Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Senegal ta kasa kai labari

Senegal ta kasa tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya bayan Colombia ta doke ta 0-1 a wasan rukuni na karshe da suka fafata.

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan and Awwal Ahmad Janyau

  1. Sanchez ya yi wa Mane keta, Senegal 0-0 Colombia

  2. Senegal ta samu fanareti, Senegal 0-0 Colombia

  3. Colombia ta samu bugun tazara, Senegal 0-0 Colombia

    Amma golan Senegal ya fitar da kwallon

  4. Senegal ta canza salon zubin 'yan wasa, Senegal 0-0 Colombia

    A karon farko Senegal ta fara wasa da Balde da Gassama da Kouyate

  5. Senegal na matsawa Colombia, Senegal 0-0 Colombia

  6. Senegal ta samu bugun tazara, Senegal 0-0 Colombia

    Amma golan Colombia ya kama kwallon

  7. 'Yan Afirka na bayan Senegal, Senegal 0-0 Colombia

    Senegal ce kasa tilo da ta rage a Afirka da ke fatan tsallakewa zuwa zagaye na biyu.

    Idan har aka fitar da Senegal zai kasance an fitar da dukkanin kasashen Afirka daga gasar a Rasha.

  8. An fara wasa, Senegal 0-0 Colombia

  9. 'Yan wasan da za su buga wasa, Senegal 0-0 Colombia

  10. Japan na fafatawa da Poland, Japan 0-0 Poland

    Japan ma maki daya take nema

  11. Senegal tana neman maki daya, Senegal 0-0 Colombia

    Yadda matsayin Senegal yake a rukunin H.

  12. Senegal kasa tilo da ta rage a Afirka, Senegal 0-0 Colombia

    Gumurzu ne tsakanin Sadio Mane na Senegal da Rademel Falcao na Colombia.

    Dukkaninsu sun ci kwallo daya a raga a wasannin da suka gabata.

  13. An fito fili, Senegal 0-0 Colombia

  14. Yadda 'yan wasan Senegal suka isa fili, Senegal 0-0 Colombia

  15. Barka da shigowa wannan shafin, Senegal 0-0 Colombia

    Jama'a, barkanku da shigowa wannan shafin inda za mu kawo muku fafatawar Senegal da Colombia.