Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 08/04/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail da Ahmad Bawage

  1. Aljeriya da Mali sun dakatar da jirage sauka a ƙasashen juna

    Air Algerie

    Asalin hoton, @medias_air

    Ƙasashen Aljeriya a Mali sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a tsakaninsu yayin da rikicin difilomasiyya ke ci gaba da ruruwa tsakanin ƙasashen na Sahel.

    A ranar Lahadi Mali ta zargi maƙociyar tata da ɗaukar nauyin ta'addanci, ba tare da bayar da wata hujja ba, bayan Aljeriyar ta harbo jirgin Mali maras matuƙi a makon jiya.

    Aljeriya ce ta fara dakatar da saukar jirage daga Mali, inda daga baya ita ma ta ce ta ɗauki matakin kan dukkan jiragen da ke fitowa daga Aljeriya.

    Aljeriya ta ce jirgin ya keta alfarmar sararin samaniyarta, abin da Mali ta musanta da kakkausar murya.

    Mali ta ce harbo jirgin "aikin tsokana ne". Ita kuwa Aljeriya ta ce zargin ɗaukar nauyin ta'addanci "abin dariya ne...da ba shi buƙatar amsa".

  2. Wike ya gana da 'yanmajalisar Rivers da aka dakatar a Landan

    Wike da 'yanmajalisa

    Asalin hoton, Lere Olayinka

    Ministan Abuja Nyesom Wike ya gana da 'yanmajalisar jihar Rivers da ke jayayya da ɓangaren Gwamna Fubara, waɗanda kuma aka dakatar.

    Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya ce an yi ganawar ne ranar Litinin a birnin Landan.

    Wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X ya nuna ministan da 'yanmajalisar na cin abincin dare tare.

    Wike ya tafi Landan ne bayan ganawa da abokan siyasarsa a jihar ta Rivers ranar Lahadi, wadda ke ƙarƙashin dokar ta-ɓaci da Shugaba Tinubu ya saka saboda rikicin siyasa tsakanin Wike da Gwamna Fubara.

    A makon da ya gabata ne 'yanmajalisar suka sanar da yin balaguron zuwa Birtaniya da zimmar inganta ayyukansu na majalisa a can.

  3. Najeriya ba ta cikin ƙasashen da Saudiyya ta daina bai wa biza - Gwamnatin Najeriya

    Jakadan Saudiyya da Yusuf Maitama Tuggar

    Asalin hoton, @YusufTuggar

    Ma'aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta musanta cewa ƙasar na cikin jerin ƙasashe da Saudiyya ta hana ba su biza daga 13 ga watan Afrilu.

    Kamfanin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar na yin ƙarin bayanin ta bakin mataimakinsa na musamman kan kafofin yaɗa labarai, Alkasim Abdulkadir, ranar Litinin.

    Ministan ya ce Saudiyya ta tabbatar musu cewa jerin sunayen da ke nuna Najeriya na cikinsu, wanda kuma aka dinga yaɗawa a shafukan sada zumunta, ba na gaskiya ba ne.

    "Hukumar Saudiyya ta tabbatar babu wani umarni mai kama da haka, dokokin da aka saka a hyanzu sun shafi aikin Hajji ne kawai. A gane cewa, dokokin sun shafi masu bizar yawon buɗe ido ne kawai a lokacin aikin Hajji," a cewarsa.

    Bisa ƙa'idojin, an haramta wa masu bizar yawon buɗe ido yin aikin Hajji, ko shiga Makkah tun daga 29 ga watan Afrilu zuwa 11 ga Yuni (ko kuma 1 ga watan Zul Ƙida zuwa 14 ga Zul Hijjah na kalandar Musulunci).

    Jerin sunayen da aka dinga yaɗawar na ƙunshe da ƙasashen Masar, Pakistan, Indiya, da kuma Najeriya.

  4. Hukuncin kisa ya kai ƙololuwa a duniya, in ji wani rahoto

    Wani rahoto ya nuna cewa adadin hukuncin kisa da aka zartar a duniya ya kai matakin ƙololuwa a cikin kusan shekara 10.

    Kungiyar kare haƙƙin ta Amnesty International ta ce sama da mutum 1,500 aka zartar wa hukuncin kisa a 2024.

    Wakilin BBC ya ce a rahoton da aka wallafa, kusan kashi 90 cikin 100 na hukunce-hukuncen an zartar da su ne a ƙasashen Iran da Iraki da Saudiyya.

    Sai dai rahoton bai haɗa da dubban mutanen da aka yi imanin an kashe a China ba, wadda aka bayyana a matsayin ta kan gaba wajen aiwatar da hukuncin kisa a duniya.

  5. Aradu ta kashe shanu takwas a jihar Ondo

    Shanu

    Asalin hoton, Reuters

    Walƙiya ko kuma aradu ta kashe shanu kusan takwas a jihar Ondo da ke kudancin Najeriya, kamar yadda rahoton Channels TV ya ruwaito.

    Lamarin ya faru ne a garin Ori-Ohin na ƙaramar hukumar Ose ranar Lahadi da yamma sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

    Mai magana da yawun rundunar 'yansandan Najeriya a jihar, Olayinka Ayanlade, ya faɗa wa kafar talabijin ɗin cewa tsautsayi ne kawai ya faɗa musu.

    Ya ƙara da cewa tuni rundunar ta fara ɗaukar mataki saboda kada lamarin ya haifar da fitina.

    Channels ta ce irin wannan lamari ya taɓa kashe shanu 36 a 2019 lokacin da aradu ta auka wa yankin Ifedore na jihar ta Ondo.

  6. Iran da Amurka za su tattauna ranar Asabar

    Ayatollah Kamnei

    Asalin hoton, EPA

    Iran ta tabbatar da kalaman Trump cewa za ta tattauna da Amurka ranar Asabar game da batun shirinta na nukiliya.

    Sai dai kuma gwamnatin Iran ta ce tattaunawar ba za ta kasance ta gaba da gaba ba saɓanin iƙirarin Trump.

    Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce za a yi ganawar ne a Oman - tattaunawar da za ta kasance zakaran gwajin dafi.

    Tuni Mista Trump ya yi gargaɗin cewa idan tattaunawar ta ranar Asabar ta gagara Iran na cikin haɗari.

    Wakiliyar BBC ta ce hakan ya nuna Shugaba Trump na son kauce wa yaƙi, haka ma Iran.

    A gefe guda kuma, yau Talata ne Rasha da China da Iran za su yi wata tattaunawa ta tuntuɓar juna a birnin Moscow.

  7. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Talata.

    Shafin zai kawo rahotonni daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana.

    Ni ne Umar Mikail zan kawo rahotonnin har zuwa ƙarfe 4:00 na rana bisa kulawar Usman Minjibir.