Yadda aka fafata a muhawarar jihar Nasarawa

Yadda ake gudanar da muhawara tsakanin 'yan takara biyar da ke neman kujerar gwamnan jihar Nasarawa.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Kreni na YPP kan batun ilmi

    Kreni ypp ilimi ya zama abin tausayi makarantu sun lallace run daga firame don babu tsoron Allah

    An san kudade ba za su isa ba amma idan aka sanya tsoron Allah za a iya yin abin da mutane za su amfana

    Za su sa jamian gwamnati su sanya yayansu a makaransun jihar maimakon fitar da su waje

    Doma zai inganta walwalar malamai da bayar da kidaden tallafi ga dalibai

  2. Muhawara da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

    Sani Gambo Kofa: Mudai fatanmu shine Allah yabamu shuwagabanni nagari a ko wane party suke.

    Abu Abd-Allah Al-Badarawy: Tambaya ga A. A. Sule, me ya sa game da harkar noma ku ka zabi noman rake kamar yadda ka bada misali da Awe, maimakon Noman abinda mutane suka fi bukata kamar su masara, shinkafa da sauran su?

  3. An koma batun Ilmi, an fara da Nubugadu

    Nubugadu ya zai tunkari kalubalen ilimi. Idan ya zama gwamna zai gyara makarantu tare da mayar da hankali kan ilimi na sanaoi. Za iganta makarantu su biya malamai albashinsu

  4. Danjuma kreni na YPP

    Danjuma kreni. Kowa ya san akwai matsala game da dokar hako maadanai. Za su tabbatar aN sauya wannan doka idan aka cimma hakan ne za su samu yi wa alumma abubuwan da alumma za su amfana

  5. Doma na ZLP

    Doma na zlp Babu bayanai a hukumance na yawan ma'adanan da jihar ke da su. Za su yi yunkurun kawar da dokar da ta baiwa gwanatin tarayya iko akan maadanai. Za su shigo da yan kasuwa ciki

  6. Ombugadu na PDP

    Nubigadu na pdp ya ce manufofi na da amfani wajen hako makamai

    Za su duba yadda za a shiga yarjejeniya ta yadda mutanen doma da awai ta yadda za a kare muradunsu kuma za su amfani da maadanan da ake hakowa a wurarensu

  7. Sule na APC

    Sule na apc ya ce zasu kafa kamfanin taki biyar. Shekararsa biyar yana aikin hako mai a Amurka kafin yanzu. Yanzu jihar na da ma'adanai 25 za su maida hankali wajen hako mai

  8. Yadda 'yan takara ke gabatar da manufofinsu

    Har yanzu kowanne dan takara na bayyana manufofinsa kan harkar noma.

    BBCGovDebate
  9. Za a fara duba manufofin yan takara za a fara da noma

    Yanzu za a dunga kiran 'yan takara daya bayan daya su yi zawabi kan manufofin da suka tanada, inda za a fara da batun Noma tushen arziki.

  10. Umaru Aliyu Doma

    Umaru Aliyu Doma gogaggen dan kasuwa ne da ya yi karatukansa a makarantunr Kasuwanci ta Harvard Business School, da ke Boston a Amurka da kuma wata Cibiyar Fasaha a Amurka wato Massachusetts Institute of Technology.

    Ya yi karatun firamare da na sakandarensa a Baptist High School da ke Jos da kuma Corona Private School a Bukuru , duk a Jihar Filato. Dan kasuwa ne da ya fi sha'awar ayyukan noma da fasaha da harkokin yawon bude ido da sauran su. Umaru ya yi aiki a bangarori da dama a cibiyoyi masu zaman kansu.

    Shi ne shugaban kamfanjn Oriya Farms, wani kamfani na harkokin kasuwancin noma da kuma kamfanin Boltzman Engineering Ltd ,na bangaren Fasaha. Shi ne daraktan kamfanin sadarwa na BCTEK Engineering.

    Umaru ne ya kirkiri kamfanin Hyatt Consult Limited kuma shi ne shugabansa. Ya taba zama mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan Nasarawa a baya. Shi ne Garkuwan Doma kuma Ajiyan Keana. Yana da mata da yara.

    Yanzu yana takarar gwamnan Nasarawa a karkashin jam'iyyar ZLP a zaben 2019.

    BBCGovDebate
  11. Honarabul Emmanuel Ombugadu

    An haife shi ranar 10 ga Janairun 1978 Ya yi firamare a Kaduna.

    Ya yi sakandare a Kwalejin gwamnati ta Keffi 1995 Jami'ar Jos 2001 Ya karanci tsimi da tanadi Ya yi digiri na biyu a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas Dan majalisar wakilai ta tarayya.

    Ya zama dan majalisar wakiltar tarayya a 2011 zuwa 2015, ya Kuma sake maimatawa daga 2015 zuwa 2019 Yana wakiltar Nasarawan Eggon da Wamba da Akwanga.

    A yanzu yana neman takarar gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin jam'iyyar PDP a 2019

    BBCGocDebate
  12. Hon Kreni Danju Mantani

    An haife shi ne a ranar 12 ga watan Augusta 1966. Kreni dai dan asalin kabilar Mada ne dake kauyen Gbugyar a Andaha karamar hukumar Akwanga, Jihar Nasarawa.

    Yayi makarantar firamare a Andaha daga 1979-1982. Yayi sakandare a Mada Common Secondary School Andaha inda ya samu takardar SSCE a 1989.

    Yaje kwalejin horas wa ta kiwon lafiya dake Alushi a 1992 sa'annan daga baya kuma ya garzaya zuwa kwalejin horas wa ta kiwon lafiya dake Zawan a Jihar Plateau. Mr Kreni dai tsohon zabbaben kansila ne daga 2004-2007 kuma shine shugaban kungiyar masu rinjaye a wannan lokaci.

    Kreni dai yana cikin kungiyoyi da dama da suka shafi harkar kiwon lafiya kamar su NACHPN da kuma MHWUN. Haka ma dai yana cikin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC.

    BBCGovdebate
  13. Yadda za ku iya bibiyar muhawarar kai tsaye

    Za a nuna muhawarar kai-tsaye a shafukan sada zumunta da muhawara na BBC Hausa Facebook da gidan talbijin na kasa, NTA, da ke jihar Nasarawa da kuma gidan rediyon jihar.

    Kazalika akwai bayanai a shafin Twitter na @bbchausa da maudu'in #GovDebate, sannan mu wallafa hotuna da bidiyo da shafin Instagram na @bbchausa.

  14. Labaran Maku

    An haifi Labaran Maku ne dai a jihar Nasarawa a ranar 1 ga watan Janairu 1962 a Lardin Wakama dake karamar hukumar Eggon dake Jihar Nasarawa.

    Yayi karatun firamare a St. Michael Primary Aloce daga 1970-1976, sai kuma Kwalejin Malamai ta Zawan daga 1976-1981. Daga nan ne ya garzaya Jami'iar Jihar Plateau a 1983 zuwa 1987.

    Ya taba zama tsohon mataimakin gwamnan Jihar daga 2003-2007. Kafin nan dai ya zama kwamishinan watsa labarai, wasanni da matasa daga 1999-2002. Sai kuma kwamishinan watsa labarai da harkokin cikin gida daga 2002-2003..

    Daga baya ne dai ya zama karamin ministan watsa labarai a 2010.

    BBCGovDebate
  15. Abdullahi Alhaji Sule

    An dai haifi shi ne a ranar 26 ga watan December 1959 a Gudi Station dake Jihar Nasarawa.

    Gudi gari ne wanda yake cakude da kabilu masu addinai daban-daban. Abdullahi yayi karatun firamare a makarantar Katolika dake Gudi Station. Daga nan ne ya garzaya zuwa Zang Commercial Secondary dake Bukuru a 1974.

    Sai kuma daga baya ya koma makarantar koyon fasaha dake Bukuru sai kuma kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Plateau. Abdullahi dai ya samu digirin sa na farko da na biyu daga jami'ar jiha ta Indiana dake Amurka a 1983 da 1984.

    Da ya dawo Najeriya, yayi aiki da kamfanin wutar lantarki na Jihar Plateau inda daga baya ya koma aiki a kamfanin mulmula karafa dake Jos a 1989.

    BBCGovDebate
  16. Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

    Idriss Ibraheem Ibraheem: BBC kune na daya daga cikin kafa wadda take nunawa mutane yancin su muna gadiya

    Oumarou Sabonguida: Daga Yaounde cameroun muna fatan duk wanda ya dawki alkawali Allah bashi ikon cikawa da amanar aloumma.

    Umar Shuaib Jibia: Allah ya sa masu sauraro da kallon ku suyi amfani da hankali gurin abinda za'a gabatar Amin

  17. Yadda jama'a suka yi layin shiga dakin muhawara

    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
  18. Kai tsaye yadda ake gudanar da muhawarar

  19. Dukkan 'yan takara sun halarci wajen muhara

    BBCGovDebate
  20. Fadar Sarkin Lafiya, mai martaba Dr Isa Mustapha Agwai

    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
    BBCGovDebate
    BBCGovDebate