Arsenal ta bai wa maraɗa kunya bayan dukan kawo wuƙa da ta yi wa Real Madrid a Emirates a karawar farko ta matakin kwata-fainal a gasar zakarun Turai ta Champions League.
Arsenal ta zura wa Real ƙwallaye uku reras bayan dawowa hutun rabin lokaci.
Ɗan wasan tsakiya na Arsenal Declan Rice ne ya zura ƙwallo biyu ta hanyar bugun tazara a minti na 58 da kuma minti na 70.
Sai kuma daga baya Mikel Merino ya cike ta uku a minti na 75.
75. Arsenal 3 - 0 Real Madrid
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mikel Merino lokacin da yake murnar zura ƙwallo a wasan Arsenal da Real Madrid
Arsenal ta hannun ɗan wasanta Mikel Merino ta zura ƙwallo ta uku a ragar Real Madrid a karawar da ake tsakanin ƙungiyoyin biyu a matakin kwata-fainal na gasar Champions League, falle na ɗaya.
Merino ya zura ƙwallon ne a minti na 74 da take wasa, bayan ɗan wasa Lewis Skelly ya zuro masa ƙwallon daga gefe.
70. Arsenal ta zura ƙwallo ta biyu a ragar Real
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Declan Rice lokacin da yake murnar zura ƙwallo ta biyu a ragar Real Madrid
Kamar yadda ya zura ta farko, ɗan wasan Arsenal na tsakiya Declan Rice ya ƙara zura ƙwallo ta biyu a ragar Real Madrid ta hanyar bugun tazara.
Lamarin ya zo da ba-zata, ganin cewa dukkanin ƙwallayen biyu na kamanceceniya ta hanyar tazara da kuma yanayin da aka jefa su a raga.
58. Arsenal 1 - 0 Real Madrid
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta zura ƙwallo a ragar Real Madrid a karawar da suke yi ta kwata-fainal a gasar Champions League, falle na ɗaya.
Ɗan wasan tsakiya na Arsenal Declan Rice ne ya zura ƙwallon ta hanyar bugun tazara bayan da ƴan wasan Madrid suka yi wa Bukayo Saka ƙeta.
An ayyana dokar haramta aure jinsi a Nijar
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Abdourahmane Tchiani
Gwamnatin
mulkin sojin Nijar ta ayyana dokar haramta auren jinsi da luwadi da madigo da
sauran dabi'u masu kama da su a kasar.
Kazalika gwamnatin ta kuma ayyana addinin Musulunci a
matsayin addini na kasa.
Gwamnatin ta dauki wannan matakai ne a sabuwa dokar
tsarin mulkin rikon kwarya ta kasa da babban taron muhawara na kasa da ya
gudana ya samar.
Nana Jubi Haruna Maty, tsohuwar 'yar majalisar dokokin Nijar ce
da ta jagoranci fafutuka yaki da wadannan dabi'u a wancen lokaci ta shaida wa BBC irin yadda ta ji dadi bayan gwamnatin ta dauki wannan
mataki.
Ta ce," Gaskiya wannan mataki babban ci gaba ne domin zai kara gyara tarbiyya a tsakanin al'ummar kasarmu."
Nana Jubi Haruna, ta ce, " A baya a lokacin da na ke 'yar majalisa mun yi gwagwarmaya wajen ganin an samar da wannan doka, ga kalubale kala-kala da na fuskanta domin ba barazanar da ba mu fuskanta ba, to amma hakarmu bata cimma ruwa ba, to amma yanzu Alhamdulillah tun da hakarmu ya cimma ruwa."
Tsohuwar 'yar majalisar dokokin ta Nijar ta ce yanzu al'adunsu da dabi'unsu za su rika tafiya tare da addini Musulunci, wannan kuma ba karamin abin jin dadi ba ne in ji ta.
Hutun rabin lokaci: Inter Milan ta zura wa Bayern Munich ƙwallo ɗaya
Asalin hoton, Getty Images
A karawar da ake yi tsakanin Bayern Munich da Inter Milan a Jamus, Inter ce ke gaba bayan ta zura wa Munich waɗanda ke wasa a gida ƙwallo ɗaya.
Lautaro Martinez ne ya zura ƙwallon lokacin da ake minti na 38 da fara wasa.
An tafi hutun rabin lokaci babu ci tsakanin Arsenal da Real Madrid
Asalin hoton, Getty Images
An kammala minti 45 na karawar da ake yi tsakanin Arsenal da Real Madrid a matakin kwata-fainal na gasar zakarun nahiyar Turai ta Champions League.
Duk da cewa babu ɓangaren da ya samu nasarar zura ƙwallo amma wasan ya yi matuƙar zafi tsakanin ɓangarorin biyu.
An rika kai farmaki babu ƙaƙƙautawa, inda ɗan wasan gaba na Real Madrid Kylian Mbappe da na Arsenal Gabriel Martinelli duk suka nemi raga a lokuta daban-daban.
Alƙaluma na nuna cewa Arsenal ta kai farmaki sau huɗu yayin da Real ta kai hari sau biyar.
Haka nan kuma a wajen shafa ƙwallo, wato Posession, Arsenal ce kan gaba da 55% yayin da Real Madrid ke da 45%.
Yadda rainon ciki ya zamo abin nishaɗi ga mata a Ghana
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Kimanin mata 300,000 ne ke rasa rayukansu a duk shekara lokacin haihuwa.
A bana, Ranar Lafiya ta Duniya ta mayar da hankali ne kan lafiyar uwa da jariri.
Komla Adom na BBC ya kai ziyara cibiyar lafiya da ke Parambo, wani ƙauye a Ghana, inda wani shiri da ya kawo tsarin yin rawa da kuma ado a wurin kula da masu juna biyu ke sauya yadda mata ke kallon renon juna-biyu.
Wannan shiri yana ƙarfafa wa ɗaruruwan mata zuwa wurin awon ciki, wanda hakan ke taimakawa wajen inganta lafiyar uwa da ɗa.
Amurka ta soki matakin ƙasashen Afirka na kafa wa Amurka shingen kasuwanci
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, .
Jami'i mai kula da harkokin kasuwanci na Amurka, Ambasada Jamieson Greer, ya soki matakin wasu kasashen Afirka na kafa shingen kasuwanci da kasarsa, inda ya bayyanasu a matsayin wadanda ba su yi wa masu fitar da kaya daga Amurka adalci ba.
Ofishin kula da harkokin kasuwanci na Amurka, ya ce haramcin da Najeriya ta yi na shigar da wasu kayayyakin Amurka zuwa kasarta da suka hada da abubuwan da suka shafi na noma da magunguna da kayan shayi da sauran kayayyaki, zai haifar da babbar koma baya da asara ga 'yan kasuwar da suka Amurka da ke harkokinsu a Najeriya.
Jami'in ya ce, haramcin da aka sanya a kan kayayyaki kamar naman sa da na alade da lemuna, zai matukar takaitawa Amurka samun damar fitar da kayayyakinta zuwa kasar.
Kasar Angola wadda ita ce kasar da Amurka ta fi shigar mata da kayan kiwon kaji, ita ma a baya bayannan ta sanar da cewa za ta takaita yadda Amurka ke shigar mata naman sa da na alade da kuma kayan kiwon kaji, matakin da Amurka ta ce zai matukar yin illa ga manoman kasarta.
Gwamnatin Amurka ta ce, matakin Algeria na takaita shigar mata da magunguna da sauran kayan kula da lafiya zai janyo babban koma baya ga 'yan kasuwar Amurka da ke fitar da magunguna zuwa Algeria.
A makon daya gabata ne gwamnatin Amurka ta sanar da karin kashi 10 cikin 100 na dukkan kayayyakin da ake shigar mata da shi kasarta.
Amurka ta ƙara haraji kan kayan China zuwa kashi 104%
Asalin hoton, White House
Bayanan hoto, Shugaban Amurka, Donald Trump
Fadar shugaban ƙasar Amurka ta tabbatar da cewa za ta lafta harajin kashi 104% kan kayan da ake ƙerawa a China waɗanda ake shiga da su Amurka, kuma matakin zai fara aiki ne daga gobe Laraba.
Hakan na zuwa ne yayin da shugaba Donald Trump ya bayyana cewa zai ƙara yawan kuɗin fito kan kayan China da ake shiga da su Amurka, matuƙar China ba ta janye harajin ramuwa da ta lafta kan kayan Amurka da ake shiga da su ƙasarta ba.
Sakatariyar yaɗa labarai ta fadar White House, Karoline Leavitt ta bayyana wa manema labarai cewa China ta yi "kuskure" da ta mayar da martani kan matakin Amurka, kuma ta ce Trump zai yi "matuƙar farin ciki" idan China ta nemi hanyar sulhu.
Ta ƙara da cewa tuni ƙasashe 70 na duniya suka tuntuɓi Amurka domin tattaunawa tun bayan da Mista Trump ya ayyana lafta haraji kan kayan da ake shiga da su ƙasar daga ƙetare.
Arsenal ta bayyana ƴan wasanta da za su kara da Real Madrid
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ita ma ta fitar da sunayen ƴan wasa 11 da za ta fara da su a karawarta ta matakin kwata-fainal ɗin gasar Champions League da za ta gudana anjima kaɗan a birnin Landan.
Jerin sunayen na nuna cewa Bukayo Saka, wanda ya dawo daga jinya a kwanan nan na cikin ƴan wasan 11 da za a fara da su.
Ga jerin sunayen: Raya, Timber, Saliba, Kiwior, Lewis-Skelly, Partey, Rice, Odegaard, Saka, Martinelli, Merino.
'Ana samun ƙaruwar mutanen da ake tilastawa komawa Afghanistan daga Pakistan'
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, .
Hukumar da ke kula da ƙaurar jama'a ta ce ana samun ƙaruwar mutanen da ake tilastawa komawa Afghanistan daga Pakistan.
Wa'adin da aka ware na komawa gida bisa raɗin kai ya kare a karshen watan Maris, inda aka tisa ƙeyar sama da mutane 800,000 zuwa Afghanistan tun bayan wannan lokacin.
Milyoyin 'yan Afghanistan sun koma Pakistan cikin shekaru 40 da suka gabata.
Galibinsu mata ne masu fafutika da mutanen da ke aiki da ƙungiyoyin yamma inda suke fargabar abin da zai iya biyo wa idan suka koma Afghanistan.
Gwamnatin Taliban dai ta ce kowa na iya komawa ba tare da nuna fargaba ba.
Real Madrid ta fitar da jerin ƴan wasanta da za su kara da Arsenal a yau
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Real Madrid, kamar yadda ta saba ta fitar da jerin ƴan wasa 11 da za ta fara da su a karawarta da Arsenal a matakin kwata-fainal na gasar Champions League da za a buga a yammacin yau.
Ƴan wasan su ne: Courtois, Valverde, Asencio, Rudiger, Alaba, Modric, Camavinga, Bellingham, Rodrygo, Mbappe, Vinicius Jr.
Benci: Gonzalez, Mestre, Guler, Endrick, Lucas V, Vallejo, Fran Garcia, Brahim, Gonzalo, Jacobo, Chema, Lorenzo.
An buƙaci ƴansanda su nemi afuwa kan dukan ƴan jarida lokacin zanga-zanga
Asalin hoton, NPF
Bayanan hoto, Kayode Egbetokun
Kungiyar 'yan jaridu ta Najeriya NUJ, ta bukaci 'yan sandan kasar da su nemi afuwa kan dukan da 'yan sanda suka yi wa wasu 'yan jarida a lokacin zanga-zangar da aka yi a ranar Litinin a wasu jihohin kasar.
Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar na kasa Comrade Paul Bazia da kuma sakatariyar kungiyar Dr. Ijeoma Tubosia, suka fitar, kungiyar ta yi alawadai da matakin da wasu jami'an 'yan sanda suka dauka na dukan 'yan jarida inda ta bukaci a gaggauta gano su tare da hukuntasu.
Sanarwar ta ce," Mu a matsayinmu na masu sanya idanu a cikin al'umma, ba zamu zauna muna gani ana aikata ba dai-dai ba sannan kuma mu yi shiru. A don haka abubuwan da ake sun isa haka duk wanda ya kara kai wa wani dan jarida hari to zai dandana kudarsa."
Kungiyar 'yan jaridun ta bayyana abin da ya faru da rashin tausayi da kuma take hakkin ɗan jaridar.
Cikin 'yan jaridar da lamarin ya shafa akwai ma'aikacin gidan talbijin na Channels da Naija FM da Nigeria Info da na AIT da kuma na Super FM.
An watsawa 'yan jarida hayaki mai sa hawaye a lokacin da suke bakin aiki a yayin zanga-zangar inda daga bisani kuma aka musu dukan tsiya tare da tsare su da jami'an tsaro suka yi.
Daga nan kungiyar 'yan jaridar ta bayyana takaicinta a kan abin da ya faru, inda ta ce hukumar da aka kafa domin kare al'umma ta koma mai cin zarafin al'umma, musamman ƴanjarida a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
Ta kuma gargaɗi rundunar ƴansandan kan cewa kada ta rusa kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninta da kafafen yaɗa labarai.
Wasu yankunan Borno na 'kuɓucewa' daga hannun gwamnati - Zulum
Asalin hoton, FB/Babagana Zulum
Bayanan hoto, Boko Haram ta kwashe sama da shekara 10 tana kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa kan yadda hare-haren ƙungiyar Boko Haram ke sanyawa jihar ke "rasa wasu daga cikin yakunanta."
Zulum ya bayyana haka ne yau Talata a lokacin taron lamurran tsaro da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar.
A cikin jawabin da ya gudanar, Zulum ya ce "Yayin da nake wannan jawabi a yau, abin takaici shi ne sabbin hare-haren Boko Haram da satar mutane da suke yi a yankuna da dama a a kowace rana, ba tare da an ƙalubalance su ba, na nuna cewa jihar Borno na rasa ƙasarta".
"Kamar yadda kuka sani, gwamnatina na taimaka wa sojoji da sauran hukumomin tsaro wajen yaƙi da Boko Haram da sauran ƴan ta'adda, lamarin da ya sanya aka samu sauƙi a cikin shekaru uku da suka gabata, amma abin takaici ne na shaida muku cewa hare-hare na baya-bayan nan da tarwatsa sansanin soja a Wajirko da Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa, da Wulgo a Gamboru Ngala, da Izge a ƙaramar hukumar Gwoza da wasu sauran kashe-kashen fararen hula da jami'an tsaro a baya-bayan nan abin damuwa ne, kuma koma-baya ne ga jihar Borno da kuma yankin Arewa maso Gabas."
A saboda haka ne gwamnan ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara ƙaimi a ƙoƙarinta na tabbatar da tsaro da kuma yaƙi da ƙungiyar ta Boko Haram.
A baya-bayan hare-haren Boko Haram na ƙara ƙamari a jihar, lamarin da ya haifar da asarar rayukan fararen hula da kuma jami'an tsaro.
Kotu a Kano ta ɗaure shahararren mai sana'ar kwalliya kan liƙi da naira, Mansur Abubakar
Asalin hoton, efcc
Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta yanke wa wani shahararren mai sana'ar kwalliya hukuncin ɗaurin wata shida, bayan samunsa da laifin liƙi da naira lokacin bikin aurensa a watan Disamba.
An yanke wa Abdullahi Musa Hussaini, wanda aka fi sani da "Amuscap" a shafukan sada zumunta hukuncin ne, jim kaɗan bayan amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Ana dai liƙi ko watsa takardar kuɗi a sama a Najeriya ne yawanci lokacin bukukuwa musamman ma na aure, domin nuna farin ciki.
Sai dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na da'awar a guji liƙa kuɗi a irin waɗannan bukukuwa, inda ta ce hakan rashin mutunta kuɗin naira ne.
Amuscap shi ne ɗan Najeriya na baya-bayan nan da aka ɗaure kan saɓa wa dokar babban bankin Najeriya (CBN) na 2007.
Dokar ta ce "liƙi da rawa ko kuma taka kuɗin naira laifi ne, hukuncinsa shi ne ɗaurin wata shida a gidan yari ko cin tarar 50,000 ko kuma duka aiwatar da duka hukuncin.
EFCC ta ce Amuscap ya liƙa tare da taka kuɗi naira 100,000 lokacin murnar bikin aurensa.
A shekarar da ta gabata, aka ɗaure shahararren ɗan daudun nan Idris Okineye, da aka fi sani da Bobrisky da kuma wata jarumar Nollywood Oluwadarasimi Omoseyin wata shida a gidan yari, bayan samun su da laifin liƙa kuɗi.
Ba a biya kuɗi wajen ceto Janar Tsiga ba - Hedkwatar tsaron Najeriya
Asalin hoton, Family
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce babu kuɗin fansa da aka biya kafin sakin tsohon shugaban Hukumar yi wa Ƙasa Hidima a Najeriya NYSC, Manjo Janar Mahrazu Tsiga, mai ritaya daga hannun ƴanbindiga.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hedkwatar tsaron Birgediya-Janar Tukur Gusau ya fitar, ya ce sojoji sun yi amfani da dabarun karfi da kuma bayanan sirri wajen ceto Janar Tsiga.
"Tun bayan sace Janar Tsiga ranar 7 ga watan Fabrairu, sojoji ba su yi ƙasa a gwiwa ba. Sun kai samame ta sama da kuma ƙasa a ƙananan hukumomin Ɗanmusa da Faskari da kuma Kankara inda ake kyautata zaton masu garkuwan sun ajiye shi," a cewar Tukur Gusau.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun yi ta aiki tukuru babu dare ba rana wajen nema da kuma ceto tsohon shugaban na NYSC.
An dai yi garkuwa da shi ne ranar 5 ga watan Fabrairu, a garin mahaifarsa ta Tsiga da ke karamar hukumar Bakori na jihar Katsina - tare da wasu mutum 13.
Meta zai taƙaita wa ƴan ƙasa da shekara 16 amfani da Instagram da Facebook
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin Meta zai faɗaɗa damar da yake bai wa iyayen na tantance yadda ƴaƴansu ke amfani da shafukan Instagram da Facebook.
Wannan sauyin na nufin duk yaran da ke ƙasa da shekaru 16, ba za su iya yin bidiyon kai-tsaye ba a shafukansu ba tare da amincewar iyayensu ba.
Sannan zai rinka disashe hotunan batsa da ake aikewa juna, sai dai idan da izinin iyaye.
Waɗannan sauye-sauye na zuwa ne yayin da kamfanin na Meta ke fuskantar tuhuma daga gwamnatoci da dama, ciki har da na Birtaniya da Amurka, kan gaza wa wajen kare yara da ke amfani da shafukansu.
Nijar ta ayyana Hausa matsayin harshen da za a yi amfani da shi a ƙasar
Asalin hoton, Elmastro TV
A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta bayyana Hausa a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar yayin da sauran harsuna ta ayyanasu a matsayin na magana.
Kazalika an kuma bayyana harshen Ingilishi da Faransanci a matsayin harsunan aiki.
To sai dai kuma ba dukkanin 'yan kasar ne ke maraba da wannan mataki ba.
An kiyasta cewa akwai mutum miliyan 18 da ke jin harshen Hausa a Jamhuriyar Nijar, abin da ake ganin wannan ne ya sanya gwamnatin kasar ta ayyana shi a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar.
To sai dai kuma ba dukkanin 'yan kasar ne wannan mataki ya yi wa dadi ba, inda wasu ke cewa ya kamata a yi nazari sosai a kai.
Harshen Hausa shi ne ke matsayin na uku a Afirka inda kasashe da dama a Afirka a ke samun masu jin harshen.
Akwai dai masu jin harshen Hausa a kasashe kamar Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi da Sudan da Benin da Togo da Gabon da kuma Burkina Faso.
Yadda kasuwar 'hatsi' ta ƴan gudun hijira a Nasarawa ke jan hankalin jama'a
Kasuwar Auta Balefi da ke jihar Nasarawa, wadda ƴan gudun hijira suka kafa, yanzu ta fara gogayya da wasu kasuwanni a jihar saboda yadda hada-hada ke gudana a cikinta.
Ƴan gudun hijirar sun koma zama a garin ne da kuma kafa kasuwar bayan gudun hijira da suka yi sakamakon matsalar Boko Haram da kuma na ƴan bindiga da ta janyo suka tserewa muhallansu kusan shekaru goma da suka wuce.
Waklin BBC da ya kai ziyara kasuwar, ya ruwaito cewa mutane daga ciki da wajen Najeriya na zuwa domin cin kasuwar, da sayan kayan abinci.
Wasu daga cikin mutane da ke hada-hada a kasuwar sun bayyana farin cikinsu yadda kasuwar take ci a yanzu.
Sun ce za ta sauƙaƙawa al'umma samun kayan abinci cikin sauki.