Yadda aka fafata a muhawarar jihar Nasarawa

Yadda ake gudanar da muhawara tsakanin 'yan takara biyar da ke neman kujerar gwamnan jihar Nasarawa.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Hira da wasu 'yan siyasa a jihar Nasarawa

    Bayanan bidiyo, Hira da wasu 'yan siyasa a jihar Nasarawa
  2. Takaitaccen tarihin jihar Nasarawa

    Nasarawa ta samu Jiha ne a ranar 1 ga watan Octoba 1996 a lokacin gwamnatin marigayi Sani Abacha.

    Jihar ta Nasarawa tana arewa da Kaduna, yamma da birnin tarayya Abuja, kudu da jihar Kogi, gabas da Taraba.

    Jihar dai tana da kananan hukumomi 13 kuma noma ne babbar sana'ar mazauna Jihar.

    Gwamnan Jihar na yanzu shine dai Alhaji Umaru Tanko Al-Makura.

    Gwamnonin Nasarawa a baya.

    • Abdullahi Ibrahim- 1996-1998
    • Bala Mande 1998-1999
    • Abdullahi Adamu 1999-2007
    • Aliyu Doma- 2007-2011
  3. Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

    Idris Kabiru Ohiz: Barkan ku da zuwa jihar Nasarawa. Muna muku godiya.

    Sade Saidu Daura: Masu takarar gwamnan jahar Nasarawa ku fadawa jama'ar ku abin da za ku iya yi ba yin romon baka ba dan kwadayin samun kujerar gwamna ba.

    Usman A Bello: Bunkari Allah kasa ayi wannan muhawarar lafiya akare lafiya Haka kuma muna kira ga yan jahar nasarawa da su saurare abinda zaa tattauna domin zaben abinda ya dace

  4. Ra'ayoyin mutane kan muhawarar da BBC za ta gabatar

    Yadda wasu mazauna jihar Nasarawa suka bayyana ra'ayinsu kan yadda suka ji da BBC ta shirya muhawara da'yan takara biyar masu neman kujerar gwamnan jihar Nasarawa.

    Bayanan bidiyo, ra'ayoyin mutane game da Muhawarar da za a yi a Nassarawa
  5. 'Yan takara biyar ke neman kujerar Gwamnan jihar Nasarawa

    1. Injiniya Abdullahi A. Sule na jam'iyyar APC

    2. Labaran Maku na jam'iyyar APGA

    3. David Emmanuel Ombugadu na PDP

    4. Umar Aliyu Doma na ZLP

    5. Danjuma Muntari Kereni na YPP.

    BBCGovDebate

    Asalin hoton, bbc

  6. Dakin da za a gabatar da muhawara

    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
  7. Tun a ranar Talata tawagar BBC ta isa jihar Nasarawa

    Tagawar BBC Hausa ta isa Nasarawa da ke arewacin kasar ranar Litinin domin gudanar da muhawara da 'yan takarar gwamnan jihar a zaben 2019.

    Tagawar, wacce ta kunshi ma'aikata fiye da goma wadanda za su kawo labarai da rahotanni a kan batutuwa daban-daban game da shirye-shiryen zabe da kuma manufofin 'yan takarar.

    Wannan shi ne karon farko da BBC ke gudanar da muhawara a zabukan gwamna.

    BBCGovDebate
  8. Jama'a barkanmu da saduwa a cikin shirin kai tsaye kan yadda za a gudanar da muhawara tare da 'yan takara biyar masu neman kujerar gwamnan jihar Nasarawa.

    Za ku iya bayar da gudunmawarku kai tsaye a BBC Hausa Facebook ko ta twitteer #BBCGovDebate.

    Nine Mohammed Abdu zan gabatar da muhawarar a BBCHausa.com