Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 12/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonni abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin kawo muku wasu sabbin labaran.

    Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. PDP ta kafa kwamiti sulhu ƙarƙashin Saraki

    Abubakar Bukola Saraki

    Asalin hoton, Abubakar Bukola Saraki

    A yau ne kwamitin amintattun babbar jam'iyyar ta Najeriya wato PDP ta rantsar da kwamitin sulhu mai ɗauke da mutum 20 a wani mataki na ƙara haɗa kan ƴan jam''iyyar a matakai daban-daban na ƙasar.

    Shugaban kwamitin amintattun PDP, Adolpus Wabara ya ce nan ba da jimawa ba jam'iyyar za ta kawo ƙarshen ka-ce-na-cen da ya dabaibaye ta tsawon lokaci, tare da ɗaukar matakai kan masu yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.Ya ce wannan matakin zai ƙara tabbatar da cewa "waɗanda ke ficewa daga jam'iyyar da ma su ne matsalar jam'iyyar," inda ya ƙara da cewa yanzu iya halastattun ƴan PDP ne suka rage a cikinta.

    Ƴan kwamitin sun haɗa da tsohon gwaman Kano, Mallam Ibrahim Shekarau da tsohon gwamnan Neja Mu'azu Babangida Aliyu, da tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom da kuma Yakubu Garaba Lado daga jihar Katsina.

    Jam'iyyar PDP ta ɗauki lokaci tana fama da rikicin cikin gida tun bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

    Shugaban sabon kwamitin, Abubakar Bukola Saraki ya wallafa a shafinsa na Facebook zaman taron ya yi armashi, sannan kwamitinsa zai yi aiki tuƙuru domin tabbatar da sun je babban taron jam'iyyar cikin lumana.

  3. Najeriya ta tabbatar da kammala biyan IMF bashin Covid-19 na dala biliyan 3.4

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

    Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da kammala biyan bashin da ta karɓo daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF na dala biliyan 3.4 domin yaƙi da annobar Covd-19 a ƙasar.

    Ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ne ya tabbatar da haka ranar Litinin, a lokacin jawabin da ya yi wa manema labarai, jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa a fadar gwamnatin ƙasar.

    ''Za mu iya tabbatar da cewa Najeriya ta fice daga ƙangin bashin IMF, kuma abin da hakan ke nufi shi ne mun kammala biyan bashin da Asusun ke bin ƙasarmu'', kamar yadda Ministan ya bayyana.

    A makon da ya gabata ne labarin kammala biyan bashin ya bayyana bayan da Asusun ya fitar da wani rahoto na jerin ƙasashen da yake bin su bashi.

    To sai dai tun daga lokacin Najeriya ba ta sanar da haka a hukumance ba.

    Masana sun ce matakin wani yunƙuri ne na tabbatar da nasarar ƙasar a fannin tsare-tsaren tattalin arzikinta.

  4. Fafaren fatar Afirka ta Kudu 49 sun isa Amurka a matsayin ƴangudun hijira

    Fararen fata

    Asalin hoton, EPA

    Fararen fata 'yan Afirka ta Kudu 49 sun isa Amurka inda gwamnatin Ƙasar ta amince da shigarsu a matsayin 'yangudun hijira.

    Shugaba Donald Trump, ya ce fararen fatar - wanɗanda manoma ne - ana kai musu hari wani lokacin ma a kashe su sannan a kwace musu gonakinsu.

    Gwamnatin Afirka ta Kudu ta musanta ikirarin na Turmp, tana mai cewa rahoton ƴansanda ya musanta iƙirarin.

    Gwamnatin Shugaba Trump ta daƙile bai wa ƴangudun hijira gurbin karatu ciki har da waɗanda suka je daga ƙasashen da ake yaƙi.

    Dangantaka tsakanin Afirka ta Kudu da Amurka ta yi tsami tsawon watanni saboda sukar da Afirka ta Kudun ke yi wa Isra'ila a kan yaƙin da ta ke a Gaza.

  5. Wike ya gargaɗi PDP kan bai wa arewa takarar shugaban ƙasa a 2027

    Nyesom

    Asalin hoton, BBC Pidgin

    Ministan babban birnin tarayyar Najeriya, Nyesom Wike y ace ya ja hankalin jam’iyyar PDP kan yunƙurin miƙa takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2027 ga yankin arewacin ƙasar.

    Nyesom ya yi gargaɗin ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai ranar Litinin, inda y ace “me zai hana a matsayinta na jam’iyya ta fito fili ta ce ɗantakarar shugabancin ƙasarmu na 2027 zai fito daga kudanci?

    “Ba sa son su yi hakan. Sun fi son su yi irin abin da suka yi a 2023. Tsarin ba zai je ko’ina ba. Wannan wayon ba zai kai ku ko’ina ba. Ku fito fili ku shaida wa duniya inda kuka dosa. Ba zai yiwu kai takarar zuwa arewa ba. Na faɗa musu. Son rai zai iya kashe kowane irin tsari.

    Misali, idan shugaban ƙasa ya tsaya takara kuma ya samu nasara a zaɓen 2027, to a 2031 APC za ta mayar da takarar arewa ne.” In ji Nyeson Wike.

  6. Ƴan hamayya na fargabar rusa jam'iyyun siyasa a Mali

    Kwamitin tsara dokoki da gwamatin mukin soji Mali ta ta kafa ya ɗauki wani ƙudiri da masu suka ke fargabar cewa zai iya kai wa ga rusa duka jam'iyyun siyasar ƙasar.

    A farkon wannan watan ne, aka samu ƴar zanga-zangar goyon bayan dimokraɗiyya a Bamako, babban birnin ƙasar.

    daga baya kuma shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Assimi Goita, ya sanar da dakatar da duka wasu ayyukan da suka shafi jam'iyyun siyasa a ƙasar.

    A makon da ya gabata ne wasu mutane riƙe da makamai da suka yi iƙirarin cewa jamai'an ƴansanda ne suka yi garkuwa da shugabannin adawa biyu a ƙasar.

    A baya-bayan wani taron tuntuɓa da aka gudanar - wanda mafi yawan jam'iyyu suka ƙaurace wa - ya bayar da shawaar ɗage zaɓukan asar tare da amincewa Janar Goita ya ci gaba da mulki har nan da shekara biyar masu zuwa.

  7. Ƴan'adawa na sukar Ganduje kan kalamansa na son Najeriya ta koma tsarin jam'iyya guda

    Shugaban Jam'iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje

    Asalin hoton, Aminu Dahiru Ahmed/Facebook

    Shugaban jam’iyyar APC na ci gaba da shan suka da caccaka bayan wasu kalamai da ya yi cewa babu matsala idan Najeriya ta koma tsarin jam’iyya ɗaya.

    Kalaman da Abdullahi Umar Ganduje, ya yi cewa idan duk jam'iyyun siyasar ƙasar za su narke su koma APC, suna maraba da hakan, to sai dai 'yan adawa na cewa kalaman Ganduje tamkar yi wa tsarin dimokraɗiyya karan tsaye ne.

    Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya ce bai yi mamaki da kalaman na Ganduje ba, saboda a cewarsa bai san darajar dimokraɗiyya ba, ballantana wanzuwar jam'iyyun siyasa a tsarin.

    ''Tsarin (Dimokraɗiyya) ya yi wa Ganduje alfarma, amma ya kasa rungumar tsarin... saboda haka waɗannan abubuwa da yake yi a akwai mamaki, abin da ya samar da kai, har ya ɗaga darajarka har ka zama wani, amma a ce da shi ake yaƙi'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa tsarin da Gandujen ke son Najeriya ta koma, tsari ne da ko a ƙasashen da suka ci gaba irin Amurka da Ingila ba a yinsa.

    A baya-bayan nan dai an riƙa samun sauyin shekar jam'iyyar hamayya zuwa APC mai mulki.

  8. Ƴansanda sun kama wani matashi kan zargin kashe saurayin ƙanwarsa a Kano

    Kwamishinan ƴansandan jihar Kano CP Adamu Bakori

    Asalin hoton, Abdullahi Haruna Kiyawa/Facebook

    Bayanan hoto, Kwamishinan ƴansandan jihar Kano CP Adamu Bakori

    Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ce ta kama wani matashi bisa zargin kashe saurayin ƙanwarsa a lokacin da ya je zance gidansa.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Kunya da ke yankin ƙaramar hukumar Minjibir.

    Sanarwar yansandan ta ce matashin wanda ɗan asalin ƙauyen Goda, ya je Kunya ne wajen budurwarsa domin zance, sai dai jim kaɗan bayan zuwan nasa sai aka yi zargin cewa yayan budurwar mai suna Mansur Umar mai shekara 25 ya doke shi da sanda a ka, lamarin da ya haddasa masa munanan raunuka.

    ''Tuni aka garzaya da shi asibitin Kunya daga baya kuma aka mayar da shi asibitin Murtala domin ba shi kulawar gaggawa, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa'', a cewar ƴansandan.

    Ƴansanda sun ce tuni suka kama Mansur, domin gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴansandan jihar.

    Rundunar ƴansandan ta yi kira ga jama'a su riƙa sanya haƙuri a cikin al'amuransu, tare da kai rahoton duk wata jayayya da aka samu tsakanin wasu mutane zuwa ofishin ƴansanda mafi kusa.

  9. 'Hare-haren masu iƙirarin jihadi sun kashe gomman mutane a Burkina Faso'

    kas

    Asalin hoton, Getty Images

    Shaidu a Burkina Faso sun ce gomman fararen hula da sojoji aka kashe a wani hari da masu iƙirarin jihadi suka kai arewacin ƙasar.

    Mazauna garin Djibo sun ce gungun mayaka masu alaƙa da Al Qaeda ne suka kai jerin hare-hare kan barikokin soji da ofisoshin ƴansanda a gidajen mutane a yankin.

    To sai dai ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Right Watch ta zargi sojojin Burkina Faso na hannu kai -tsaye a kisan fararen hula ƴan ƙabilar Fulani kimanin 130 a lokacin wani samame da suka kai wasu ƙauyukan yammacin ƙasar.

    Kawo yanzu sojojin mulkin ƙasar ba su ce komai ba game da zarge-zargen.

  10. Hamas ta miƙa wa Red Cross Ba'amurken Isra'la Edan Alexander

    Mutane

    Asalin hoton, EPA

    Rahotonni daga Isra'ila na cewa ma'aikatan agaji na Red Cross sun karɓi Ba'amurken Isra'ila, Edan Alexander daga hannun mayaƙan Hamas.

    Tuni dandazon mutane suka taru a dandalin - tunawa da Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su - wanda ke birnin Tel Aviv, inda suke jiran gudanar da murnar sakin Mista Alexander.

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce sakin matashin mai shekara 21 ba zai kai ga tsagaita wuta ba, ko sakin Fursunonin Falasɗinawa ba.

    A gobe Talata ake san Shugaba Trump na Amurka zai ziyarci yankin Gabas ta Tsakiya.

    Jirgin

    Asalin hoton, Reuters

    Tuni wasu daga cikin dangin Alexander suka isa sansanin sojin Isra'ila na Re'im da ke kusa da Gaza, inda a nan ne a a ɗauke a jirgin sojin sra'ila zuwa Isra'ila.

  11. ASUU ta zaɓi Christopher Piwuna a matsayin sabon shugabanta

    Christopher Goson Piwuna

    Asalin hoton, Christopher Goson Piwuna/Social Media

    Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU ta zaɓi Farfesa Christopher Goson Piwuna a matsayin sabon shugabanta.

    Farfesa Piwuna ya kasance babban likita, kuma ƙwararren malami a fannin likitanci a jami'ar koyarwa da ke birnin Jos.

    An zaɓi sabon shugaban a lokacin babban taron wakilan ƙungiyar na ƙasa karo 23 da aka gudanar a jami'ar Benin, da ke jihar Edo ranar Lahadi.

    Farfesa Piwuna - wanda malami ne a jami'ar Jos - zai maye gurbin Emmanuel Osode.

    Kafin zaɓen nasa shi ne shi mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, kuma shugaban sashen kula da walwalar ɗalibai na jami'ar Jos

    An zaɓi farfesa Pinuwa bayan takara da Farfesa Adamu Bayero na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

  12. China da Amurka sun amince da rage harajin kaya da suka sanya wa juna

    Shugabannin Amurka da China

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen China da Amurka sun amince da rage harajin kaya da suka sanya wa junansu, wanda hakan zai sauƙaƙa yaƙin kasuwancin da ya hargitsa kasuwannin duniya.

    Sanarwar - wadda ta zo wa kowa da mamaki na zuwa ne bayan tattaunawar da ɓangarorin biyu suka yi a Geneva.

    Duka ƙasashe - Amurka da China - sun ce sun rage kuɗaɗen da ake sanya wa kayan da ake shiga da su cikinsu da kashi 115 cikin 100.

    Matakin da zai rage harajin da Amurka ta lafta a kan kayayyakin China da kashi 30 cikin 100.

    Ita kuma China za ta riƙa cazar kashi 10 cikin 100 a kan kayayyakin Amurka.

    Wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar Laraba mai zuwa inda kuma za a kwashe kwanaki 90 akan hakan.

  13. Ancelotti zai bar Madrid domin horas da Brazil

    Carlo Ancelotti

    Asalin hoton, Getty Images

    An tabbatar da kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocin babbar tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brazil

    Ɗan ƙasar Italiyan - wanda aka jima ana alaƙantawa da aikin horas da Brazil - ya kasance ɗan ƙasar waje na farko da zai horas da babbar tawagar ƙasar.

    Ana sa ran Ancelotti zai fara sabon aikin nasa zuwa ƙarshen watan da muke ciki.

    A watan Maris ne Brazil ta kori manajan tawagar ƙasar - Dorival Júnior - bayan Argentina ta casa ƙasar 4-1 a wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya .

    Ana sa ran Xabi Alonso - wanda a makon da ya gabata ya bayyana barin ƙungiyar Bayer Leverkusen - zai karbi ragamar Real Madrid, wadda ke ta biyu a kan teburin La Liga da tazarar maki bakwai, yayin da aka fitar da ita daga Gasar Zakarun Turai a matakin kwata fiyinal.

  14. JAMB ta ce za ta yi nazarin ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar kan sakamakon Jarrabawar UTME

    ...

    Asalin hoton, Jamb

    Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta ce za ta sake duba Jarrabawar UTME ta shekarar 2025, bayan korafe-korafe da yawa daga jama’a kan matsalolin fasaha da tambayoyi da ba su cika ba, da kuma sakamakon ƙaramin maki ba kamar yadda aka saba ba.

    A cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Fabian Benjamin ya fitar, JAMB ta bayyana cewa ta karɓi “ƙorafe-ƙorafe da ba su saba ba” tun bayan fitar da sakamakon jarrabawar a ranar Jumma’ar da ta gabata.

    Sanarwar ta ce wannan ƙoƙorafe-ƙorafen ne ya saka hukumar ta yanke shawarar yin bincike cikin gaggawa saɓanin yadda aka saba yi a baya watanni bayan kammala jarrabawar.

    An haɗa ƙwararru daga fannin kimiyyar kwamfuta da masu kimanta jarrabawa da shugabannin jami’o’i don taimakawa a aikin.

    JAMB ta tabbatar da cewa idan aka gano wata matsala a tsarin, za ta ɗauki matakan gyara da suka dace nan take.

    A halin yanzu kuma, rahotanni na nuna cewa dubban waanda suka rubuta jarabawa na shirin shigar ƙara a kotu bisa zargin rashin daidaito a gudanar da jarabawar.

  15. Amurka ta amince da fararen fata ƴan Afrika ta Kudu a matsayin ƴan gudun hijira

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Rukunin farko na fararen fata ƴan Afirka ta Kudu 'Afrkaners' guda 49 da Shugaba Trump ya amince da shigarsu a matsayin 'yan gudun hijira sun bar ƙasar zuwa Amurka, kamar yadda shafin labarai mai zaman kansa, The Citizen, ya ruwaito.

    Rukunin farkon sun hau jirgi zuwa birnin Washington a jiya daga filin jirgin sama na OR Tambo da ke garin Kempton Park, a ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro daga ‘yan sanda.

    Wannan na zuwa ne duk da gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana matakin Amurka na ba su matsayin ‘yan gudun hijira bisa zargin nuna musu wariya a matsayin mara tushe.

    Rahotannin kafafen yaɗa labarai na Afirka ta Kudu sun bayyana cewa daga cikin mutanen guda 8,000 da suka nemi sake zama a Amurka, aƙalla mutum 100 ne gwamnatin Amurka ta amince da su.

    Dangantakar diflomasiyya tsakanin Afirka ta Kudu da Amurka ta yi tsamin gaske tun bayan dawowar Trump kan mulki a watan Janairu.

    Trump ya dakatar da dukkan tallafin kuɗi da Amurka ke ba Afirka ta Kudu, yana zargin gwamnatin ƙasar da nuna wariya ga fararen fata, bayan Shugaba Cyril Ramaphosa ya sanya hannu a doka kan ƙwace filaye ba tare da biyan diyya ba a watan Janairu.

  16. Mun tarwatsa wani sansanin Boko Haram a Sambisa - Sojojin Najeriya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation HADIN KAI (OPHK) sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama a wani samame da suka ƙaddamar a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

    Wannan aikin, a cewar sanarwar da shalkwatar sojojin ta fitar ta ce ya gudana ne a ranar 11 ga watan Mayu, 2025, a yankin Ladin Buttu, "wurin da aka san shi da zama mafakar ’yan ta’adda" kuma rundunar sojin ta bayyana nasarar a matsayin muhimmin ci gaba a yaƙin da ake yi da ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso gabashin ƙasar.

    Hakan na zuwa ne bayan sabbin hare-haren da mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar kan wurare daban-daban a jihar Borno, inda matsalar rikicin Boko Haram ta fi ƙamari.

    A sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, mataimakin daraktan hulda da jama’a na Sojojin, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da cewa sojojin sun yi arangama da ’yan ta’addan cikin kazamin fada.

    "Sojojin sun yi amfani da ingantattun makamai da dabaru, lamarin da ya ba su nasara wajen kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga." in ji sanarwar.

    An kuma ƙwato makamai da kayan yaki masu tarin yawa, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Ladin Buttu na daya daga cikin muhimman sansanonin mayaƙan Boko Haram a yankin, "inda su ke amfani da shi wajen tsara dabaru da adana kayayyaki, da ƙaddamnar da hare-hare."

    Kyaftin Kovangiya ya bayyana cewa wannan aiki ya yi daidai da umarnin sabon shugaban Hafsan Sojin Kasa na ƙara kaimi wajen kai hare-hare da rushe cibiyoyin Boko Haram a yankin.

  17. Amurka da China sun amince da rage harajin shigo da kaya na tsawon kwana 90

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka da China sun cimma yarjejeniyar da za ta rage harajin shigo da kaya, wato harajin da kowanne ɓangare ke sanya wa juna, na tsawon kwana 90.

    Sakataren baitul mali na Amurka, Scott Bessent, ya bayyana cewa ƙasashen biyu za su rage harajin da suke sanya wa juna da kashi 115% na tsawon kwanaki 90.

    Sanarwar ta fito ne bayan ganawar da ƙasashen suka yi a Switzerland – karo na farko da suka yi irin wannan tattaunawa tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗora haraji mai tsanani kan kayayyakin da ake shigo da su daga China.

    Wannan mataki na haraji ya haifar da rikici a kasuwannin hada-hadar kuɗi tare da tayar da fargabar durƙushwar tattalin arzikin duniya.

    Shugaba Trump dai ya sanya harajin kashi 145% kan kayayyakin da ake shigo da su daga China, yayin da Beijing ta mayar da martani da harajin kashi 125% kan wasu kaya daga Amurka.

    Sai dai yanzu, harajin da Amurka ke sanyawa kayayyakin China zai ragu zuwa kashi 30% na tsawon kwana 90, yayin da harajin China kan kayayyakin Amurka zai ragu zuwa kashi 10% na wannan lokacin.

    Wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar 14 ga Mayu.

  18. Ambaliya ta hallaka ɗaruruwan mutane a Gabashin DR Congo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 110 tare da jikkata wasu da dama a kauyen Kasaza da ke cikin yankin Fizi na gabashin lardin Sud Kivu a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, kamar yadda gidan rediyon Okapi da ke ƙarƙashin goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ya ruwaito.

    Aƙalla gidaje 150 ne ruwa ya shafe a sakamakon ruwan sama da aka samu tsakanin ranakun 8 zuwa 9 ga Mayu, lamarin da ya bar fiye da mutum 850 ba tare da matsuguni ba.

    Mai kula da yankin Fizi, Samy Kalonji, ya nemi agaji domin binne mamatan da kuma taimakawa iyalan da suka rasa matsugunansu.

    "Jikunan mutane da dama har yanzu na kwance a ƙasa. Muna buƙatar akwatin gawa da taimako domin a samu a binne su cikin mutunci," in ji Kalonji.

    A wani labari makamancin haka kuma, mutum 62 ne suka mutu a daren 8 zuwa 9 ga watan Mayu bayan ambaliya daga rafin Kasaba ta mamaye wani ƙauye daban da ke cikin yankin Fizi, kamar yadda shafin Media Congo mai zaman kansa ya bayyana.

    Jami'an yankin sun ce aikin ceto yana fuskantar cikas sakamakon lalacewar hanyoyi da kuma nisan wurin da abin ya faru.

    Wannan na zuwa ne ƙasa da wata guda bayan da aƙalla mutum 30 suka mutu sakamakon ruwan sama da ambaliya a babban birnin ƙasar, Kinshasa.

  19. Indiya da Pakistan za su kammala tattaunawa kan tsagaita wuta a yau

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan hafsoshin soji daga ƙasashen Indiya da Pakistan za su gana a ranar Litinin domin ƙarƙare magana kan yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma a karshen mako.

    Wannan yarjejeniya da aka samu ta hanyar shiga tsakani daga Amurka, ta zo ne kusan kwanaki huɗu bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙasashen biyu, waɗanda dukkaninsu suka mallaki makaman nukiliya.

    A ranar Asabar, Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana tsagaita wutar, yana mai cewa: "Lokaci ne da ya kamata a dakatar da wannan rikici da ka iya janyo mutuwar mutane da lalacewar dukiya masu yawa."

    Tun daga lokacin ne ƙasashen biyu suka dakatar da faɗa, amma kowanne daga cikinsu yana ci gaba da gargadi kan sakamakon karya yarjejeniyar.

    India ta sanar da sake buɗe filayen jiragen sama 32 da ta rufe saboda dalilai na tsaro, wadanda aka ce za su kasance a rufe har zuwa Alhamis.

    Bayan yarjejeniyar tsagaita wutar, kowanne ɓangare ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a fagen daga.

    A ranar 7 ga Mayu ne dai India ta bayyana cewa ta kai hare-hare kan wurare guda tara a cikin Pakistan a matsayin martani ga harin 'yan bindiga da ya kashe mutane 26 a yankin da India ke iko da shi na Kashmir.

  20. Birtaniya za ta ƙara tsaurara dokokin shige da fice

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Birtaniya na shirin bayyana sabuwar doka kan shige da fice a yau, wadda za ta haɗa da ƙarin tsauraran sharuddan samun biza ga mutane daga wasu ƙasashe, ciki har da Najeriya da ake sa ran za ta shiga jerin.

    Firaminista Keir Starmer dai na shirin bayyana sabbin matakai masu tsauri kan bizar ɗalibai da kawo ƙarshen samun zama na dindindin bayan shekaru biyar, da kuma ƙara tsaurara ka'idoji kan bizar yawon buɗe ido.