Sanatoci 107 ne suka halarci zaman
Sunayen sanatoci 107 daga cikin 109 aka karanto a matsayin wadanda suka halarci zaman na yau.
Kuma akawun majalisar ya ce adadin ya kai wanda ake bukata domin aiwatar da aikin majalisa.
Labarai da rahotanni game da rantsar da 'yan majalisar dattawa da wakilai na Najeriya, da kuma zaben shugabannin majalisun guda biyu.
Umar Rayyan, Usman Minjibir and Umar Mikail
Sunayen sanatoci 107 daga cikin 109 aka karanto a matsayin wadanda suka halarci zaman na yau.
Kuma akawun majalisar ya ce adadin ya kai wanda ake bukata domin aiwatar da aikin majalisa.
Wasu gwamnonin jam'iyyar APC karkashin jagorancin shugabansu Kayode Fayemi na jihar Ekiti, sun isa zauren majalisa domin shaida yadda zaben zai kasance.
Daga cikinsu akwai Aminu Masari na Katsina, Umar Ganduje na Kano, da kuma Abdulrahman Abdulrazak na Kwara.

Asalin hoton, Premium Times
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A yanzu ana kan tantance dukkan 'yan majalisa, inda ake kiran sunansu jiha bayan jiha domin tabbatar da wadanda suke zauren majalisar.
Daga bisani ne kuma za a fara batun kada kuri'a.
A yanzu 'yan majalisar dattawa ake kira.

Asalin hoton, Chennels TV
Za ku iya garzayawa shafiinmu na Facebook don kallon yadda ake rantsar da 'yan majalisar dokokin Najeriya kai-tsaye a Abuja.
Tsohon dan majalisar wakilai daga jihar Neja Abubakar Cika Adamu ya ce babban akawun majalisa ne zai fara da karanta jawabin shugaban kasa.
Daga nan kuma sai ya jagoranci zaben, inda za a fara da zaben shugabannin majalisar dattawa kafin na wakilai.
Mai neman shugabancin majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmed Ibrahim Lawan lokacin da suka isa zauren majalisar a ranar Talata.

Asalin hoton, Twitter
Mai neman shugabancin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila tare da matarsa lokacin da suka isa zauren majalisar a ranar Talata.

Asalin hoton, Twitter
Dan majalisar wakilai Femi Gbajabiamila daga jihar Legas shi ne jam'iyyar APC take mara wa baya don zama shugaban majalisar wakilai ta 9.

Asalin hoton, Facebook

Asalin hoton, Facebook
Babban Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar adawa ta PDP ya tsayar da Sanata Ali Ndume a matsayin dan takararta a zaben shugabancin Majalisar Dattawa da kuma Umar Mohammed Bago a matsayin Kakakin Majalisar Wakilai.
Kwamitin ya bayyana haka ne a wani sako da ya aike wa manema labarai ta hannun sakatarenta na kasa Umar Ibrahim Tsauri, inda kuma ta ce ta zabi Ndume ne bayan wata muhimmiyar tattaunawa tsakanin manyan ‘ya’yanta.
Ciki har da gwamnoni da sanatoci da sauran ‘yan majalisun da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar.
Jam’iyyar ta ce: “Mun dauki wannan mataki ne domin ci gaban kasa ta hanyar tabbatar da manufar jamn’iyyarmu ta karfafa dimokradiyya da kuma tabbatar da samar da Majalisar Kasa mai cin gashin kanta, da kuma bin diddigin aikace-aikacen bangaren zartarwa.”
Sanata Ahmed Ibrahim Lawan daga Yobe da kuma Sanata Ali Ndume daga jihar Borno, Sanata Lawan shi ne wanda jam'iyya mai mulki wato APC ta tsayar da shi. Yayin da Sanata Ndume yake takarar bisa radin kansa.

A ranar Alhamis ne aka rufe Majalisar Tarayyar Najeriya ta 8 da ke a Abuja. Wannan ya zo ne bayan cikar wa'adinta na shekara hudu kamar yadda doka ta tanada.
A mako mai zuwa wato a ranar Talata 11 ga watan Yunin 2019 ne ake sa ran za a sake bude majalisar ga zababbun sanatoci da 'yan majalisar wakilai, inda za su zabi shugabanninsu domin tafiyar da ayyukansu.
BBC ta halarci nade tabarmar majalisar inda muka zan ta da wasu sanatoci da 'yan majalisa a kan kalubale da nasarorin da majalisar ta samu.
Barka da shigowa wannan shafi, inda za mu kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye game da rantsar da 'yan majalisar dattawa da na wakilai na Najeriya, da kuma zaben shugabannin majalisun guda biyu.