Labarin wasanni daga 20 zuwa 26 ga watan Disamba 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 13 zuwa 19 ga watan Disambar 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Sir Ben Ainslie sun mallaki Oakley Capital

    Sailing

    Asalin hoton, Getty Images

    Sir Ben Ainslie, wanda shi ne mafi nasarar a wasan tseren jirgin ruwa a tarihin Olympics, tare da Athena Racing Team, sun sanar da cewa sun samu jarin mallakar Oakley Capital, wanda zai ba su damar shiga gasar America Cup a gasar gaba.

    A bara, Sir Ben da tawagarsa ta Birtaniya sun kai zagayen ƙarshe a gasar.

    Haka kuma, an sanar da sabuwar Haɗin Gwiwar America’s Cup tsakanin ƙungiyoyi biyar da suka kafa gasar, wadda za a kashe kuɗi na miliyan 55 daga shekarar 2029.

  2. Howe na neman dalilin da ba a ba su fenariti a wasan Chelsea ba

    Gordon

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Newcastle United, Eddie Howe, ya ce za su tuntuɓi hukumar alkalan wasan Premier League – PGMOL – game da hukuncin da aka yanke na rashin bai wa Anthony Gordon bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan da suka buga da Chelsea.

    Howe ya yi ikirarin cewa an hana Newcastle bugun fenareti karara a wasan Premier League da suka tashi 2-2 a ranar Asabar a filin St James’ Park, bayan Trevoh Chalobah ya tunkuɗe Anthony Gordon ya fadi a ƙasa.

  3. Alexander Isak zai yi jinyar watanni - in ji Slot, Liverpool

    Isak

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Liverpool, Arne Slot ya ce Alexander Isak zai yi jinyar watanni, sakamkon ƙetar da ɗan wasan Tottenham, Micky van de Ven ya yi masa ranar Asabar.

    Isak, wanda shi ne ya ci Liverpool wasan farko da ta yi nasara a kan Tottenham 2-1 ya karya kafa a wasan.

    Hakan ya sa ya shiga jerin wasu ƴan wasan Liverpool da ke jinya, koda yake ana cewar Cody Gakpo ya murmure zai iya buga wasan Wolves.

    Shima Jeremie Frimpong ya warke har ma ya buga mata wasan Tottenham, inda Slot ya ce zai fara wasan da shi.

    Sai dai Slot ya yi watsin batun yi wa Harvey Elliot kiranye, wanda ke buga wasannin aro, domin ya kara karfin Liverpool.

  4. An ci tarar Finch a lokacin gasar ƙwallon NBA ta Amurka, Gasar NBA

    Babban kocin Minnesota Timberwolves, Chris Finch, an ci tararsa dala $35,000 saboda abin da ya aikata a wasan da ƙungiyarsa ta doke Oklahoma City Thunder da maki 112–107 ranar Juma’a, kamar yadda NBA ta sanar.

    Finch, mai shekaru 56, ya nuna matuƙar fushi tun farkon wasan sakamakon laifukan da ‘yan wasan Thunder suka yi, inda alƙalai ba su busa laifuka a kansu ba.

    An fara da jan kunnensa karo biyu sai aka kore shi daga wasan tun kafin a kai tsakiyar zangon farko.

  5. Paul ya ce zai ci gaba da damben boksin da waɗanda suka fi karfinsa, Jake Paul da Anthony Joshua

    Paul Anthony

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan YouTube da ya koma dambe, Jake Paul, ya ji rauni an kuma cire wasu haƙoransa, bayan da Anthony Joshua ya karya masa muƙamuƙi a fafatawar da suka yi ranar Juma’a.

    Damben da aka yi a birnin Miami ta kai zagaye shida, amma an dakatar da wasan ne bayan da ake ta yi wa Paul bugun da ke kaishi ƙasa sau da dama.

    Wasan ya jawo suka daga mutane da dama saboda banbancin girman jiki da kuma tazarar kwarewa tsakanin yan wasan biyu.

    Paul ya ce zai ɗan ɗauki lokaci yana hutu daga dambe, amma yana da niyyar dawowa domin ya fafata da mutane da suka fi karfinsasa.

  6. Arteta zai fara wasa da Jesus karon farko bayan kwana 345, Gabriel Jesus

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Mikel Arteta ya ce ya shirya fara wasa da Gabrriel Jesus a karon farko bayan 345 da ya buga wa Arsenal fafatawar Carabao Cup zagayen kwata fainal a karawa da Crystal Palace.

    Arsenal za ta fuskanci ƙungiyar da Oliver Glasner ke jan ragama a Emirates ranar Talata, yayin da Arteta ke fatan lashe kofin Premier League a karon farko daga kaka shida a Gunners.

    Jesus ya ci Palace kwallo uku rigis a bara a zagayen ƴan takwas daga baya ne Newcastle United ta yi waje da Gunners a daf da karshe a League Cup.

    Ɗan ƙwallon tawagar Brazil ya yi jinyar wata 11, bayan da ya ji rauni a gwiwa.

    Sai dai ya murmure a kwanan nan, har ma ya canji ɗan wasa a karawar da Arsenal ta yi da Club Brugge a Champions League da Wolves da Everton a Premier League.

    Kenan Arteta na bukatar Jesus a karawa da Palace, bayan da ƙungiyar za ta yi wasa shida cikin kwana 20.

  7. Liverpool na fargabar girman raunin Isak, Alexander Isak

    Isak

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool na fargabar cewa Alexander Isak ya samu mummunan rauni a ƙasan ƙafarsa, lokacin da ƙungiyar Anfield ta yi nasara 2-1 a gidan Tottenham a gasar Premier League ranar Asabar.

    Dan wasan tawagar Sweden ya shiga wasan bayan da ya fara daga zaman daga baya Micky van de Ven ya yi masa ƙeta.

    An yi wa mai shekara 26 gwaje-gwaje, domin tantance girman raunin da ya ji.

  8. Ba yanzu zan sa ran lashe Premier ba - Emery, Aston Villa

    Unai Emery

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Aston Villa, Unai Emery ya ce ba zai fara tunanin ko ƙungiyarsa na cikin masu fafatan lashe kofin Premier League ba sai zuwa karawar mako na 34 a kakar bana, ba a halin yanzu ba.

    Aston Villa ta rage tazarar maki tsakaninta da wadda take kan tebur Arsenal zuwa maki uku kacal, bayan ta doke Manchester United da ci 2–1 a Villa Park ranar Lahadi.

    Villa za ta kara da Chelsea wadda ke matsayi na huɗun teburi, sannan za ta je wasa da Arsenal a Emirates a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

  9. Mako huɗu za a fafata a gasar kofin Afirka a Morocco, Afcon Morocco 2025

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan watanni na shirye-shiryen gudanar da gasar cin kofin ƙasashen Afirka (AFCON) tuni aka yi bikin fara wasannin ranar Lahadi a birnin Rabat, inda Morocco mai masukin baƙi ta doke Comoros 2-0 a rukunin farko.

    Ƙungiyoyi 24 za su kece raini a gasar da za a yi birane guda shida a filayen wasa tara a ƙasar da ke da tsananin sha’awar ƙwallon ƙafa.

    Za a yi mako huɗu aka tata ɓurza a wasannin, kuma za ta yi ta yi gwaji a wasannin kafin gasar cin kofin duniya ta 2030, inda Maroko ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da za su karɓi baƙunci.

    Hakan ya sa masarautar kasar ta fara shirye-shiryen gina manyan kayayyakin more rayuwa mafi girma a tarihin wasannin motsa jiki na Afirka domin shiri da take yi kafin gasar kofin duniya da za ta yi hadaka da Sifaniya da kuma Portugal.

    Mai rike da kofin, Ivory Coast, tana fatan kare kofin da ta lashe a 2023, yayin da Najeriya za ta yi fatan wuce matakin da ta kai bayan rashin nasara a wasan karshe a hannun Ivory Coast.

    Senegal ta Sadio Mané tana cikin wasannin bayan lashe gasar shekarar 2021, yayin da Masar ke fatan rade-radin makomar Mohamed Salah ba zai ɗauke hankalin tawagar ba daga neman lashe kofi na takwas jimilla a nahiyar, wanda zai zama sabon tarihi.

    Ga jerin rukunin kasashen da za su buga Afcon a Morocco:

    Rukunin farko: Morocco, Mali, Zambia, Comoros

    Rukuni na biyu: Egypt, South Africa, Angola, Zimbabwe

    Rukuni na uku: Nigeria, Tunisia, Uganda, Tanzania

    Rukuni na huɗu: Senegal, DR Congo, Benin, Botswana

    Rukuni na biyar: Algeria, Burkina Faso, Equatorial Guinea, Sudan

    Rukuni na shida: Kamaru, Gabon, Ivory Coast da kuma Mozambique

    An fara gasar cin kofin Afirka a Morocco ranar 21 ga watan Disambar 2025 za kuma a karkare ranar 18 ga watan Janairun 2026.

  10. Za a buga wasa na biyu a Afcon tsakanin Mali da Zambia

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Mali da Zambia za su kece raini a wasa na biyu a gasar cin kofin Afirka a Morocco ranar Litinin karawar rukunin farko at Stade Mohammed na biyar a Casablanca.

    Wasan baya da suka fuskanci juna a Afcon shi ne a zagayen daf da karshe a 1994 ranar 6 ga watan Afirilu a Stade El Menzah a birnin Tunis, Tunisia, kenan bayan shekara 31 da ta wuce.

    Zambia ce ta yi nasarar cin Mali 4-0, kuma ta zura ƙwallayen ta hannun Elihah Litana da Zeddy Saileti da Kalusha Bwalya da kuma Kenneth Malitoli.

    Shi ne karo na biyu da aka zura ƙwallaye da yawa a ragar Mali a Afcon da wanda Morocco ta doke ta 4-0 a zagayen daf da karshe a 2004.

    Zambia ce ta lashe babban kofin tamaula na Afirka a 1994.

    Jimilla tawagogin biyu sun fuskanci juna sau shida, Zambia ta yi nasara biyu da Mali da ta ci wasa ɗaya da karawa uku canjaras.

    Tuni mai masukin baki Morocco ta fara da cin Comoros 2-0 ranar Lahadi, bayan da aka kammala shagulgula buɗe gasar a birnin Rabat.

  11. Morocco ta fara Afcon da kafar dama da cin Comoros, Morocco 2-0 Comoros

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar ƙwallon kafa ta Morocco ta doke ta Comoros 2-0 a wasan farko a gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka kara ranar Lahadi a birnin Rabat ranar Lahadi.

    Tun farko sun je hutu ba ci, sai da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne mai masaukin baƙin ta ci biyu.

    Brahim Diaz ne ya fara zura ta farko a raga daga baya Ayoub El Kaabi ya ci ta biyu mai kayatarwa.

    Wannan shi ne karo na 19 da Morocco ta ci wasa a jere.

    Wasannin da za a buga ranar Litinin:

    Ranar Litinin 22 ga watan Disamba

    Rukunin farko

    • Mali da Zambia

    Rukuni na biyu

    • Afirka ta Kudu da Angola
    • Masar da Zimbabwe
  12. Barcelona za ta kare 2025 a kan ragamar teburin La Liga

    Lamine Yamal

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ta je ta doke Villareal a wasan mako na 18 a gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi.

    A minti na 12 da fara take leda Barcelona ta fara cin ƙwallon farko a bugun fenariti ta hannun Raphinha daga baya Lamine Yamal ya kara na biyu.

    Villareal, wadda ta ci wasa shida baya a La Liga ta kare karawar da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Renato Veiga jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Yamal.

    Barcelona za ta kammala La Liga a 2025 a matakin farko a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta yi.

    Yanzu haka za a je hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara a La Liga, yayin da Barcelona za ta buga wasan gaba da Espanyol ranar 3 ga watan Janairun 2026, ita kuwa Villarreal za ta je Elche a dai ranar.

  13. Kano Pillars ta doke Plateau United a jihar Katsina

    Kano Pillars

    Asalin hoton, Getty Images

    Kano Pillars ta doke Plateau United 2-1 a wasan mako na 18 a gasar Premier League ta Najeriya da suka kara ranar Lahadi a jihar Katsina.

    Wisdom Ndon ne ya fara ci wa Plateau United ƙwallo a minti na 13 da take leda, kafin hutu Pillars ta farke ta hannun Mustapha Jibrin.

    Ana komawa zagaye na biyu ne Pillars ta kara ta hannun Ahmed Musa.

    Da wannan sakamakon Pillars, wadda take ta karshen teburi ta 20 da maki 16 ta ci wasa na biyar kenan da canjaras huɗu aka doke ta tara daga cikin, bayan wasannin mako na 18.

    Ita kuwa Palateau United mai maki 19 tana tana ta 18 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Najeriya.

    Sakamakon wasannin da aka buga ranar Lahadi:

    • El Kanemi Warriors 3-2 Enyimba
    • Kano Pillars 2-1 Plateau United
    • Abia Warriors 1-0 Warri Wolves
    • Enugu Rangers International 2-1 Ikorodu City
    • Kwara United 2-0 Bayelsa United
    • Remo Stars 2-3 Bendel Insurance
    • Shooting Stars 2-1 Niger Tornadoes
    • Wikki Tourists 0-0 Kun Khalifat

    Wasan da za a buga ranar Litinin:

    • Katsina United da Rivers United
    • Nasarawa United da Barau FC
  14. Christensen ya kara cin karo da cikas a Barcelona

    Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan Barcelona Andreas Christensen ya ji rauni, kamar yadda ƙungiyar ta sanar ranar Lahadi, yayin da rahotani daga kafafen yaɗa labarai na Sifaniya ke cewa ɗan wasan tawagar Denmark na iya jinya watanni.

    Christensen, wanda ya ji rauni a watan Oktoba har ta sa ya yi jinyar makonni biyu, ya ji ciwo a wannan karon ranar Asabar a wajen Atisaye.

    Dan wasan mai shekara 29 ya fara dukkan wasannin da Denmark ta buga na neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya na bana, inda ya zura kwallo guda ɗaya da bayar da biyu aka zura a raga, yayin da suka kare a matsayi na biyu a rukuninsu, hakan ya ba su damar shiga wasannin cike gurbi daga nahiyar Turai.

    Denmark za ta kara da Arewacin Macedonia ranar 26 ga Maris a wasannin cike gurbin, inda ta ci wasan sai ta fuskanci Jamhuriyar Czech ko kuma Ireland, domin neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya da za a buga a watan Yuni a Amurka da Canada da kuma Mexico.

  15. Kyrgios zai buga ATP tour a karon farko bayan wata 10, ATP Tour

    Nick Kyrgios

    Asalin hoton, Getty Images

    Nick Kyrgios na dab da buga wasansa na farko a Gasar ATP Tour cikin wata 10, bayan da aka yi masa alfarma a wasannin da za a yi a Brisbane International a watan gobe.

    Rashin koshin lafiya ya sa wasa biyar ya yi a Australian Open a 2025, inda wasansa na ƙarshe ya yi rashin nasara a zagaye na biyu a hannun Karen Khachanov a Miami Open a watan Maris.

    Kafin gasar Brisbane, zai fafata da Aryna Sabalenka, wadda ke rike da matsayi na ɗaya a duniya a bangaren mata, a wasan tenis tsakanin mace da namiji da za su kara ranar 28 ga Disamba.

  16. Atletico za ta kare cikin ƴan huɗun teburin La Liga a 2025, Atletico Madrid 3-0 Girona

    Atletico Madrid

    Asalin hoton, Getty Images

    Atletico Madrid ta je ta doke Girona 3-0 a gasar LaLiga da suka buga a ranar Lahadi - ta ci ƙwallayen ta hannun Koke da Conor Gallagher da kuma Antoine Griezmann wanda ya shiga karawar daga baya.

    Kenan Atletico ta yi nasara ta huɗu a jere a dukkan wasannin da ta buga a baya bayan nan.

    Da wannan sakamakon Atletico ta yi sama zuwa mataki na uku a kan teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakani da Villareal, wadda take da kwantai uku tana kuma fafatawa da Barcelona ranar Lahadi.

    Girona, wadda ke fuskantar barin La Liga a karshen kakar bana, wadda wasa ɗaya ta ci daga biyar baua ta ci gaba da zama ta 18 a kasan teburin gasar.

    Wasan gaba da Atletico za ta yi shi ne a gidan Real Sociedad ranar 4 ga watan Janairu kwana biyar tsakani ta buga wasan hamayya da Real Madrid a Spanish Super Cup.

  17. Ƴan wasan Aston Villa da na Man United da za su buga Premier, Aston Villa da Manchester United

    Aston Villa ta karɓi bakuncin Manchester United a wasan mako na 17 a Premier League da za su fafata ranar Lahadi a Villa Park.

    Villa tana mataki na uku a kan teburin Premier da maki 33, ita kuwa United tana ta bakwai da maki 26.

    Ƴan wasan Aston Villa: Martinez, Cash, Konsa, Lindelof, Maatsen, Kamara, Onana, McGinn, Tielemans, Rogers, Watkins.

    Masu jiran ko-ta-kwana: Bizot, Buendia, Digne, Garcia, Malen, Bogarde, Guessand, Hemmings, Routh.

    Ƴan wasan Manchester United: Lammens, Yoro, Heaven, Shaw, Dalot, Ugarte, Fernandes, Dorgu, Cunha, Mount, Sesko.

    Masu jiran ko-ta-kwana: Bayindir, Heaton, Martinez, Zirkzee, Malacia, Fredricson, Fletcher, Lacey, Mantato.

    Alkalin wasan: Michael Oliver (Northumberland)

  18. Liverpool na fargabar Isak ya ji mummunan rauni, Liverpool

    Isak

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool na fargabar cewa Alexander Isak ya samu mummunar rauni a wasan da ta doke Tottenham 2-1 a gasar Premier League ranar Asabar.

    Dan ƙwallon tawagar Sweden ya fara daga zaman benci daga baya aka sa shi a wasan, kuma shi ne ya fara cin ƙwallon farko.

    Daga baya ne Micky van de Ven ya yi masa ketar da dole ya hakura da fafatawar a gidan Tottenham

    Dan wasan mai shekara 26, wanda ya koma Liverpool daga Newcastle kan fara kakar nan kan kuɗin mafi tsada a tarihin Premier League na fam miliyan 125, za a ci gaba da yi masa gwaje-gwaje, domin tantance girman raunin da ya ji.

    Sai an kammala gwaje-gwajen ne, sannan za a tantance lokacin da zai yi jinya da ranar da zai koma taka leda.

  19. Afcon 2025: Me ya sa wasannin cikin watan Disamba?

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a fara buɗe labulen gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar Lahadi 21 ga watan Disambar 2025 a birnin Rabat a Morocco - to sai dai me ya sa za a buga wasannin a cikin watan Disambar.

    Tun farko an tsara gudana da gasar a tsakiyar shekara, domin rage kalubalen jadawali domin ya saɓa da wasannin gasar Turai.

    An yi niyyar fara ta lokacin bazara domin bunƙasa yawon buɗe ido tare da nuna abin da Moroko ke da shi, kafin ƙasar ta karɓi bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya a 2030 tare da Sifaniya da Portugal.

    Sai aka canja lokacin da ya kamata ta shirya gasar zuwa Disamba domin samun damar buga Fifa Club World Cup a Amurka da aka yi a lokacin bazara.

    Haka kuma gudanar da Afcon cikin watan Disamba zai sa ba a ci karo da wasannin cin kofin zakarun Turai ba wato Champions League da Europa League waɗanda za a ci gaba da fafatawa daga 20 zuwa 22 ga Janairun 2026.

    Wannan ne karon farko da za a gudanar da Afcon a wannan lokacin a cikin Disamab, yayin da Morocco ta shara yin wasanni a manyan biranenta da ya haɗa da Rabat da Casablanca da Marrakech da Agadir da Tangier da kuma Fez.

    Ana san kammala Afcon ranar 18 ga watan Janairun 2026, kuma ba a buga gasar ba ranar 25 ga watan Disamba, kenan ranar Kirsimeti.

  20. Lawandowski zai buga wasa da Villareal Pedri na jinya

    Lewandowski

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Barcelona, Robert Lewandowski ya warke zai buga gasar La Liga a gidan Villareal ranar Lahadi, in ji koci, Hansi Flick.

    Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu mai rike da kofin bara.

    Lewandowski bai buga wa Barcelona karawa biyu baya ba, sakamakon jinya da ya sha.

    Pedri, wanda shima ke jinyar bai yi wa Barcelona wasan da ta doke Guadalajara a Copa ​del Rey ba zagayen ƙungiya 32.

    Wasan da Barcelona za ta ziyarci Villareal, wadda take ta ukun teburi, shi ne na karshe daga nan a yi hutun Kirsimeti, kuma Flick ya ce yana fatan a karkare shekarar nan da tazarar maki bakwai tsakaninsa da Real.

    A kakar da ta gabata Flick ya ja ragamar Barcelona ta lashe La Liga da Copa ‍del Rey da kuma Spanish Super Cup.