Labarin wasanni daga 20 zuwa 26 ga watan Disamba 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 13 zuwa 19 ga watan Disambar 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Hakimi ya murmure daga jinya zai buga wa Morocco Afcon

    Hakimi

    Asalin hoton, Getty Images

    Wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon kafa na bana na Afirka, Achraf Hakimi ya warke daga jinya, zai kuma buga wa Morocco gasar cin kofin nahiyar Afirka da za ta gudanar, kamar yadda ya sanar ga manema labarin wasanni ranar Asabar.

    Tun farko an yi tantamar da ƙyar ne idan ƙyaftin din zai yi wa Morocco wasannin, bayan raunin da ya ji a karawa da Paris St Germain ta yi rashin nasara a hannun Bayern Munich a Champions League a Faransa a watan jiya.

    Tun daga lokacin ake cewa ba zai warke da wuri ba, amma kuma mai shekara 27 ya sanar da bakinsa cewar ya warke a kuma lokacin da za a yi bikin fara wasannin ranar Lahadi 21 ga watan Disamba.

    Morocco mai masaukin baƙi za ta fara wasa a rukunin farko da Comoros a Rabar ranar Lahadi, amma ba a fayyace ko za a fara wasan da Hakimi ba.

    An bayyana mai tsaron bayan a matakin gwarzon ɗan ƙwallon kafar Afirka na bana a watan jiya a Rabat, ya kuma karɓi ƙyautar tare da sandunan dogarawa, sakamkon aiki da aka yi masa a kafarsa.

    Sai dai kuma tawagar Morocco ta bayyana shi cikin ƴan ƙwallon da za su buga mata babbar gasar tamaula ta Afirka.

  2. Ko Man City za ta ɗare kan teburin Premier zuwa Kirsimeti?

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a fara wasannin mako na 17 a gasar Premier ta kasar Ingila a ranar Asabar, inda za a yi karawa bakwai.

    Arsenal ce a saman teburi, amma idan ta yi kasassaba za ta iya tsintar kanta a ta biyu kasancewar maki biyu ne kawai ya raba ta da Manchester City wadda take taka rawar gani a baya-bayan nan.

    Kawo yanzu an buga wasa 160 da cin ƙwallo 457, kuma Erling Haaland na Manchester City shi ne kan gaba mai 17 a raga, bayan kammala wasannin mako 16.

  3. Wasannin Premier League mako na 17, Premier League

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Asabar 20 ga watan Disamba

    • Newcastle da Chelsea
    • Wolves da Brentford
    • Bournemouth da Burnley
    • Brighton da Sunderland
    • Man City da West Ham
    • Tottenham da Liverpool
    • Everton da Arsenal

    Ranar Lahadi 21 ga watan Disamba

    • Leeds da Crystal Palace
    • Aston Villa da Man Utd

    Ranar Litinin 22 ga watan Disamba

    • Fulham da Nottm Forest
  4. Salah ya bai wa ƴan wasan Liverpool hakuri - Jones

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya bai wa taƙwarorinsa hakuri, bayan kalaman da ya yi sakamakon ransa da ya ɓaci a baya in ji Curtis Jones.

    A wata hira da ya yi da ƴan jarida ya bayyana ɓacin ransa da cewar ana ɗora alhakin rashin kokarin ƙungiyar a bana a kansa, ya kuma ce dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da kociya, Arne Slot.

    Dan ƙwallon tawagar Masar ya yi waɗan nan kalaman ana tashi daga wasan da Liverpool ta tashi 3-3 da Leeds United a Premier League, bayan da ya ɗumama benci.

    Daga nan Liverpool ba ta je da shi Inter ba a Champions League, sai dai ya koma buga mata wasa a karawar da ta ci Brighton a Anfield a Premier League.

    Salah ne tilo daga Liverpool da zai buga gasar cin kofin Afirka da za a fara ranar Lahadi a Morocco.

    Salah wanda bai taɓa lashe Afcon ba, za su fara fuskantar Zimbabwe ranar Litinin 22 ga watan Disamba.

  5. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.