Kotu ta hana yi wa Musulmin Rohingya kisan kare-dangi
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da umarnin daukar matakan kare Musulman Rohingya daga kisan kare-dangi a kasar Myanmar da a baya ake kira (Burma).
An yanke shawarar hakan ne duk da cewa jarogar gwamnatin kasar, Aung San Suu Kyi, ta kare kasarta da kanta kan zarge-zargen a watan jiya.
Dubban ‘yan Rohingya sun mutu, sannan fiye da mutum 700,000 sun tsere zuwa Bangladesh a lokacin da sojoji suka far masu a 2017.
Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa za a iya sake samun irin wannan kisan kare-dangin.
Karar, wadda kasar Gambiya ta shigar a kotun, ta yi kira da a dauki matakan gaggawa kan sojojin Myanmar har sai an gudanar da cikakken bincike.
Myanmar ta sha dagewa cewa sojojinta na yakin magance masu tsattsauran ra’ayi ne a jihar Rakhine.
A takarda da ta fitar na kariya kan karar a babban kotun Hague, Aung San Suu Kyi, ta kwatanta rikicin a matsayin ‘’yakin cikin gida’’ da ‘yan ta’addan Rohingya suka kai hare-hare kan wuraren aikin jami’an tsaron gwamnati.

Asalin hoton, EPA

















