Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Senegal ta kasa kai labari

Senegal ta kasa tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya bayan Colombia ta doke ta 0-1 a wasan rukuni na karshe da suka fafata.

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan and Awwal Ahmad Janyau

  1. Japan ta koma ta uku, Senegal 0-0 Colombia

  2. Mane ya dirka kwallon a sama, Senegal 0-0 Colombia

  3. Senegal ta samun bugun tazara, Senegal 0-0 Colombia

    Sanchez ne ya buge Sadio Mane a kusa da harabar Colombia

  4. Bednarek ya ci wa Poland, Senegal 0-0 Colombia

    Yanzu Japan na fuskantar barazana

  5. Poland ta ci Japan, Senegal 0-0 Colombia

  6. Senegal na kokarin kai hari

    Senegal 0-0 Colombia

    Senegal na kokarin kai hari. Sai dai kuma 'yan wasan suna komawa baya.

  7. Senegal na bukatar taka-tsan-tsan

    Senegal 0-0 Colombia

    Tun da aka dawo daga hutun rabin lokaci dai Colombia ta fi rike kwallo. Ya kamata Sengal kada ta yi sake a sha ta.

    Amma yanzu Senegal din ta so ta kai hari... kafin lafiri hura 'off-side.'

  8. Mane ya kai wata kora, Senegal 0-0 Colombia

    Amma Idrissa ya yi satar gida bayan Sadio Mane ya kai ma shi kwallo

  9. Niang (Senegal) ya karbi kati, Senegal 0-0 Colombia

  10. Senegal wakiliyar Afirka, Senegal 0-0 Colombia

    Senegal ce kasa ta karshe daga Afirka da ta rage a gasar cin kofin duniya

  11. Wasan rukuni na karshe, Senegal 0-0 Colombia

    Wannan ne wasan rukuni na karshe da ake fafatawa tsakanin Senegal da Colombia

    Japan kuma da Poland.

  12. Babu ci har yanzu, Senegal 0-0 Colombia

    Japan 0-0 Poland

  13. An dawo, Senegal 0-0 Colombia

  14. Yadda Senegal da Colombia suka yi gumurzu, Senegal 0-0 Colombia

  15. Japan a sama, Senegal na biye da ita

    Hutun rabin lokaci: Senegal 0-0 Colombia

    Japan tana saman teburi. Senegal na biye da ita. Colombia da Poland za su koma gida.

    Haka teburin zai kasance idan ba a ci kwallo ba a daya daga cikin wasannin.

  16. Colombia ta fi taba kwallo, Senegal 0-0 Colombia

    Amma Senegal ta fi kai hare-hare.

  17. Japan 0-0 Poland, Senegal 0-0 Colombia

    Idan an tashi haka Senegal ta tsallake zuwa mataki na gaba da maki biyar.

  18. An tafi hutun rabin lokaci, Senegal 0-0 Colombia

  19. An kara minti uku kafin hutun rabin lokaci, Senegal 0-0 Colombia

  20. Mojica ya karbi kati, Senegal 0-0 Colombia

    Dan wasan Colombia Mojica ya karbi katin gargadi