke karamar hukumar Dawakin Kudu inda suke karbar magani.
Kazalika, gwamnatin jihar ta Kano ta samar da kudade
domin shawo kan cutar tare da wayar da kan al'ummar jahar dangane da alamomin
cutar da matakan da ya kamata a dauka domin gujewa kamuwa da ita.
Gwamnatin
ta kuma bayar da lambobin waya da za a kira da zarar an ga alamun cutar
An dai fara
samun bullar cutar ne a jihar ta Kano a ranar 21 ga watan Janairu, bayan da jami'in da ke kula da cututtuka a karamar hukumar Tarauni ya bayar da rahoton wasu mutane uku da ke dauke da cutar ta Lassa.