Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Senegal ta kasa kai labari

Senegal ta kasa tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya bayan Colombia ta doke ta 0-1 a wasan rukuni na karshe da suka fafata.

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan and Awwal Ahmad Janyau

  1. Sai wani lokacin

    A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo mu ku kai tsaye.

    Mu hadu a wasannin zagaye na biyu da za a fafata a gasar cin kofin duniya a Rasha.

    Sai wan lokacin.

  2. Colombia da Japan sun tsallake, Senegal 0-1 Colombia

  3. Ta faru ta kare, Senegal 0-1 Colombia

    An fitar da Senegal, kasa ta karshe da ta rage a Rasha daga Afirka.

    Yanzu za a buga zagaye na biyu babu kasa daya daga Afirka.

  4. An tashi, Senegal 0-1 Colombia

    Colombia ta samu sa'ar Senegal 0-1

  5. Saura minti daya, Senegal 0-1 Colombia

    Senegal na bukatar ta ci kwallo

  6. An kara minti hudu, Senegal 0-1 Colombia

  7. Colombia ta yi canji, Senegal 0-1 Colombia

    Borja ya karbi Falcao

  8. Sai Senegal ta yi da gaske, Senegal 0-1 Colombia

    Saura minti biyu lokaci ya cika

  9. Senegal ta yi canji, Senegal 0-1 Colombia

    Sakho ya karbi Niang

  10. Yadda Mina ya ci Senegal, Senegal 0-1 Colombia

  11. Colombia ta yi canji, Senegal 0-1 Colombia

    Lerma ya karbi Uribe

  12. Saura Minti 10, Senegal 0-1 Colombia

    Senegal na kokarin ta farke

  13. Japan da Senegal wa zai tsallake?, Senegal 0-1 Colombia

    Japan da Senegal dukkaninsu yanzu suna a maki hudu, kuma ba banbanci a yawan kwallaye.

    Wata kila za a diba kasar da tafi karbar katin gargadi.

  14. Senegal ta samu kwana, Senegal 0-1 Colombia

    Mane ya yi kokarin sa kai amma Golan Colombia ya kame kwallon

  15. Saura kiris Senegal ta rama, Senegal 0-1 Colombia

  16. Senegal na cikin hatsari, Senegal 0-1 Colombia

  17. Colombia ta ci Senegal, Senegal 0-1 Colombia

    Mina ne ya zura kwallon a ragar Senegal a bugun kwana

  18. Colombia, Senegal 0-1 Colombia

  19. Saura Minti 20, Senegal 0-0 Colombia

  20. Yadda Jan Bednarek ya ci Japan, Senegal 0-0 Colombia

    Colombia za ta tsallake Idan ta tashi babu ci da Senegal bayan Poland ta sha Japan.