Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 17/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar,Rabiatu Runka da Haruna Kakangi

  1. Rufewa

    Masu bibiyar mu a nan muke sallama da ku, sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu, za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Rabiatu Kabir Runka da Haruna Ibrahim Kakangi ke maku fatan alheri.

  2. Syria na buƙatar agajin gaggawa - MDD

    UN CHIEF

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria, ya yi gargadin matukar ana son lamura su daidaita a kasar, dole sai an kai wa Syria daukin gaggawa sakamakon yakin da ya daidaita kasar.

    Geir Pedersen, ya shaida wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa ba a kare yakin ba, duk da cewa an hambarar da mulkin Bashar al-Assad.

    Ya yi misali da tashin hankali na baya-bayan nan tsakanin mayakan Kurdawa da kungiyoyin da Turkiyya ke mara wa baya a arewa maso gabashin kasar.

    Ya ce "ana samun tashe-tashen hankula cikin makonni biyun da suka gabata, kafin a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta wadda Turkiyya da Amurka suka jagoranta.

    Yarjejeniyar ta kwanaki biyar ta kare, ina cike da damuwar abin da zai faru nan gaba," in ji shi.

  3. Sau biyu ana yunƙurin kashe ni - Fafaroma

    Pope Francis

    Asalin hoton, Reuters

    Fafaroma Francis ya ce sau biyu 'yan sandan Iraqi da jami'an tsaron Birtaniya na dakile yunkurin kashe shi a lokacin da ya kai wata ziyara birnin Mosul a shekarar 2021.

    Wannan bayanin na kunshe cikin littafin tarihin rayuwar babban limamin mabiya darikar Katolika da aka yi wa lakabi da 'Fata' ko 'Hope' a turance.

    Fafaroman ya ce daya daga cikin hare-haren na kunar bakin wake ne da wata mace ta sha damara da ababen fashewar, yayin da wani aka dasa shi cikin wata mota.

    Ya kara da cewa 'yansandan Iraqi sun cafke mutanen tare da hallaka su.

    Ziyarar ta kwanaki uku da Fafaroma ya kai birnin Mosul na Iraqi, ita ce tafiya ta farko da ya yi cikin shekara guda kuma ana tsaka da annobar Korona.

  4. Vinicius Junior ya zama gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na FIFA, 2024

    Vinicius Junior

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Vinicius Junior

    Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil da Real Madrid, Vinicius Junior, ya lashe kyautar ɗan ƙwallon ƙafa mafi ƙwazo na Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) na shekara ta 2024.

    Haka nan kuma Aitana Bonmati ta Barcelona ita ce ta lashe irin wannan kyautar a ɓangaren mata, karo na biyu a jere.

    Vinicius ya zura ƙwallo a wasan ƙarshe na gasar zakarun nahiyar Turai na wannan shekara, sai dai bai samu nasarar lashe ɗan wasa mafi ƙwazo ba a kyautar Ballon d'Or mai matuƙar farin jini.

    An soki ƙungiyar Real Madrid saboda ƙaurace wa bikin bayar da kyautar ta Ballon d'Or.

    Bonmati ta taimaka wa ƙungiyarta wajen lashe kofuna uku na cikin gida da kuma kofin zakarun nahiyar Turai na mata a kakar wasanni da ta gabata.

    Haka nan ta zura ƙwallo a wasan kusa da na ƙarshe da kuma na ƙarshe lokacin da ƙasarta Sifaniya ta lashe gasar Nations League a watan Fabarairu.

  5. Ukraine ta ɗauki alhakin kai harin bam a Rasha

    UKRAINIAN PRESIDENT

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an tsaron Ukraine sun dauki alhakin kai wani harin bam da ya hallaka wani babban janar din sojin Rasha da ake zargi da amfani da makamai masu guba a Ukraine.

    Laftanar janar Igor Kirillov, shi ne shugaban rundunar kula da makaman nukiliya da masu guba na Rasha.

    Ɗaya daga cikin Yulia,mazauna yankin da abin ya fashe ta shaida wa BBC cewa "mun ji kara mai karfin gaske, na tsorata matuka, na kasa leka taga na ga abin da ke faruwa a waje. Sai karar motocin daukar marassa lafiya kawai ka ke ji, nan da nan wurin ya rude da koke-koke."

    A jiya litinin masu shigar da kara a Ukraine suka zargi Janar Kirillov da hannu a harin makamai masu guba kan sojin Ukraine.

  6. An gano ma'aikatan bogi sama da 6,000 a Jigawa

    JIGAWA STATE GOVERNOR

    Gwamnatin jihar jigawa ta tabbatar da rahotannin da ke cewa ta bankaɗo ma'aikatan bogi sama da 6,000.

    Gwamnatin ta ce ta gano hakan ne ta hanyar tantance ma'akatan jihar da aka gudanar,inda aka samu ma'aikata 50,800 daga cikin 57,236 da ake da su tunda farko,

    Sagir Musa Ahmed Kwomishinan Watsa labarai da kula da bunkasa rayuwar matasa da wassannin motsa jiki da kuma raya al’adu na jihar Jigawa ya bayyanawa BBC cewa an fara tantancewar ne daga kan gwamnan jihar da manyan jami'an gwamnati, "Ta haka ne aka gano ma'aikatan na bogi."

    Gwamantin ta ce duk wata tana asarar kudin da suka kai sama da naira miliyan 300, wato sama da biliyan uku a shekara, "Wadanda za a iya karkatasu zuwa wani ɓangaren wajen yi wa al'umma aiki."

    Sagir Ahmed ya ce gwamnatin a dauki matakin ne domin tsabtace aikin gwamnati a jihar.

  7. Kayan agaji sun isa yammacin Pakistan inda rikici ya ɗai-ɗaita

    Jiragen dakon kayan agaji sun isa arewa maso yammacin Pakistan, inda dubban mutane suka makale sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 200 a watan Yulin, 2024.

    Mahukunta sun ce ana fama da karancin abinci da magunguna a gundumar Kurram da ke yankin Khyber Pakhtunkhwa, saboda datse hanya, ya yin da gwamnati ke kokarin shako kan rikicin addinin da ya barke tsakanin mabiya mazhanar Shi'a da 'yan Sunni.

    Sama da shekara 10 kenan ana wannan rikicin tsakanin bangarorin biyu kan mallakar fili, amma wanna karon ne lamarin ya munana.

    Ko a watan Nuwamba ma an kai wa motocin jam'an tsaro hari da kashe sama da mutane 40, a lokacin da suke kwashe wadanda suke son ficewa daga yankin.

  8. Ƴansanda sun kama matar da ake zargi da jefa jaririnta cikin kogi

    NIGERIAN POLICE

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar ƴansanda a jihar Delta ta gabatar da mutum 30, wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka ciki har da fashi da makami, da garkuwa da mutane da ƴan ƙungiyar asiri da kisan kai da sauransu.

    Ƴansandan sun kuma ce sun samu nasarar ansar bindigogi 150 ciki har da AK-47 guda 32.

    Kwamishinan ƴansanda a jihar, Abaniwonda Olufemi, ya bayyana haka a ranar Talata a yayin wani jawabi da ya yi wa ƴan jarida a shalkwatarsu da ke Asaba.

    Ɗaya daga cikin laifukan da ya yi bayani a kai akwai na kisan wani jariri ɗan wata 10 wanda aka bayar da rahoton ɓatansa a ranar 4 ga watan Disamba, 2024.

    Ƴansandan sun samu nasarar gano gawar yaron a cikin rafin Aviara.

    "A lokacin da ake bincike, mahaifiyar yaron ta amsa cewa ita ce ta jefa yaron cikin rafi a ranar 31 ga watan Nuwamban 2024.

    Ana ci gaba da tsare wadda ake zargin.

    "An kama wadanda ake zargin a watannin da suka gabata, sai dai mun samu ƙalubale, amma an samu goyon bayan sauran jami'an tsaro, da masu ruwa da tsaki da kuma al'ummar Delta wajen dawo da zaman lafiya a yankin, " in ji Abaniwonda Olufemi.

  9. Donald Trump ya gana da mai shafin Tiktok

    Donald Trump ya karbi bakwanci mai shafin TikTok a gidansa da ke Florida makonni kafin haramcin majalisa kan shafin ya soma aiki a Amurka, muddin kamfanin da ya mallaki shafin, Bytedance bai sayar da shi ba.

    Kamfanin ya yi kokarin amfani da kotun koli wajen datse wannan haramci a wani mataki na ƙarshe.

    Kafin ganawarsu a lokacin taron manema labarai, Mista Trump ya ce zai duba sabuwar dokar da ta haramta shafin, da ake saran ta soma aiki kwana guda kafin ya shiga Ofis.

    Wakilin BBC "ya ce da alama ya sauya ra'ayi domin ya nuna yana tausayin shafin saboda matasa da dama da suka zabe shi na cin moriyar manhajar."

  10. Ƙasashe masu amfani CFA sun ɗauki matakan inganta tattalin arzikinsu

    Kamaru

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙasashen yankin Afrika ta tsakiya masu amfani da kuɗi na bai-ɗaya na CFA sun gana domin samar da wasu hanyoyi da suka ce za su taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin yankin.

    Shugabannin sun yi taron a birnin Yaounde, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Paul Biya na Kamaru da Faustin Archange Touadera na Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya.

    Shugaban ƙasar Kamaru ya ce tattalin arzikin ƙasasashen yankin ya samu koma-baya daga kashi 3.3 zuwa kashi 2.3 tsakanin shekara ta 2022 da 2023.

  11. Majalisa za ta gayyaci hafsoshin tsaro kan kama Bello Boɗejo

    Boɗejo

    Asalin hoton, Bello Bodejo/Facebook

    Majalisar wakilai ta yanke shawarar gayyatar babban hafsan tsaro da na sojin ƙasa da kwamandan bataliya ta 177 da ke jihar Nasarawa kan kama shugaban Miyetti Allah Kautal Hore na ƙasa, Bello Abdullahi Bodejo.

    Mansur Soro ne ya miƙa buƙatar hakan a zauren majalisa a ranar Talata, inda ya ce a ranar 9 ga Disamban 2024 ne sojoji daga bataliya ta 177 suka kama Boɗejo a garin Maliya, kuma a cewarsa suke tsare da shi ba bisa ƙa'ida ba, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Ya ƙara da cewa mako ɗaya ke nan da kamen, amma ba a gabatar da shi a kotu ba, inda ya ce hakan ya saɓa ƙa'ida, kuma an tauye masa haƙƙinsa na ɗan'adam.

    Ana sa ran manyan hafsoshin tsaron za su bayyana a gaban kwamitin kare haƙƙin ɗan'adam da adalci na majalisar a ranar Alhamis, 20 ga Disamban 2024.

  12. Ma'aikatan wasu jihohin Najeriya na ƙorafi kan albashi mafi ƙaranci

    Ƙorafe-ƙorafe tsakanin ma'aikatan gwamnati sun ƙi ƙarewa a Nijeriya, duk da ƙarin albashi ko kuma alƙawarin hakan da hukumomi suka yi musu a wasu jihohin ƙasar.

    Ma'aikata a wasu jihohin sun ce ƙarin albashin da suka fara karɓa, ya gaza abin da suka yi tsammani, lamarin da ya sanyaya musu gwiwa, a daidai lokacin da Nijeriya ke fama da matsin rayuwa da hauhawar farashi mafi tsanani a tarihi.

    Hukumomi sun ƙara albashi mafi ƙanƙanta da kimanin kashi 130, yayin da kayan masarufi da dama suka ninka farashinsu fiye da sau uku zuwa huɗu.

  13. Buhari ya kasance shugaba mai gaskiya da tausayin talaka - Garba Shehu

    Buhari

    Asalin hoton, Buhari Sallau

    Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kasance mutum mai gaskiya da amana da tausayin talakawa.

    Mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, a ranar da tsohon shugaban yake murnar cika shekara 82 a rayuwarsa.

    Garba Shehu ya ce, "Buhari shugaba ne daban, wanda yake damuwa da damuwar talakawa da masu rauni, sannan yake dagewa wajen inganta rayuwar talakawa da fitar da su daga cikin ƙunci."

    Garba Shehu ya ce siyasa da cin hanci da rashawa ɗanjuma ne da ɗanjumai a ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya. "Tunanin mutane shi ne duk ɗansiyasa ɗan rashawa ne. Amma shi sunansa "Mai gaskiya" saboda gaskiyarsa da rashin ɗaukar duniya da zafi."

    Garba Shehu ya ƙara da cewa Buhari ya yi kamfe ne kan inganta tattalin arziki da samar da tsaro da yaƙi da rashawa.

    "A zamanin mulkinsa, ƙasar ta ga yadda aka ɗauki matakai masu yawa domin yaƙi da talauci. Buhari ya mayar da hankali kan inganta kiwon lafiya, inda a zamaninsa aka cire ƙasar daga cikin masu fama da cutar polio," in ji shi.

  14. 'An kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza'

    Gaza

    Bayan tsaikon da aka samu na watanni, alamu sun nuna Isra'ila da Hamas za su cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza tare da sakin waɗanda aka yi garkuwa.

    Wani babban jami'in gwamnatin yankin Falasɗinu da yake cikin kwamitin sulhun ya shaida wa BBC cewa, "ana matakin ƙarshe-ƙarshe ne a tattaunawa."

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, shi ma ya ce lallai tattaunawa ta yi nisa.

    A cikin ƴan makonnin da ake ciki, Amurka da Qatar sun koma teburin jagorantar sulhu, inda suka bayyana shirinsu na kawo ƙarshen yaƙin wanda ya kwashe wata 14 ana gwabzawa.

  15. Bankin duniya da gwamnatin Najeriya za su kashe dala miliyan 600 domin inganta hanyoyin karkara

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu Facebook

    Gwamnatin Najeriya tare da haɗin gwiwar bankin duniya sun kasafta dala miliyan 600 domin faɗaɗa hanyoyin karkara a ƙarƙashin zagaye na biyu na shirin inganta hanyoyin kasuwanci da noma wato Rural Access and Agricultural Marketing Project (RAAMP).

    Minista a ma'aikatar noma da samar da abinci, Sabi Aliyu Abdullahi ne ya bayyana a wani taron manema labarai da ya yi a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Ya ce tsarin kashe kuɗin zai kunshi dala miliyan 500 da bankin duniya zai bayar, sai kuma gwamnatin tarayya da gwamnonin Najeriya da za su haɗa dala miliyan 100.

    Ya ce inganta hanyoyin zai taimaka wajen sauƙaƙa kai amfanin goma kasuwanni da inganta tattalin arziki.

  16. Gobara ta ƙona kayayyakin miliyoyin naira a Neja

    Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya aika da saƙonsa na jaje zuwa ga mazauna da masu shaguna da annobar gobara ta faɗa musu a kusa da tashar hukumar sufuri ta jihar da ke Minna.

    Tashar Channels ta ruwaito gwamnan yana bayyana haka ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar, inda ya ce annoba ce gobarar, amma yana jajanta musu.

    Ya kuma yi kira ga waɗanda lamarin ya shafa su karɓi ƙaddara, wanda a cewarsa hakan zai sa Allah ya mayar musu da alheri.

    Ya ƙara da cewa yawaitar gobara, musamman a yankin Minna, abin tashin hankali ne, wanda hakan ya sa ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su wayar da kan al'umma, sannan ya ce gwamnatin domin rage musu raɗaɗi.

  17. ECOWAS za ta samar da kuɗin bai-ɗaya a 2027

    ECOWAS

    Asalin hoton, Others

    Ƙungiyar ci gaban tattalin arziƙin yankin Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta ƙara zabura domin tabbatar da samar da kuɗi na bai-ɗaya a tsakanin ƙasashenta mai suna ACO.

    Ƙasashen ƙungiyar sun cimma wannan yarjejeniyar ce a babban taron da suka yi karo 66 a Abuja.

    Asali, ƙasashen ƙungiyar sun ɗauki haramar ƙaddamar da kuɗin ne a shekarar 2020, amma annobar covid-19 ta kawo tsaiko.

    Amma yanzu, sun yanke shawarar ƙaddamar da kuɗin a shekarar 2027, kamar yadda Channels ta ruwaito.

    Ƙungiyar ta ce kuɗin na bai-ɗaya zai taimaka wajen inganta harkokin kasuwanci, da tattalin arzikin ƙasashen.

  18. An kafa makarantar kimiyya da fasaha ta mata a Nijar

    A Jamhuriyar Nijar, an kafa wata sabuwar kwalejin kimiyya da fasaha a birnin Yamai domin faɗaɗa ilimin mata, musamman a fannin kimiyya da fasaha da ƙasar ke fama da matsalar ƙarancinsu.

    Wannan yunƙuri na da nufin ƙarfafa mata, da cike giɓin da ke akwai tsakanin jinsi a fannin Kimiyya, da Fasaha, da Injiniya, da Lissafi, da kuma haɓaka ci gaba mai dorewa.

  19. Ƴansanda na binciken rusa mutum-mutumin shugaban ƙasar Ghana mai barin gado

    Ghana

    Asalin hoton, Citi Newsroom

    Ƴansanda a ƙasar Ghana sun fara binciken dalilin rusa mutum-mutumin shugaban ƙasar, Nana Akufo-Addo mai barin gado.

    A wata sanarwa da rundunar ƴansandan ƙasar ta fitar, ta ce bincike na farko-farko, "ya nuna cewa an rusa gefen hagu na mutum-mutumin, sannan an cire wata lambar yabo da ke jiki."

    A watan Nuwamba ne shugaban ƙasar ya ƙaddamar da mutum-mutuminsa, lamarin da ya jawo masa suka musamman a kafofin sadarwa.

    An kafa mutum-mutumin ne a ƙofar shiga asibitin Sekondi, wanda ya sa ƴan ƙasar suke nuna yatsa tare da cewa akwai muhimma ayyuka da ba a kammala ba.

    Wasu sun yi kira da a cire mutum-mutumin, wasu kuma suka ce babu matsala, duba da irin gudunmuwar da ya ba ƙasar.Ƴansanda sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike, kuma za su kama waɗanda suka aikata ɓarnar.

  20. Amurka ta ce an kashe sojojin Koriya ta Arewa a yaƙin Ukraine

    Koriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce an kashe sojojin Koriya ta Arewa a cikin dakarun da suke gwabza yaƙi da ƙasar Ukraine.

    Wannan ne karon farko da aka fara samun labarin kashe sojojin ƙasar, tun a watan Oktoba da aka samu labarin cewa Koriya ta Arewa ta tura kusan sojoji 10,000 domin su taya Rasha yaƙi.

    Hukumar leƙen asirin Ukraine, ta yi iƙirarin cewa aƙalla sojojin Koriya ta Arewa 30 ne aka kashe ko a jikkata a yaƙin a ƙarshen makon jiya.

    Sai dai BBC ba ta tantance sahihancin iƙirarin ba.

    Dakarun Koriya ta Arewa - waɗanda ake tunanin ba su da horon yaƙi ba - suna samun horo na musamman ne na makonni kafin su shiga fagen daga.