APC ta cinye kujerun shugabancin majalisar dokoki

Labarai da rahotanni game da rantsar da 'yan majalisar dattawa da wakilai na Najeriya, da kuma zaben shugabannin majalisun guda biyu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Rayyan, Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. An fara ware kuri'u

    An fara ware kuri'un da aka kada na zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa.

    An fafata tsakanin Omo-Agege na APC da kuma Ike Ekweremadu na PDP.

    Majalisa

    Asalin hoton, Channels

  2. Wane ne Ahmed Lawan

    Ahmed Lawan

    Asalin hoton, Nigeria

    Sabon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, wanda ke wakiltar Arewacin Yobe, gogaggen dan majalisa ne wanda ya shafe shekara 20 a zauren majalisar tarayya.

    An fara zabarsa ne zuwa majalisar tarayya a shekarar 1999, inda kuma ya kasance a can har zuwa shekarar 2007.

    Ya shugabanci kwamitoci daban daban da suka hada da na ilimi da kuma ayyukan noma.

    Dr Ahmed Lawan, wanda aka haifa a shekarar 1959 a jihar Yobe, inda kuma ya yi digiri na farko a jami'ar Maiduguri, kafin ya yi na biyu a Jami'ar Ahmadu Bello da kuma na uku a Burtaniya, ya zama Sanata a 2011.

    Ya shugabanci kwamitoci daban daban, kuma ya zama mamba a kwamitin gyaran tsarin mulki na kasa.

    An nada shi shugaban masu rinjaye bayan da aka sauke Sanata Ali Ndume a wani yanayi mai cike da rudani.

  3. Ana kada kuri'ar zaben mataimakin Lawan, An zabi Ahmed Lawan shugaban majalisar dattawa

    Ana kada kuri'a a zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa a asirce.

  4. Za a fara zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa

    Bayan zaben Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya, yanzu za fara zaben mataimakinsa.

  5. An rantsar da Ahmed Lawan

    Bayan bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Ahmed Lawan ya karbi rantsuwa daga hannun akawun majalisa.

    Ahmed Lawan

    Asalin hoton, Channels

  6. Ndume ya taya Ahmed Lawan murna

    An bayyana Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban majalisar dattawa, inda ya samu kuri'a 79, yayin da Ndume ya samu 28.

    Kuri'a 107 aka kada gaba daya.

    Majalisa

    Asalin hoton, Channels

    Bayanan hoto, Ndume da Lawan
  7. Labarai da dumi-dumi, Ahmed Lawan ya lashe zabe

    Ahmed Lawan ya zama shugaban majalisar dattawa inda ya kayar da Ali Ndume.

  8. An fara kirga kuri'a

    Tuni aka fara kirga kuri'un da aka kada a zaben shugaban majalisar dattawa tsakanin Ahmed Lawan da Ali Ndume.

  9. Sanatoci na gaisa wa da Ahmed Lawan

    Wasu daga cikin sanatocin da ke goyon bayan Ahmed Lawan na gaisawa da shi bayan da aka fara ware kuri'un da aka kada.

    Alamu na nuna cewa kamar na sa sun fi yawa.

    Majalisa

    Asalin hoton, Chennels

  10. Yadda 'yan takara ke jiran sakamako

    Sanata Ali Ndume da kuma Ahmed Lawan suna jiran sakamakon zaben da aka kada, inda ake tantance kuri'u.

    Ali Ndume

    Asalin hoton, Channels

    Bayanan hoto, Ali Ndume cikin fararen kaya kamar yadda ya saba bayyana
    Ahmed Lawan

    Asalin hoton, Channels

    Bayanan hoto, Ahmed Lawan yana jiran sakamakon zabe
  11. An kammala kada kuri'a

    An kammala kada kuri'a a zaben shugaban majalisar dattawa.

    A yanzu za a fara ware kuri'un da aka kada domin tantance su.

  12. Ra'ayoyinku daga Twitter

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Kauce wa X, 3
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 3

    Kauce wa X, 4
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 4

    Kauce wa X, 5
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 5

  13. "Zan rushe ofishin Shugaban Majalisar Dattawa in aka zabe ni"

    Sanata Ali Ndume, wanda shi ne dan takarar da PDP ke mara wa baya ya ce idan har ya yi nasarar cin zaben Shugaban Majalisar Dattawa zai rushe ofis din shugaban majalisar.

    Ya ce wannan yana cikin manufofinsa ne guda tara da yake da zummar aiwatarwa idan ya yi nasara.

    Ya kuma bayyana cewa hakan zai bai wa sauran 'yan majalisa damar taka muhimmiyar rawa da kuma kara masu kwarin gwiwa domin ofis din yana hana su rawar gaban hantsi.

    "Tasirin sanatoci yana raguwa saboda tarin iko da aka bai wa ofishin shugaban majalisa, wanda shi ne yake dakile su a wasu lokuta."

    Sanata Ali Ndume da Ahmed Lawan, wadanda su ne 'yan takarar dukkaninsu 'yan jam'iyyar APC ne mai mulki.

    Ali Ndume
  14. BBC Hausa Facebook

    Za ku iya garzayawa shafiinmu na Facebook don kallon yadda ake rantsar da 'yan majalisar dokokin Najeriya kai-tsaye a Abuja.

  15. Zabe na tafiya lami-lafiya

    Kawo yanzu babu wani tsaiko da aka samu tun bayan fara kada kuri'a a zaben shugaban majalisar dattawa.

    Sanatoci na kada kuri'a daya bayan daya.

    Haka kuma suna ci gaba da zagayawa suna gaisawa da magana da juna cikin kwanciyar hankali.

    'Yar fargabar da aka taso da ita da farko ta kau.

  16. ...Zauren majalisar

    Zauren majalisar yayin da ake ci gaba da kada kuri'a a zaben shugaban majalisar dattawa.

    Ana fafatawa ne tsakanin Ali Ndume daga jihar Borno da kuma Ahmed Lawan daga Yobe.

    A
    A
    A
  17. An fara kada kuri'a a majalisar dattawa

    'Yan majalisar dattawa sun fara zaben shugabansu tsakanin Sanata Ali Ndume da kuma Ahmed Lawan.

    Ana kiran sanatocin ne daya bayan daya inda suke tafiya suna kada kuri'unsu a cikin sirri.

    Sanatocin jihar Abia ne suka fara jefa kuri'unsu kuma za a karkare ne da na jihar Zamfara.

    Majalisa

    Asalin hoton, Channels TV

  18. Ina takara ne saboda ci gaban kasa - Sanata Ahmed Lawan

    Sanata Ahemd Lawan, wanda shi ne dan takarar da APC ke mara wa baya ya ce takararsa ta ci gaban kasa ce.

    Ya bayyana hakan a zauren majalisa yayin da ake shirye-shiyen fara jefa kuri'a a zaben shugabannin majalisar.

    Ahmed Lawal ya ce "Tarihi zai tuna da mu idan mun yi aiki tare, cewa son zuciyarmu bai hana mu cim ma muhimman ayyukan majalisa ba."

    "Duk da cewa mun yi aiki tukuru a shekara hudu da suka gabata don inganta tsaro amma har yanzu muna fama da matsaloli.

    "Wajibi ne mu yi aiki tare don samar da yanayi mai kyau wanda zai samar da aikin yi ga 'yan kasa da kuma tsaron lafiyarsu.

    "Ina tabbatar maku cewa idan kuka zabe ni zan yi aiki tare da kowa da kowa a wannan majalisa ta tara."

    Ahmed Lawal

    Asalin hoton, Channels TV

  19. An gabatar da Ali Ndume

    An gabatar da sunan Sanata Ali Ndume a matsayin wanda zai nemi shugabancin majalisar dattawa, kuma ya amince.

    A yanzu shi ne zai fafata da Sanata Ahmed Lawan.

  20. An gabatar da sunan Ahmed Lawan

    An gabatar da Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takarar Shugaban Majalisar Dattawa, kuma ya amince da ya tsaya takara.

    Ahmed Lawan

    Asalin hoton, Channels TV